← Book details Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 59

Sashe 17

Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari da safe indo ta tashi tayi wanka domin ta riga ta saba kullum sai tayi wanka da safe da kuma yamma wanda Mum ce tasa take hakan harya zaman mata jiki, wata doguwar riga tasa ta kamata ta sama, dankwali ta daura ta nufi kitchen domin yunwa take ji, dan tasan inta zauna a daki yunwa ne zai kashe ta, kitchen ta shiga wanda a yanzu ta daina jin tsoro🤣 store ta bude taga babu komai, fridge ma haka babu komai sai drinks kala2, rufewa tayi tana tunanin mai zata yi domin dai yunwa take ji, sama ta koma ta dauko gyalenta tare da bude jakarta ta dauko kudi a cikin wanda Mum take bata in zata Skul, ta fita gate ta nufa taga security din gidan tace musu dan Allah a ina zan samu shago? Daya daka cikinsu yace ta kawo mai za'a siyo mata, tace a'a zata da kanta, nan ya kwatanta mata ta fita, shagon da nisa sosai, tafiya takeyi a kafa da yake anguwan masu hannu da shuni ne sai dai kaga mota jefi2 tazo ta wuce, wani katon shago ta gani nan taje ta siya indomie guda biyar da Egg guda goma sannan ta dawo gida, a falo ta ganshi hada ido sukayi, gabanta taji ya fadi domin Allah yasa mata tsoranshi bana wasa ba, tamke fuska yayi hanyar kitchen tayi, jin maganan shi tayi yana fadin daka gidan uban wa kika fito? Tsayawa tayi cak gabanta na dukan uku2, bata bashi amsa ba haka kuma bai kara yin magana ba, amma daka ganin alama yana jiran amsan nata ne, bata ga sanda ya tashi ba kawai taga mutum a gabanta tare da amsan ledan hannunta yana dubawa yaga ko miye, jefa mata yayi tare dayin tsaki yace wa yace ki fita? Tace naje siyo abunda zanci ne, wani kallo ya mata tare da fadin daka yau idan kika kara fita siyo wani abu sai nasa an ballamin ke, idiot yana fadin haka ya shige dakinshi yana jin haushin indo gaba daya ta zaman mishi matsala idan ya tuna matarshi ce wani irin takaici yake ji, yarinyar da batafi ayi rainonta ba wai ita aka aura mai, toilet ya shiga yayi wanka domin yaji baya son zaman garin gwara ya koma Abuja kawai, ita indo tunda ya tafi ta shiga kitchen ta dafa Indomie dinta a kitchen dinma ta zauna taci ta wanke komai, lokacin da zata fito ta ganshi yana jan akwati fuska daure yace kizo mu wuce, yana maganan ne kaman baya son yi, daki ta koma ta dauko kayanta a cikin akwati tare da feshe jikinta da turare sannan ta fito, a bakin gate ta ganshi yana ba security kudi yana murmushi, a zuciyarta tace dama yana dariya sai taga ya kara kyau, ajiyan zuciya tayi tare da nufa motar driver yasa mata kaya a boot ta bude baya ta shiga motar kamshi ga a.c a kunne, harya gama sallaman su ya nufo motar ya bude ya ganta a baya tsaki yaja tare da fadin tashi ki fitar min a nan ki koma gaba, bude motar tayi zata fita komai ya Tuna kuma oho yace dawo ki zauna, rufe kofan tayi tare da zama, shima ya shiga ya zauna driver yaja,gudu mota take ta shararawa a titi A Majeed fuska a daure yake ta lallatsa wayanshi, ita ko indo duk ta gaji ga sanyin AC din ya dameta yana so ya sata bacci gashi bata son yi, indo dai bacci ya dauketa ta wajan kofa tasa kanta, A Majeed ya waiga yana kallonta tare dayin tsaki ya juyar da kanshi gefe.

Sun shiga cikin dangareren gidanshi a lokacin indo ta farka, bayan driver yayi parking A Majeed ya fito, indo tana nan zaune tana tsoran fita tasha masifa, wucewa yayi ba tare daya kalleta ba, driver ne yace hjy ki fito an kawo, bude kofar tayi ta nufi inda taga A Majeed yayi, gidan ya hadu ga masu gadi kala2 wani katon falo ta ganta a ciki A Majeed ta gani da wata mata kyakyawa ta rungumeshi, indo ta danji wani iri ganin yanda tamai domin abun ya bata kunya, dan sakin shi Zainab tayi tare da fadin keee daka ina haka? A Majeed ya waiga yaga indo ce, yace oh swty tare muke, kallonshi tayi alaman ban gane ba, kaman ya fahimci hakan yace na kawo ta ne dan ta dinga min traditional food kinga basai na dinga zuwa jalingo sosai ba, Zainab tayi dan murmushi tare da fadin hakan yayi ta kuma kallon indo dake tsaye tana mamaki tabe baki tayi domin kwata2 taji indo bata mata ba, kai anya zan zauna da wannan a matsayin yar aiki kuwa No gskya ya kamata asan abunyi ba'a gida na bah...

Taku Maryam obam😘

*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*

*NA*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*

*WWW.maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

100to105

*DEDICATED THIS PAGE TO....*

*HAFSAT MAMANI MMN JAWAHEER😍*

A Majeed ne ya katse mata tunani da swty a bata wajan zama, Zainab tace gskiya Baby ni bana sonta kawai ta koma inda ta fito sai a sami wata, A Majeed shuru yayi Kafin yaja hannun Zainab sukai ciki, komai ya ce mata oho sai gasu sun fito indo dai tana nan a tsaye takaici ya isheta, Zainab ta tabe baki tare da fadin na yarda zaki dinga min aiki So sai dai bana son kazanta sannan bana son sata dan ku yaran talakawan nan daka an baku dama sai ku fara yima mutum sata, duk ranan dana kamaki da wani abu nawa wanda ban baki ba saina kulleki harda iyayenki, Hope kinji abunda na fada indo da hawayen da take boyewa dan kar su zubo lokaci daya Suka zubo tare da fadin naji, Zainab tace good, kiran wata tayi a cikin masu aikinta tace a kai indo dakinsu, A Majeed yana zaune bai tanka ba, indo wani irin tsananshi taji tana yi, ta tabbata baya sonta kaman yanda yake fada, shikenan dai talaka a wulakance ake kallonshi koda yaushe, mai kudi yana ganin kanshi kaman wani Sarki, jiba yanda take gayamin magana kaman zata cinyeni danya, tabbas koma miye A Majeed yaja min tunda baya son auren mai zai sa bazai sakeni ba, in sami dai2 ni in aura, wani hawayen ne ya kuma gangaro mata, a dai2 lokacin Suka karasa dakin da za'a kaita, dakin babba ne akwai katifa guda uku manya, sai TV dake manne a jikin bango da AC, matar tace ma indo ga gadon ki nan, indo tace toh tare da ajiye kayanta akan katifa din dakin, matar tace zaki fara aiki idan madam ta fadi abunda zaki dinga yi, indo tace toh sannan matar ta fita, tana fita indo ta saki kuka tare da fadin ta tabbata inda sulaiman ta aura da bazai mata haka ba duk da tasan shima yafi karfinta nesa ba kusa ba, karan wayanta taji dauka tayi taga Mum ce, ta dauka da fadin barka da Gida Mum? Mum tayi murmushi daka gefenta tace aysha kina lafiya koh,? Tace lfya Mum, Mum tace ya naji kaman kinyi kuka ko ma dai ince kina kuka? Tace ba kuka nakeyi ba mum mura ne ya kamani, Mum tayi ajiyar zuciya daka gefenta tace ya dai sai miki Magani koh? Tace eh, Mum tayi dan murmushi tare da fadin nakira inyi miki ya hanya ne tunda tafiya babu sallama, kiyi ta hakuri da abokiyar zaman ki Dashi kanshi mijin naki sannan ki dage da addu'a komai zai wuce, indo tace ngd Mum, Mum taci gaba da fadin zan mishi magana a duba miki islamiya a nan kafin ki fara zuwa skul din nayi magana dasu akan a baki transfer sunce sai nan da sati biyu, indo taji dadi sosai tunda zata ci gaba da karatu koba komai zata dinga dibe ma kanta kewa domin harga Allah bata son zama gidan nan tunda taga irin tarban data samu da kaskantar da ita din da akayi koh da yake dama ita tunda talaka ce ai a hakan za'a kalleta, Mum ce ta katseta da fadin dan Allah komai ya miki ki fadamin kinji karki boyemin komai, ke bama shi ba ko matarsa ce ta miki wani abu ki fadamin indo tace toh Mum sannan sukai sallama, indo tace Allah Sarki Mum ita bata da wulakanci irin na masu kudi koh dai dan ita ba yar kasar bace oho, kai shima haka dad din A Majeed din yana da kirki, toh a ina dansu ya koyo irin wannan halin? Domin dai iyayenshi mutanan arziki ne, ko da yake shima yana da kirki dan taga yanda yake da masu aikin shi, toh ko dai nice daya tsana bayamin kirki,tabbas hakane haka taita tunanin ta har aka Kawo Mata abinci taci tayi sallah.

Zainab tunda taga indo taji ta tsaneta ita da kanta ta rasa dalili sai dai tana ganin ko dan tana da kyau ne yasa bata sonta dan ta lura da indo tana da kyau na Bala'i sai dai kyan nata bai gama fitowa ba dan taga kaman bata wani waye sosai ba, idan yarinyar ta kile tabbas babu namijin da zai ganta bai so ya aureta ba, wannan abun yake damun zainab dan koda indo ta wuce dakin masu aiki, zainab ta dire akan sai an kori indo A Majeed ya dinga rarrashinta akan tayi hakuri Mum ce ta bashi ita akan ta dinga musu aikin girki, kuma dakyar Mum ta bashi ita dan yace yana son irin abincin ta, wata sabuwa jin yace Mum ta bada indo yasa ta kara tsanan indo din, tare da burin safiya tayi ta fara horata ta yanda ba zata sami lokacin kanta ba balle har ta daukan mata hankalin miji kaman yanda take tsoro.
Chapter 17 · 0% Book details