Sashe 30
Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Gaba daya ta gama sa abunda zata bukata cikin akwati, duk da ba komai ta dauka ba, fita tazo yi amma saita tsinta kanta da kasa bude kofar dakin, domin tunanin alkawarin da tayi ma Mum ya fado mata, bani da yawan dangi koh yara, naso ki zauna dani har abada sai dai hakan bamai yuhuwa bane dan za kiyi aure May be Ma mijin da kika aura ya hanaki hulda dani, sakan akwatin tayi tana kara rusar kuka, tunawa tayi da amsan da taba Mum, bazan taba barinki ba mum duk mijin dazan aura dole ya soki a matsayin Mum dina, zama tayi a wajan tana kuka gwanin tausayi, mai yasa talaka bashi da gata mai yasa wanda bashi da iyaye yafi shiga irin wannan matsanacin rayuwan mai yasa, A Majeed mai yasa kake son Sani cikin kunci koda yaushe mai yasa maina maka, ni nasan bawai dan kana sona dagaskiya kake wannan abunba, kanayi ne dan wata manufa taka ta daban, dan shuru tayi kaman Tana dan nazari lokaci daya kuma ta lumshe ido hawaye na zuba jin karan wayanta ne yasa to bude ido Bros taga an rubuta da sauri ta dauka tare dayin sallama, bayan ya amsa yace sister lafiya Kuwa? Naji muryanki kaman mai kuka, dan murmushi tayi na karfin hali Kafin tace lafiya qalau bros, yace ya mai jikin da fatan dai da sauki koh? Tace eh Alhmdlh da sauki bros, nan suka taba dan fira kafin sukai sallama akan cewa gobe zaizo gidan, yana kashewa kiran yazeed ya shigo wayanta, kaman karta dauka harya kusa tsinkewa ta dauka tare da fadin Hello, daka gefenshi shima ya amsa da fadin barka da dare, dan lumshe ido tayi tare da fadin barka kadai, yaka koma Gida? Ya amsa da lafiya dan shuru ya biyo baya, jin muryanshi tayi yana fadin aysha tun ranan dana ganki Allah yasa min sonki a raina, sai dai kuma a lokacin baki bani lokaci ba dan kin nuna kina sauri, amma haka zuciyata taci gaba da tunaninki duk da ban san inda zan kuma ganinki ba, sai dai nabar ma Allah komai sai gashi kuma ya kara hadamu cikin sauki wanda ina fata wannan karan zai zama shine hanyar da zamu kasance har abada, domin dai ni bada wasa nazo ba, dagaske nake aurenki zanyi sannan bana son ya dauki Lokaci mai tsawo, amma fah inkin amince dani, dan shuru yayi alaman yana jiran amsa, kanta ne ya kulle tama rasa abunda zata ce mai jin muryanshi tayi yana fadin ban samu karbuwa bako? Tace a'a yaya yazeed na amince Allah yasa hakan shine alkhairi, cikin jin dadi ya amsa da ameen, tare da fadin insha Allah zaki farin cikin kasancewa mata2 sannan dan Allah inaso kar aja da tsawo inaso ayi komai nanda wata biyu, bata iya cewa komai ba dan tama rasa abunda zata cemai tadai yardan mishi ne kawai badan tana sonshi ba ko Tana jin wani abu a kanshi ba, sai dai auren nashi zaisa tabar gidan nan gaba daya hakan zaiba A Majeed daman tashi tare da wargajewar wani abu da yake nufi a kanta, jin tayi shuru yasa yazeed ya kira sunanta tare da fadin gobe zanzo sai muyi magana, tace Allah ya kaimu tare da kashe wayan, Mum ce ta shigo dakin ta ganta a bakin kofa ga akwati a gefenta, kallon akwatin tayi sannan ta Kalli indo wacce fuskan ta tayi ja ga idonta duk ya kumbura dan kuka kun san farar Mace, Mum tace aysha lafiya kuwa? Maiya sameki wannan akwatin fah? Badai kina nufin Zaki barni bane,? Wannan tambayar duk a lokaci daya Mum ta mata shi, indo gaba daya kunya ya hanata magana dan bata so Mum ta shigo dakinba ba tare data maida komai wajanshi ba, mum ta tsugunna tare da kiran sunan aysha tace aysha mai aka miki da zakiyi irin wannan danyan aikin, koh wani ne ya bata miki rai? Indo kuka ta kuma saki tare da fadin Dan Allah mum kiyi hakuri wlh na rasa abunyi ne, gaba daya komai ya jagule min Mum dan Allah karki min wani fahimta ta daban.... Kuka yaci karfinta dan haka tayi shuru ba tare data karasa abunda tayi niyan fada ba, Mum janyota tayi jikinta Tana shafa mata baya tare da fadin aysha na fahimce ki, amma mai yasa ba zaki iya fadamin abunda yake damunki ba, saiki yanke hukunci dakanki? Cikin murya mai sanyi tace Mum A Majeed yana son kara bata min rayuwa Mum...... Shuru tayi dan tunawa dawa take magana, jin muryan Mum tayi Tana fadin aysha kiyi hakuri A Majeed bai isa yasa kiyi abunda baki niya ba, bashi da iko akanki, sannan ba zamanshi kike ba, kiyi shuru ki daina damuwa da komai kinji, bazan bari ya kara miki wani magana makamancin hakan ba, sannan idan kina da wanda kike So ki bashi dama ya fito kinji? Ido kasa amsa ma mum tayi dan gaba daya jikinta yayi sanyi, tare dajin kunya yau gashi Tana nuna bata son jinin Mum, wani hawaye mai zafi ya zubo mata sai dai hakan bazai sa ta canza ra'ayi ba, dan tasan bawai sonta yake ba, yaudara ce kawai irin tashi, shida yake da zee mai zaiyi da ita, gata yar masu arziki nida ba yar kowa ba, bazan iya kishi da itaba .... Wata zuciyar tace mata sai kace ba Mace ba, ai indai Mace ce ko wacece zaki iya zaman kishi da ita, ido ta lumshe ba tare data gamsu ba, Mum ce ta katse mata tunani tare da fadin tashi kije kiyi wanka ki sauko kici abinci, tashi tayi ta nufi toilet Mum kuma tabar dakin, ta nufi dakin dan nata dan taga ya yake ciki.