← Book details Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 59

Sashe 18

Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe Gari tun wajan 8 A Majeed ya tafi office, Zainab tasa aka kira mata indo, bayan indo tazo ta gaida zainab, bata amsa ba sai fadin da tayi miye sunanki? Indo tace aysha, tabe baki tayi sannan ta kalli indo din tace daka yau ke zaki dinga wanke2 kina mopping din ko ina sannan ban yarda a dinga shigo min falo da sunan mopping ba in mijina yana nan ba, da sassafe zaki dinga yi Kafin ya fito, dan ni bazan iya cin abincinki ba dan baki kai wannan matsayin ba, ina fatan kin fahimta indo tace eh,. Tun daka wannan ranan indo ta fara aiki ga gidan kato haka take goge ko ina in Zainab taso yin rashin mutunci tace bai goguba, haka zata sa ta kara gogewa, ganin kaman aikin baya damun indo yasa zainab tace ita zata dinga yima masu aikin gidan abinci indo tace toh haka kullum inta tashi da asuba zata fara aiki bata samun hutu sai dare domin daka ta tashi zata daura ma masu aikin gidan abinci tayi shara da goge2 inta gama tayi wanke2 sannan abincin rana, inta gama na rana saina dare, duk da abun yana damun indo bata taba gaya ma mum ba duk kuwa da yawan tambayanta da takeyi, indo tana samu taci ta koshi kuma tana kara girma da kyau Zainab har mamaki takeyi ganin kaman indo bata damuwa da aikin da takeyi sai dai yanzu ta dan fara raga ma indo din domin ganin kaman A Majeed din ya tsani indo din.

Mum ta kira A Majeed akan maganan makaranta indo tace ana abuja akwai islamiya So zata dinga zuwa tun safe sai 6, yace OK zaisa a kaita, koda yama Zainab magana tace ita sam bata yarda ba, sai dai indo ta zaba aiki ko karatu babu yanda baiyi da Zainab ba amma taki yarda, ganin haka shima ya share maganan dan baya son gimbiyar tashi tayi wani tunani akai, yau wajan watan indo daya a abuja da sati biyu, har yanzu bata zuwa skul abun na damunta duk ta rame saboda tunani, yau Zainab zata bar kasar domin zata raka Mum dinta Canada, tunanin yanda zata bar indo a gidan take ita ta rasa dalilin da yasa bata son indo ta zauna waje daya da mijinta, kiran A Majeed tayi a waya akan zata kai indo Skul din,yaji dadin hakan sosai nan ya fada mata inda skul din yake, tare da ce mata inta je ta fada musu itace akama transfer daka jalingo hakan ko akayi bayan driver ya kaisu basu bata lokaci ba aka gama komai indo a can aka barta abun dadi ma babu wani nisa daka skul din da Gida, amma akwai dan tafiya kadan, ita Zainab tana ganin indo zata wuni bata Gida inta dawo kuma sai bacci da wannan tunanin yasa ta kai Indo skul din ,itako indo farin ciki takeyi sosai, Zainab anyi tafiya an bar kasan kuma a kalla za tayi sati biyu ko uku, indo ta dage da karatu sosai ga girki da take koya shima, islamiya ma suna karatu sosai daka ta dawo gidan in tayi wanke2 taci abinci sai bacci da safe kuma tayi shara da mopping ta wuce skul yanzu bata girki sai wanke2 da shara, yau indo ta fito tana shara wanda falon ma babu wani datti amma kullum sai an share an goge, A Majeed ne ya fito daka gani abu yake son dubawa, kallo daya yama indo ya kauda kai ita kam bata daina sharan ba dan tana sauri tayi ta gama kar tayi lati, sai dube2 yakeyi a kasa ya hango wata takarda da sauri ya nufi wajan dauka yayi ya bude cikin fushi ya karasa inda indo take da karfi ya jata tare da wanka mata mari mai dan karan zafi har sai da taga Star yace ke wace irin mahaukaciya ce kin san takardan miye wannan da zaki share? Yanzu inda ban fito ba dakin share kina aiki kaman mahaukaciya bakya duba abu, cikin kuka tace kayi hakuri a kasa na gani ban...... Enough ya katseta tare da fadin fitar min daka nan idiot, zama yayi a falon yana huci kai wai mai yasa Mum ta aura mishi wannan abun ne gskya ya kamata indau mataki akai, tashi yayi ya nufi dakin masu aiki amma babu kowa a ciki dan tsaki yaja tare da komawa falonshi yana tunanin ina taje, indo koda ta fita daka falon skul ta wuce dan dama ta gama komai falon ne kawai ya rage, tana kuka har ta nufi skul babu kowa sai ita daya dan 8 suke Zuwa yanzu kuma 7 , tana nan zaune har aka fara zuwa, tun daka wannan lokacin Indo bata kara bari sun hadu da A Majeed ba duk kuwa Dashi yana son ganinta domin ya gaji da zama da takeyi a matsayin matarshi, satin zainab biyu ta dawo Nigeria A Majeed yana falo sai gata ta shigo cikin fushi ko kallonshi ba tayi ba ta nufi dakin indo ta janyota har suka karaso falo, ta jefar da indo ta kalli A Majeed tace dagaske wannan jakar matarka ce?........ Muje zuwa

Taku maryam obam😘

*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*

*NA*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*

*WWW.maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

105to110

*DEDICATED THIS PAGE TO....*

*HASSAN ATK🤝*

A Majeed da sauri ya tashi tare da fadin god forbid taya zata zama matata? Zainab tayi wani irin dariya tare da fadin ok tunda ba matarka bace yau zata bar gidan nan tunda bana ubanta bane, daga kafada yayi kalan I don't care dinnan,ganin haka yasa zainab ta fara janta har riganta ya yage daka sama, ganin riganta ya yage yasa ta fara kokarin ta yaga mata shi duka indo babu abunda takeyi sai kuka tare da tsanan A Majeed da Zainab tabbas koda yau bata ce tabar gidannan ba toh ta barshi kenan har abada, A Majeed ganin ta yaga mata riga kirjinta duk a bude idonshi ya sauka a kai nufansu yayi tare da rike zainab din yana fadin swty what are you doing? Mai kike shirin yi haka? Ta fara kokarin kwatan jikinta daka nashi tana fadin wlh yau saina kashe ta kaima zan dawo kanka, riketa yayi da karfi yana fadin na fada miki ba matata bace, dai2 lokacin Mum ta shigo gidan tace tabbas ba matarka bace, nufa wajan indo tayi da take durkushe tana kuka, Mum ta daga ta tare da fadin muje kisa kaya, dakin da indo take nan suka nufa, Mum takaici duk ya cikata wato yar aiki suka maida aysha, lallai A Majeed ka nunama duniya bamu isa dakai ba, ita ta taya Indo hada kaya domin tace bazata kara kwana a gidan ba, Mum da indo suka fito Mum itace ke jan akwatin indo din, A Majeed da sauri ya nufeta yana son amsan akwatin mari Mum ta sakar mai tare da fadin nagode da abunda ka aikata dama tun tuni jikina ya bani akwai abunda ke faruwa duk da Aysha Tana boyemin tace komai lafiya, sai yasa nayi zuwan ba zata, Ashe abunda zan gani kenan, ta kalli Zainab da take muzurai kaman zaki najin yunwa tace bari kiji in fada miki abunda kike son ki tabbatar, aysha matar abdul-majeed ce, amma daka yau ba matarshi bace, ta Kalli A Majeed tace ka rubuta min takardan aysha kuma saki uku nake So yanzu ka ban, Zainab da sauri tabar wajan jim kadan sai gata da takarda da biro tana mikama A Majeed, bai amsa ba bai kuma yi mata magana ba, illa Mum ce data karaso wajan ta amsa takardan cikin takaici ta mika mai, amsa yayi ga mamakin Mum sai gashi ya fara rubutu, harya gama ya mika ma Mum tare da fadin Mum kiyi hakuri naso in zauna da ita amma na kasa sata a raina domin bata cikin tsarin macen da nake so.... Mum jan hannun indo tayi wacce take ta faman kuka suka fita mota Suka shiga driver yaja, gidan su na abuja suka nufa, Mum Tana shiga ta zaunar da indo ta fara mata nasiha akan tayi hakuri haka Allah ya tsara mata, sannan tana rokan indo akan taci gaba da zama da ita karta ce zata barsu, indo ta kasa magana sai kuka mum ta janyota jikinta ta rungumeta itama tana hawaye, dakyar ta samu ta rarrashi indo tayi shuru, ranan zazzabi ne ya kama indo sosai Mum ta tsorata dan haka suka nufi hspt Dr yace damuwa ne ya mata yawa tana bukatan hutu, nan ya bata Magani sannan suka dawo, washe Gari suka dawo jalingo, Mum ta fadama his excellency abunda ya faru tun a waya ranshi yayi mugun baci, koda su Mum suka dawo yace ta bashi takardan amsa yayi ya Fara karantawa kaman haka *NA SAKI AYSHA SAKI DAYA MUM KIYI HAKURI BAN TABA SON AYSHA BA, BANA SON FUSHIN ALLAH A KAINA DAN ALLAH MUM KI GAFARCI DANKI* his excellency bayan ya gama karantawa yace Allah yasa haka shine alkhairi yace Mum ta kira mishi aysha din, Mum ta tashi ta kirata bayan tazo his excellency yace aysha naji abunda ya faru da farko dai zan baki hakuri akan abunda ya faru sannan in nemi alfarmanki akan ki zauna damu har Allah ya fito miki da wani mijin, tace insha Allah sannan ban rike komai a raina ba komai ya wuce, his excellency yaji dadi sosai yana ta sa mata albarka, tare da fadin zai zamo mata uba ta dauka tana tare da iyayenta, taji dadi sosai, bayan indo ta fita Mum tace akira A Majeed ya karasa ma indo sauran sakin, his excellency yace babu kyau saki uku duk da daya yayi mata bana ma tunanin zai dawo da ita tunda ya tsaneta kawai ki barshi .
Chapter 18 · 0% Book details