← Book details Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 59

Sashe 46

Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Tuki yake yana tunani jin karan wayanshi yasa ya dauka yaga zainab ce, murmushi yayi tare da dauka yace Baby gani nan zuwa tace ok tare da kashe wayan kai tsaye gidanta ya nufa, bayan ya shiga tayi hugging dinshi tare da fadin ina kaje Baby, yace naje gidan mum ne, tace ya Mum din? Yaji dadin tambayan yace lfya nan ya zauna tare da fadin mai zaki bani inci? Tace babu komai nasha mako zaka siyo mana ne, yace Baby ya kamata ki faramin abinci ina cin naki, tace Baby kaifa da kanka kasan ban wani kware ba sosai a girki kai ya girgiza alaman takaici, kiran Abdul ne ya shigo wayanshi dauka yayi tare da fadin gani gidan aysha bakin gate security yace min wai kwananka wajan uku baka zoba, haba Man sannan kasan yau gidanta kake, A Majeed baya son Zainab ta gane yace ka jirani gani nan zuwa, bayan ya kashe ya kalli zainab tare da fadin zanje wajan Abdul sannan daka nan zan tafi gidan aysha kin san yau can nake, ga mamakinsa sai yaji tace inka je kace ina gaidata, hakan ya mishi dadi tare da ganin girmanta peck ya kai mata a goshi tare da fadin I love You har mota ta rakashi yana fita ta dawo Gida ta fara kuka tare da fadin wlh saina illata ki saina nuna miki kinyi kuskuren auran min miji akanki zan koya ma duk wata mce mai gigin auran mijin wata darasi ni Zainab nayi alkawarin bata miki rayuwa sai nasa kin tsani kanki banga wacce zan zauna da ita a matsayin kishiya ba kuka take sosai tana surutai.

Koda A Majeed yaje kofar gidan yaga motar abdul a gefe shima bai shiga ba fakawa yayi a gefe tare da fitowa ya bude motar Abdul ya shiga tare da fadin wato kai har lisafamin kwanaki kakeyi koh? Abdul yace haba Man gskya kaban mamaki wannan ne son da kake fada Kana ma aysha haba dan Allah kwana uku baka leko kaga halinda take ciki ba, kai dan tacema kayi nesa da ita shine zaka biye mata bayan kasan mata karancin tunani garesu kuma suna da rauni haba Man, A Majeed yakai mai duka irin na wasa tare da fadin kaida kanka kasan ina sonta sanda nake mata shine yasa ma har nake biye mata, nake daukan duk wani abu da tace, Abdul yace Man duk irin sonda kake ma Mace idan ta kawo abunda baiyi dai2 da hankali ba karka biye mata wlh ni nazo nema inci abincin amarya dan nasan Kana nan yau Ashe kai Kana can, A Majeed yace sai kazo muje Ai, abdul yace ina ai badani zaka shiga ba next time dai zan dawo yanzu dai kaje kaga halinda matarka take ciki, fita yayi a motar abdul ya shiga nashi tare dayin horn Mai gadi ya bude, Abdul shima ya wuce, bayan yayi parking ya fito tare da kulle motar ciki ya shiga kofar falon a bude yake bata falo direct dakinta ya nufa yaga bata ciki har zai juya yaga kaman mutum a kasa da sauri ya nufi wajan ya ganta bata ko motsi, cikin tashin hankali ya fara kiran sunanta tare da bubbugata amma ko gezau batayi ba hankalinshi ya tashi matuka hawayen da yakeyi ne Ya sauka fuskanta wani irin nishi tayi mai karfi ganin haka yasa ya tashi da sauri ya dibo ruwa ya fara shafa mata a jiki, ido ta bude tana ganin dishi2 ganin kaman A Majeed yasa ta kara bude idan sosai jikinta babu kwari ta Kasa tashi sai kallonshi da takeyi shima ita din yake kallo, lokaci daya kuma tasa kuka mai karfi......

Taku Maryam obam😘

*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*

*NA*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*

*WWW.maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

220to225

*DEDICATED TO....*

*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
Chapter 46 · 0% Book details