Sashe 13
Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Indo ta rasa inane bayi, Tana so tayi wanka ga fitsari ya dameta tun dazu, bude kofar dakin akayi wata yar dattijuwa ce, ta shigo dakin da murmushi, indo cikin dashewan murya tace mata ina wuni? Matar ta amsa da lafiya yata, ya naganki haka fuska babu kwalliya maza shiga toilet kiyi wanka kinji, indo ta fara zare ido To inane cholit kuma, kaman daka sama taji matar tace zo ki gani, nan ta bude wata kofa a cikin dakin indo baya tayi da sauri dan tsoro toilet ne, nan matar tayi dariya dan Mum ta bata labarin indo bata san komai ba Tana son ta koya mata, tace yata zo ki gani kinji? Indo girgiza kai tayi alaman a'a, ganin haka matar ta kamo hannunta tace shigo kiga yanda ake amfani Dashi, ihu indo tasa tana fadin dan Allah karki shigar dani, amma bata saurare ta ba, har saida ta shigar da ita, sannan tace ma indo ki nutsu yata babu wani abu, nan ne bayi, indo ta danyi shuru amma tana hawaye, nan ta nunama indo yanda ake amfani da komai na bayin sannan ta fita tace tayi wankan, indo sharp2 tayi domin har yanzu a tsorace take, matar tace badai har kinyi wankan ba, tace eh nayi, nan taba indo wata doguwan riga tace tasa, rigan yayi ma indo yawa kadan bayan tasa, tace suje falo Tela zai gwada ta, Tela ya gwada indo sannan matar tace sunanta Maryam indo hawaye ya fara zuba a idonta jin sunanta daya da mamanta,matar tace lafiya aysha? Indo tace naji sunanki daya da inna ta, matar tayi dan murmushi tare da fadin To saiki dinga cemin Mama koh?indo ta daga kai alaman eh cikin jin dadi,tun daka wannan lokaci indo take kiranta da mama.
Kaman yanda A Majeed yace hakan ko yayi ya sami mahaifinshi akan a rabashi da matar da Mum dinshi ta bashi, Dad dinshi ya nuna shima bai yarda ba tare daja mishi kunne akan karya fara cewa zai saketa domin bazai zubar mishi da mutunci ba, A majeed haka ya koma gida cikin takaici, washe gari da sassafe ya nufi gidan nasu domin yayi ma mum sallama akan zai wuce, lokacin Mum na kitchen domin indai his excellency na gari ita take mishi abinci da kanta, gaida Mum yayi ta amsa babu yabo babu fallasa, yace Mum zan wuce ne gobe akwai Office, Mum ta danyi shuru can tace ok amma da matarka Zaka tafi dam gabanshi ya fadi........
Taku Maryam obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
80to85
*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*DADIQA ISAH*😍
Domin baiyi zaton mum zata mishi maganan tafiya da wacce ake kira da matarshi ba, yace mum bada ita zani ba, Mum tace wannan kuma bazai taba faruwa ba dole ka tafi tare da matarka, dan shuru yayi na wani lokaci kafin yace Mum ita a nan zan barta ta dinga zama sai in dinga zuwa, Mum tace sam hakan bazai taba yihuwa ba, ganin Mum ta dage kuma taki bashi fuska yasa yace shikenan mum, amma da an barta Friday zan zo sai mu koma tare kafin nan nasa an gyara inda zata zauna, Mum shuru ta danyi tana nazari kafin tace shikenan hakan yayi, Allah ya kiyaye hanya, ya amsa da ameen, sannan Mum tace ka dai sallameta koh, dan naga kaman da shiri ka fito, yace eh Mum munyi sallama da ita, Mum taji dadi sosai har tana ce mishi ya tsaya yayi breakfast, yace No mum ina so in kai da wuri tace ok tare da bashi dambun nama da drink, fita yayi driver ya ja, suka daga abuja, A Majeed rabonshi da ganin indo tunda Mum tazo jiya kenan bai kara ganinta ba, amma yace ma Mum sunyi sallama.
Indo ita da Maryam wacce take kira da Mama yanzu suna zaune a falo, Mama tana koya mata yanda ake canza channel indo an rike remote ana dannawa, idan ta canza channel daya sai tayi dariya irin ta canza dinnan, Mama babu abunda take sai dariya tare da mamakin irin kauyancin indo, haka indo taita canza channel Tana dariya, Mama ganin abun bamai karewa bane, yasa tace tazo su zaga gidan taga ko ina, tashi indo tayi ta bita suna shiga ko wani lungu da sako, gidan kato ne sosai domin falo uku ne a cikin gidan akwai guda biyu a kasa sai daya a sama, daki uku a kasa, biyu a sama da falo babba, indo dai baki da ido ta bude tana kallo, Mama Tana ta mata bayani,har suka zo kitchen dake kasa, indo tace Mama ni kam tsoran nan nakeji wlh, Mama tayi dariya tare da fadin ki daina jin tsoro aysha, nan kitchen ne, indo kasa fadan kitchen tayi dan haka tace mai kenan? Mama tace wajan yin girki, indo ta zaro ido cike da mamaki, nan ne wajan yin girki tabdi, to ya banga murhu ko dutse ba ko akan me akeyi oho, mama ce ta katse mata tunani tare da fadin matso ki gani, nan indo ta matsa Mama ta kunna Gas sai ga wuta ya kawo indo da gudu tabar kitchen din tana fadin mun shiga uku,mama da sauri ta fito tana dariya tare da cewa indo tazo su koma ciki, indo taki yarda sai fadi take wutan ya mutu? Mama tana ta dariya babu yanda batai da indo ba akan su koma kitchen din amma taki yarda su koma, domin abun ya bata tsoro.
Mama tana taimaka ma indo sosai musamman wajan yin tsaftan jiki, domin a rana sau biyu take sata yin wanka, wanda ada sai tayi wata batai wanka ba, suna zaune a falo suna hira, Mama tace wai ni kam aysha kullum kanki a rufe,bude mu gani, indo ba tare da damuwa ba ta cire dankwalin kanta, nan Mama tasa salati ganin kan a dangare ga wari na tashi, tace aysha haka kanki yake, Indo dai bata ce komai ba, mama waya ta dauka ta kira Mum, bayan Mum ta dauka Sun gaisa take cema Mum ya kamata aysha taje Saloon, Mum tace ku shirya zansa driver yazo ya daukoku sai a mata a nan, Mama tace toh ranki ya dade, nan Mama tasa indo ta kara yin wanka, tare da fito mata da wani riga da skirt tace tasa, indo ta fito wanka tasa Mama ta bata powder ta shafa, babu laifi ta danyi Kyau, Mama ta bata gyale ta yafa, basu dade ba driver yazo ya daukesu akai gidan mum dasu, indo anata kalle2 har Suka shiga ciki, a makeken falon gidan suka zauna, basu dade da zama ba aka cika musu gaba da kayan motsa baki, Mum ce ta fito cikin shiga ta alfarma fuskanta dauke da Fara'a, tace sannu Maryam, maryam tayi murmushi tare da fadin yauwa ranki ya dade nan ta gaida Mum, itama indo ta gaida Mum, cikin Fara'a Mum tace aysha zo mana tare da miko mata hannu, alaman tazo inda take, tashi indo tayi ta nufi inda Mum take, nan Mum ta fara tambayanta ya kwanan bakwanci? Indo kunyan Mum takeji bata amsa ba sai murmushi, mum daukan wayanta tayi tasa a kunne tare da fadin kizo ciki, bata dade da ajiyewa ba, wata mata tazo cikin riga da skirt baki da baby hijab fari, tace yauwa hafsat ga Aysha nan ki gyara mata kai da gyaran jiki, hafsat ta amsa da ok ma, Mum ta kalli indo tare da fadin aysha tashi kuje, indo tashi tayi tabi bayan hafsat din, bayan sun fita Mum ta kalli, Maryam tace mai kika fahimta a gidan? Maryam tace ranki ya dade tunda naje gidan ban kara ganin shiba, haka kuma ban ganshi wajanta ba, mum tace ya wuce abuja, amma ai yazo sunyi sallama koh? Tace a'a bata ganshi wajanta ba sai dai in a waya ya mata, Mum shuru tayi amma Kana ganin fuskanta kasan ranta a bace yake, can tace ma Maryam inaga zaki koma ki dibo ma aysha kaya da dai abunda zata bukata sai ta zauna a nan kafin ya dawo dan tare nake so su tafi, maryam tace ranki ya dade inda zaki dauki shawara na aida an barta a nan sai a sata makaranta in yaso sai ya dinga zuwa, domin naga aysha bata san komai ba,nan taba Mum labarin abunda indo tai tayi Mum dariya tayi sosai sannan tace hakane gskya tana da bukatan tasan wani abu, bari zansa a duba mata makaranta duk da tayi girma ,maryam tace gskya hakan ya kamata nan sukai ta tattaunawa.
An wanke ma indo kai, gashinta har gadon baya kun san Fulani ba baya ba wajan gashi, gashi an Mata gyaran jiki tayi kyau fuskan ta tayi dan haske kadan, ita kanta hafsat din tayi mamakin gashin indo, nan tace ma indo suje ciki, bayan sun shiga wajan Mum, Maryam tace kai Masha Allah, mum tace kai aysha kinyi kyau sosai, Maryam tace muga gashin indo ta cire dankwalin, maryam ta saki baki domin ganin yawan gashin, Mum tace Masha Allah sai kace balarabiya wajan gashi su Maryam sukai dariya, nan Mum tace ma hafsat yanzu gyaran jikin zuwa nan da yaushe za'a daina? Hafsat tace za'a mata kaman na sati biyu, dan naga fara ce sosai idan aka mata farinta zai fito sosai, nan Mum tace ok, tun daka wannan ranan indo ta dawo zama gidan mum ga tela ya kawo mata wasu kayanta dinkin dai2 jikinta Mum tasa ana koya mata abubuwa da dama irin su girki da makeup, ranan da indo zata fara shiga kitchen anyi drama har sai da Mum tazo kafin ta shiga.