← Book details Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 59

Sashe 35

Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Gaba daya ranshi yaji ya baci sosai, sai huci yakeyi kaman tana gabanshi, wata irin iska ya furzar mai zafi, tare da kwanciya ya lumshe ido yana mai jin zafin kalaman nata, tuna irin soyayyan da sukayi da yayi Zainab macece mara caring da nuna I don't care akan abubuwa masu muhimmanci, yaushe raban da yayi kwanciyan aure da ita tun kafin ta tafi shima d way yanda ta mishi itace take bukata, wani irin zafi yake ji a ranshi miye dan na kara aure niban kasance mazinaci ba, ina da bukata sosai nima mutum ne ba dutse ba, karan wayanshi ne ya fargar Dashi daka tunanin daya lula, Abdul ne yace Man gani a waje ka fito muje, A Majeed yace ka shigo mana, idan mukayi magrib sai mu wuce, abdul yace OK, horn yayi aka bude mai gate din gidan ya shiga, a falon Gidan ya zauna babu kowa a cikinsa, A Majeed wanka yayi tare dayin alwala yayi wajan 30minute kafin ya fito wai dan ma ana jiranshi ne, masallacin kofar gidan suka nufa, sukayi sallah, bayan an idar Abdul ya gaisa da mai girma sanata, sannan suka wuce, wuse2 suka nufa inda gidan yake a kofar wani dangareren Gida suka faka,fita dukansu sukayi inda A Majeed ya bude gidan suka shiga, gidan kato ne sosai ga fulawowi gwanin Sha'awa, Abdul yace kai gidan babba ne kaman ma na mata biyu ne ginin dan kaga can gefen Da can, A Majeed yace aysha na ita kadai zata zauna ban san a takura mata, dariya abdul yayi, sannan suka shiga cikin falon, hmm fadan kalan tsaruwan falon bata lokaci ne, kujeru kala biyu ne a falon kuma manya2 masu tsadan gaske, kofofi uku suka gani a falon, dayan kitchen ne dayan bedroom ne dayan kuma wani karamin falo ne, sama suka haura, bedroom hudu ne a saman sai falo guda daya shima mai kyan gaske komai dai yayi babu abunda ake bukata, sauka sukayi Suka zaga baya ta kofan kitchen bukka ne a wajan Da garden, ga kujerun robobi a wajan abun Sha'awa,haka shima dayan gefen komai iri daya sai dai shi ba'a sa kaya ba, Abdul yace Man gskya Gidan nan yayi sosai, A Majeed yace hakane babu abunda yake bukata, nan suka fita tare da rufe gidan, A Majeed yace plz kasan yanda zaka sa aysha ta fito in ganta, Abdul yace kai nifa babu abunda zan karayi maka na gama nawa, A Majeed yace Kana da problem Abdul, dariya Abdul yayi tare da fadin ai gaskiya na fada, bayan sun karasa gidan Mum a lokacin ana kiran sallah isha'i masallaci suka nufa, bayan sun idar Abdul ya wuce duk Da A Majeed yaso su shiga amma yaki yace akwai masu jiranshi, koda A Majeed ya shiga baiga kowa a falo ba, dakin Mum ya nufa yaga bata ciki har zai wuce dakinshi yaji maganan Mum din a dakin da aysha din take tsayawa yayi tare dayin baya, shiga dakin yayi yaga Mum din a zaune gefen gado aysha din na kwance daka gani zazzabi takeyi, da sauri ya matsa tare Da fadin Mum maike damunta indo dake kwance taji maganan nashi kaman a mafarki dan bata san ya dawo ba, dan bude ido tayi wanda a dai2 lokacin ya karaso wajan sukai ido biyu kirjinta taji ya buga, Mum tace fever ne kaman, yace bari muje hspt sai a dubata Mum tace na kira Dr yanzu zata zo, kallon aysha din ya kuma yi tare da fadin sannu ya jikin kai kawai ta daga mai ba tare data amsa ba, Mum tashi tayi tabar dakin tare da fadin bari in jira Dr din a falo, ganin Mum ta fita yasa ya zauna akan gadon idanta a lumshe jin hannunshi tayi a saman goshinta wani iri taji tare da bugawan zuciya,batai aune ba taji hannunshi a wajan wuyanta yana tabawa tare da dan daddanawa cikin muryanshi mai kama da kasala yace jikin naki da zafi sosai tun yaushe kike jin zazzabin bata kulashi ba, sai bugawan da kirjinta yake mata tare dajin haushin taba ta din da yakeyi,dan har yanzu hannunshi na wuyanta ,idanshi gaba daya yana kanta ji yake kaman ya jita a jikinshi, cire hannun nashi yayi daka jikin nata dai2 lokacin Mum ta shigo ita Da Dr, nan ta fara dan dubata tare Da fadin fever ne Dr Aysha kina Dr ya zaki bari fever ya kamaki haka baki sha Magani ba, indo murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba, nan taba indo Magani, sannan ta wuce Mum tace bari in hado miki tea sai kisha kafin kisha maganin, A Majeed ganin kowa ya fita yasa ya koma kusa da ita ya zauna yana mai jin tausayinta, Mum bata dadeba ta dawo, dauke da tea din, ganin A Majeed din a wajan yasa ta bashi tea din tare da fadin tashi kisha ina zuwa fita tayi tabar dakin dan taga dan nata nason nuna fitsaranshi a gabanta, ajiye tea din yayi tare da dagota ya zaunar da ita, idanta a lumshe maganar shi taji a wajan kunnenta yana fadin plz gashi kisha bude ido tayi taga yana kallonta yana sakar mata murmushi da sauri ta kawar da kanta gefe dan murmushi ya kuma saki komai tayi kyau yake mata Cup din yasa mata a baki dan haka ta fara sha, bata wani shada yawa ba, ta kawar da kanta duk yanda yaso ta kara amma taki, Magani ya bata tasha aiko Tana sha ta amayoshi kusan rabin aman a jikinshi duk da bamai yawa bane,dan bata kaunar Magani ko kadan, duk da tana cikin yanayi na ciwo saida gabanta ya fadi ganin tamai amai a jiki, amma ga mamakinta sai taga koh a jikinshi saima rudewa da yayi yana mata sannu tare da daura hannunshi a bayanta yana shafawa a hankali, ganin kaman aman ya tsaya yasa yace tashi in tayaki ki gyara jikinki, wani irin kallo tamai wanda yasa shi murmushi duk da yaso ya dake, hannunshi ta ture daka jikinta tare da tashi dakyar tafiya ta farayi kaman mai koyan tafiya ido ya bita Dashi yana jin sonta na fisgarshi, ganin ta shige toilet yasa ya tashi ya fita,daya daka cikin masu aikin gidan ya kira yace suje su gyara mata daki, sannan ya nufi dakinshi dake gidan toilet ya fada yayi wanka koda ya fito shiryawa yayi yasa jallabiya, fita yayi dan yaga jikin nata kafin ya kwanta, koda ya nufi dakin ya bude kofar a rufe ya jishi, babu yanda ya iya dole komawa yayi badan ranshi yaso ba.

Koda ya koma daki kasa bacci yayi domin tunanin halin da take ciki yaita yi, wayanshi ya dauko danya kirata, lokaci daya kuma yayi tsaki tare da ajiye wayar dan bashi da number dinta, ido ya lumshe yana mai jin takaici na rashin number din nata, gashi yanzu idan ya kira Abdul yace ya bashi sai yayi ta mishi surutu May be ma ya Tuna mai baya, haka dai ranan yaita tunani bai san Lokacin da bacci ya daukeshi ba, ta gefen indo zazzabin ya dan sauka kadan ita da kanta ta rufe kofar gudun kar yace zai kara shigo mata ile sai gashi Tana jin lokacin da ake kokarin bude kofar dan tasan ba mum bace tasan shine, sai yasa bata bude ba kuma batai magana ba, domin bata bukatar ganinshi kusa da ita dan haushin shi takeji sosai, daka ta ganshi take tunawa da messages din da yazeed yai mata wannan dalilin yasa ta kara tsananshi fiyeda nada.
Chapter 35 · 0% Book details