← Book details Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 59

Sashe 10

Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dubu dari fah kace sadakin indo? Yace hakane wlh ban san mai arziki bane, niko tsayawa inji daka ina yake ban yiba, Tani tace wlh baza ta sabu ba, dan ban yarda da wannan auren ba, nan jamila ta ranged'a buda tana fadin dama haka Allah yake abunsa duk wanda yace uwar wani ba zatai bacci ba, to wlh tashi ma ba zata rintsa ba, kuma dama hausawa na cewa in zaka gina ramin mugunta gina shi gajere wata kil kaine zaka fada, kin so ki bata rayuwan yarinya ki bata wanda bai dace da itaba baya sana'a sai uwarshi ta bashi yarki yake so amma kika hanashi kika So bashi indo to yanzu kinga lamarin uban giji koh, nan Tani ta hasala da yan uwanta sukai kan jamila suna ta yabama juna magana, dakyar mijin jamila ya janyeta yai daki da ita, itako Indo duk abunda ke faruwa tana ji babu abunda takeyi sai kuka, yanzu wata aura? Waye mijinta? Wani kukan ta kuma saki jin tani na fadin hala ma dan yankan kaine, inba dan shan jini ba, yaushe za'a bada sadaki har dubu dari sai kace yar Sarki, nan dai sukai ta fadin magan ganu gidan biki dai ya koma kaman gidan mutuwa domin babu wani jin dadi a cikin gidan dan Tani zuciyarta ji take kaman zata fashe, a haka dai har yan daukan Abu suka zo a mota biyu daukan amarya dangin tani suna ta guda tare da fadin mudai mun san asalin wanda yarmu ta aura badan yankan kai bane, suna cikin haka sai ga motoci Sun shigo layin da yawa a kalla za suyi ishirin na daukan indo da yan uwanta Wanda suke son zuwa, nan Abu ta fara kuka wai bata son Sulaiman ita mijin indo zata aura yafi Sulaiman kudi, tashin hankali🙆‍♀ nan akai ta toshe mata baki kar dangin sulaiman suji, amma taki yin shuru, jamila kam ta shirya indo cikin wata doguwar riga da aka aiko ma mijin jamila yace in anzo daukanta a sa mata, indo tayi kyau duk da har yanzu kuka takeyi Tana fadin ita bata san wannan auren, kar a shanye mata jini, dakyar da dadin baki jamila ta samu tayi shuru, amma fa zuciyarta cike yake da tsoro har yanzu, musamman ma da taji ana fadin motoci sun kai dari na zuwa daukanta, nan cikinta ya kara rudewa dan tsoro, amma jamila Tana ta bata baki harta gama shiryata Suka fito , nan Tani ta tare hanya tace wlh babu inda za'a da Indo, domin ita sam bata yarda da wannan auren ba, hmmm tashin hankali, waje ma Abu ta tirje akan sai ansa Sulaiman ya saketa domin ita mijin indo take so, nan wata yar uwan maman Sulaiman din ranta ya baci, tace dama badan Allah ta auri Sulaiman din ba, Abu tace eh ina ruwanki nan aka fara cacan baki da dangin amarya da ango, masu daukan indo sunji shurun yayi yawa ga hayani nan aka kira mijin jamila akan a bada amarya, shiga gidan yayi yaga Tani ta tare hanya tana fadin babu inda za'a da indo indai indo tayi aure tabar gidan nan toh gidan dan jummai ne, dan ni wannan dan iskan auren ba yarda Dashi nayi ba, mijin jamila yace haba Tani wannan wani irin magana ne yarinya dai an daura mata aure mutane sun shaida dan haka ki basu hanya a fita da ita, nan ta fara fadin toh munafiki dama kaida matarka ku kuka shirya komai toh wlh makircinku bazai taba aiki akaina ba wlh, indo dai babu abunda take sai kuka, mijin jamila ganin Tani ta hakince taki basu hanya ya fita jim kadan sai gashi da mlm musa, mijin jamila yace ka mata magana ta bada hanya a fitar da yarinya anzo daukan ta, mlm musa ya kalli tani yace ki matsa su wuce Allah yasa ma in an kaita su yanke mata kai, Tani da bakin ciki da hassada suke cinta tace wlh bazan matsa ba, ganin dagaske Tani take yasa mijin jamila fita, waje kuma rikici ake sosai har Sulaiman shima yazo wajan amma abun mamaki saiya fara rarrashin Abu, Yan uwanshi ransu ya baci dan haka suka wuce suka barshi da amaryan tashi, babu rarrashin da bai mata ba amma taki yarda ta bishi, suna cikin haka saiga motan sodoji har guda uku da gudu Abu ta shige gida sodojin Suka shiga gidan da mijin jamila a gaba, Tani taga Abu ta shigo da gudu ta fara tambaya lafiya nan Abu ta fara fadin Tani..... Kafin ta karasa sodoji sun shigo gidan Tani Ba shiri ta matsa a hanya Tana gani su jamila da indo Suka fita, Tani baki ya mutu taga sojo mazan fama🤣 nan aka sa amarya a mota ita daya sai jamila Suka shiga wata motar nan dangin tani suma suka shige motocin domin sunce baza'a barsu a baya ba, cikin masu shiga motar harda makota dan dai suje su karas, nan mota ta tashi aka fara tafiya

Anyi tafiya mai nisa Kafin suka Isa wani makeken gida, nan aka firfito, jamila ta nufi motar da amarya take ciki, tace ta fito, wasu mata guda biyu suka musu iso, har cikin wani makeken falo, wanda zaka rantse ba'a Nigeria kake ba, Nan sukai ta kauyanci masu taya ta murna nayi masu bakin ciki nayi irin dangin Tani, amarya dai Tana waje ita da jamila basu riga sun shiga ba, wasu motoci ne Suka shigo gidan guda uku, bayan sunyi parking, abdul ya fito ata farkon na biyun Mum din A majeed ce, sai security a cikin na ukun, wajan su indo Suka nufa nan Mum din A majeed tace sannun ku, ta kamo indo tare da fadin sannu da zuwa yata, nan ta rike hannun indo sukai dayan sashin gidan tace ma indo ta shiga da kafar dama da bismillah, hakan koh tayi idon indo dai a rufe yake, har suka shiga ciki, bayan Mum ta zaunar da ita Suka gaisa da jamila nan Mum tace itace maman mijin indo, jamila ta kuma gaidata domin ita dai mamaki take yanda taga Mum na hausa, Mum tace ma indo yata bude fuskan in ganki mana, dai2 lokacin abdul ya shigo da sallama shida A Majeed, Mum tace har ka karaso Tana yi tana kallon dan nata daya tamke fuska kaman wani dodo, Mum ta kalli jamila tare da fadin ga mijin aysha nan ta nuna A Majeed daya tamke fuska, nan Suka gaisa da jamila, Mum tayi musu nasiha sosai, sannan tace ma jamila tazo suje su kwanta, jamila tace yau zasu koma babu yanda Mum batayi ba amma jamila tace yau zasu tafi, nan Mum tasa azo a maida su tare da raba ma ko wacce dubu ishirin2 nan sukai ta murna, aka kwashe su zuwa kauyensu, Mum ta kira A Majeed taja mishi kunne sosai akan indo tare da mishi nasiha yaji tsoran Allah sannan ta wuce shima abdul wucewa yayi jiki ba kwari dan ya tabbar ma kanshi ya rasa indo har abada.......... To ga indo dai da A majeed a gida su biyu komai zai faru oho ku biyoni dan jin ya akai indo ta auri A majeed...

Taku Maryam obam😘

*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*

*NA*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*

*WWW.maryamobamnovels.com*

65to70

*DEDICATED THIS PAGE TO....*

*MY DEAR F MARDIYAH LAWAN AKA PRETY MARDY.... KINA WUTA🔥 ALLAH YA BAKI IKON GAMA NOVEL DINKI LFY.... KOWA DA RANARSA*

A Majeed ya dade a waje kafin ya shiga ciki, yanda take a zaune fuskanta a rufe haka ya kuma samunta tsaki yayi tare da wucewa dakin shi abunshi ya kwanta, koda ya shiga daki toilet ya fada yayi wanka, sai da ya dauki lokaci yana gyara gashin kanshi, wayanshi yaji yana kara, tsaki yayi ya nufi wajan wayan murmushi ya sake ganin zainab ke kiranshi, dauka yayi tare da fadin Baby yanzu nake son in kira ki, tayi murmushi tare da fadin kasan komai namu muna yi lokaci daya, sai yasa nima naji ina son kiranka yanzu nan Suka sha firansu daka karshe tace mishi tana son ya dawo gobe dan tayi missing dinshi dan shuru yayi ya lura idan yazo jalingo bata So ya dade duk da bawai tana bashi kulawa bane in yana wajanta amma sai ta damu ya dawo, katse shi tayi da fadin Baby Why r You silent? Ajiyan zuciya yayi tare da fadin Baby kiyi hakuri jibi zan dawo, nan tace ita bata yarda ba dakyar dai ya samu ya shawo kanta ta amince, bayan sunyi sallama yayi dan tsaki tare da fadin ina tsoran my Baby tasan da wannan auren da Mum tamin,dan shuru yayi na lokaci Kafin yace zan nemi mafita Kafin lokaci ya kure min.

ZAMU DAWO BAYA KADAN
Chapter 10 · 0% Book details