← Book details Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 59

Sashe 7

Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mum na zaune har A Majeed ya farka, ganin Mum kusa dashi yasa abun ya bashi mamaki dan haka ya kare ma dakin kallo, ya tabbatar yana asibiti ne, lumshe ido yayi tare da fadin Allah yasa Dr bai fadama Mum matsalata ba, jin hannun Mum yayi tana shafa gashin kanshi, bude ido yayi a hankali, murmushi ta sakar mai tare da fadin Alhmdlh, son ya jikin naka? A hankali yace Mum da sauki, yaushe kika Zo? Tace dazu nazo na ganka cikin wannan halin, bari in kira Dr, fita tayi jim kadan sai gata ita da Dr, nan Dr ya dan duba shi,sannan ya fara dan tsokan shi, Oga ya kamata ayi aure shine maganin matsalan, ji yayi kaman yasa ihu gashi a gaban Mum duk kunya ta rufeshi, shiko Dr ko a jikinshi, nan Dr ya rubuta mai wasu Magani da za'a bashi kafin su wuce, A Majeed yasan Mum tasan komai haka ya tashi jiki babu kwari bayan an basu maganin Suka nufi gidan su mum dake abuja domin tace ba zata gidansa ba, hakan akayi, driver ya aika yace ya siyo mai jallabiya guda biyu da zai sa, Kafin ya koma gida, wanka yayi sannan Mum ta kawo mai abincin da tasa aka siyo kafin tayi girki, kadan yaci sannan ya kwanta, bacci ne ya dauke shi, ganin haka Mum ta nufi kitchen ta duba kayan ciki, abunda babu ta bayar a kawo mata su, wanda suka zo tare kuma ta basu kudi tare da cewa suba driver ya siyo musu abunda suke so, Mum ta kammali komai ta nufi dakin dan nata, ji tayi yana waya yana fadin yanzu Baby kina ganin kin kyauta yau wajan 7 days ina kiranki baki packing, ban san mai take ce mishi ba,naji yana fadin kin san ina missing dinki sosai har hakuri na ya kare yau na dawo daka hspt, gskya Baby kina cutana da yawa, shuru yayi yana sauraranta Kafin yace ok plz come back 2moro, I love you too My angel, kashe wayan yayi Mum dake tsaye gaba daya takaici ya kamata wlh bazata sabu ba, idan shi baison ciwon kanshi ba, to ita tasan zafin haiyuwarsa, dakin ta karasa ta ganshi a zaune murmushi ya sakar mata ganin fuskan Mum din a daure yasa yasha jinin jikinshi tare da fadin Allah yasa ba maganan matarshi zata mishi bah,mum zama tayi a gefen gadon dakin tace ya jikin? Yace da sauki My Mum, dan murmushi tayi tare da fadin muje kaci abinci,yace No Mum bana jin yunwa sai anjima zanci, tace toh shikenan, tashi tayi ta fita, jim kadan sai gata ta dawo da wani bowl a hannunta naman Rago ne, bashi tayi tace gashi kaci amsa yayi ba tare da musawa ba, ya fara ci, fita ta kuma yi ta dauko mishi maganin shi da drinks, duka naman ya cinye tare dashan maganin, dan fira Suka fara can mum tace A Majeed kai yanzu haka kake so kaita zama koh? Shuru yayi domin yasan za'a rina, taci gaba da fadin yau matarka tana can kasan gobe tana can, baka da iko da ita, inkai baka son kanka karka manta ni ina sonka kuma kasan bazan dauka ba, tun tuni nake maka maganan karin aure kana nokewa toh wlh kaji na rantse wannan karan sai ka kara aure, inko kaga bakai auren nan ba toh wlh bana raye, yau shekara nawa dayin aurenka har yanzu shuru babu karuwa yau mata nacan gobe tana can, shidai shuru yayi dan yasan Mum tunda ta rantse dakyar ta canza zance, zufa yana keto mai tako ina, Mum tace na baka nan da wata daya ka Kawo min wacce kake so tashi tayi ta fita daka dakin fuuuu, A Majeed innallilahi wa Inna'ilaihira jiun kawai yake fada, yanzu da wani idon zai kalli zainab yace zai kara aure, bayan ya mata alkawarin bazai mata kishiya ba, kuma sun tsara yanda zasu tafi da Al'amarin su, kai gskya bazai yihuwa ba dole yama Mum bayani yanda zata fahimce shi, duk da yasan yana da karfin Sha'awa amma hakan ba matsala bane zai fara azumi, hmm tabdi lallai kana da aiki A majeed, bari dai nayi shuru🙊 inga yanda zata kaya .

Indo ta fito da dambu ta nufi tasha kaman jiya aka siye duka, tana zaune a wani benci a cikin tashan dan bata son komawa yanzu, kaman daka sama taji magana waigawa tayi taga Abdul, ita harga Allah ta manta yace mata zaizo, cikin sauri tace ina wuni yaya Abdul, yace lafiya qalau kanwata tun dazu nake ta jiranki a waje nayi wajan awa daya, naji shuru shine nace bari in shigo koh zan ganki, tace kayi hakuri wlh na manta ne,kuma tun dazu na siyar, yace toh yanzu ni zan koma abuja, gashi baki da waya, ni kuma kullum ina son jin muryan kanwata, murmushi tayi tace hakane sai dai idan ka dawo, yace kai gskya zan dan dade coz ina da aiki sosai yanzu dai na samo mana mafita, muje waje, tashi tayi ta bishi Suka fita waje, mota ya bude ya dauko wani leda, yace gashi waya ne, akwai sim a ciki, sai kisa caji, kai ta girgiza tace ka barshi ni bana bukatan waya, yace saboda me? Tace hakanan mu bamu da wuta ma a garin mu, shuru yayi cikin mamaki,babu yanda baiyi ba akan ta amshi wayan taki, haka ya mayar tare da bata kudi yace tunda taki amsa shima dai Kin amsa tayi sai da yayi mata da gaske Kafin ta amsa, sallama ya mata tare da fadin zai zo ranan juma'a koh sati, tace toh sannan ya wuce, tsallaka titi tayi sai ga dan jummai yasha gabanta, yana fadin indo ina washe baki tunda kin hanani kanki zan turo gidanku inna aureki ai babu wanda ya isa ya hanani inyi yanda naso koh, tace waye zai aureka Allah ya kiyaye, dariya yayi tare da fadin wlh saina aureki indo ke gobe2 zan turo gidanku sai inga ta tsiya........

Taku Maryam obam😘

*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*

*NA*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*DASHEN ALLAH......*
*(TOGETHER WE STAND NENVER DIVIDE FOR ALL)*

*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*

*WWW.maryamobamnovels.com*

45to50

*DEDICATED TO....*

*FAIZA DABO......Allah Ya raya Baby girl akan tafarkin addinin musulunci👏*

Indo bata kara cewa komai ba, tayi gaba abunta, binta yayi da kallo tare da lashe baki yana fadin inna aureki zan kwashi dadi, gida ta nufa tayi sallama Tani na zaune Akan tabarma duk ta cinye, tace sannu da gida inna? Bata amsa ba sai hannu data mika mata alaman ta bata kudin, mika mata tayi ta girga taga ya cika, Abu ce ta fito da tilin kayan wanki ta zubar a kasa tare da komawa ta dauko wasu, kayan da yawa sosai ta Kalli indo tace ga sunan kizo ki wanke Min ta wurga mata naira ishirin gashi ki siyo sabulu, indo babu yanda ta iya hakan ta dauka ta fita bata dade ba ta dawo, dakinta ta nufa zata shiga tani tace kee ina zaki kuma kizo ki kwashe kayan nan, indo tace inna hijjabina zan ajiye, Tan bata kuma cewa komai ba sai tsaki da taja ta shige daki, indo na shiga daki ta boye kudin da abdul ya bata cikin kayanta dake daure a leda, sannan ta fito ta fara wanki kayan da uban yawa ta dauki Lokaci sosai har wajan karfe goma saura tana waje tana wanki gashi ta gaji ga yunwa, haka ta gama wankin bayanta duk ya rike ga ruwan gidan ya kare, daukan roba tayi ta nufi gidan makotansu ta dibo kadan Kafin safiya yayi, bayan ta gama ta nufi dakin tani sallama tayi tace inna na gama tani tace toh naji mayya saiki tashi kije kisha ruwa ki kwanta domin sauran tuwan dana ajiye miki abu ta cinye,tashi tayi ta fita jiki a sanyaye dakinta ta nufa ta dauko kudin da abdul ya bata ta nufi dakin jamila tura kofar tayi a hankali dan kar ajita, jamila dake kwance ta tashi da sauri jin an bude mata kofa yar fitilan kwanta ta dauko ta haska taga indo ce, tace indo lafiya Kuwa? Indo tace lafiya inna jamila mika mata kudin indo tayi tace gashi ki ajiye min, jamila a ina kika sami wannan kudin indo tace inna jamila wannan mutumin ne ya bani wanda yaban kayan jiya, jamila ta dan bata fuska tare da fadin indo daka yau karki kara amsan abun wani saurayi domin ki tsira da mutuncin ki, indo tace wlh Inna jamila babu yanda banyi ba amma saida yaban, nan ta bata labarin yanda sukayi, jamila tace toh Allah ya saka mishi da alkhairi, yanzu dai bari inga nawa ne, kirgawa tayi taga dubu ishirin zare ido jamila tayi tace kai wannan uban kudi haka, yanzu mai zakiyi dasu, Indo tace inna makaranta nake son shiga wlh ina son nayi karatu in zama wata abu, jamila tace Allah sarki indo sai dai burinki kaman bamai yihuwa bane saboda Tani ba zata barki ba, indo jikinta yayi sanyi domin tasan haka dinne, jamila ta dauko mata shinkafa ta manja taji kayan miya sosai ta bata, nan indo ta fara ci sosai abincin ya mata dadi, tas ta cinye, jamila tace tunda kin gama tashi ki tafi daki kar Tani ta ganki, tace toh tare da tashi ta fita tana sambo kaman munafuka ta shiga dakinta.
Chapter 7 · 0% Book details