Sashe 1
Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
[12/10, 22:01] Maryam Muhammad Fkb Hausa Novels Kd: 💅 TAMBARIN TALAKA 💅
1to5
https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/
Alhmdlh godiya ya tabbata ga Allah wanda ya sake bani daman rubuta wannan labarin bayan na kammala "SAINA AURESHI" Allah ka bani ikon gama wannan littafin lafiya dan alfarman annabi Muhammad (S A W)
PLZ BANDA YAWAN KORAFI BANCE KAR AMUN GYARA BA, BUT IN ZA'AYI GYARAN AYI TA HANYAR DAYA DACE PLZ👏
Gida ne ginin kasa wani wajan ya rufta, an rufe da buhu, saman kwanan ya tsofe duk yayi tsatsa, kana ganin gidan kasan lallai talauci yana cikin gidan dumu2, dan haka na shiga gidan in dauko muku bayani dakyau, daki uku ne a cikin Gidan, ciki da falo guda biyu,sai wani karamin daki, dakunan duk ba wasu girma garesu ba, jin gunjin kuka a karamin dakin yasa na le'ka, wata yarinya da bazata wuce shekara goma sha bakwai ba, naga Tana kuka tare da shesheka, fara ce amma saboda wahala farin nata ya boye, Tana kukan ne rike da cikinta domin yunwa take ji, kaman zata mutu,wata mata ta leko dakin ta Saki baki tare da fadin au kuka kikeyi sai kace wanda aka bigeki, jar uba, shiga dakin tayi ta cakumi wuyan yarinyar Tana fadin bari inci ubanki sai kiyi kukan da hujja, matsiyaciya, dukanta takeyi tako ina, yarinyar na fadin dan Allah inna tani kiyi hakuri,amma Tani ko a jikinta domin hakurin da take bata kaman ma Kara zugata takeyi, saida ta mata lilis ta tabbatar data daku sannan ta barta Tana fadin yar iskan yarinya kinzo kina kuka a daki, maza ki fito kije ki siyomin garin tuwo, kuma wlh idan kika dade sai jikinki ya kuma gaya miki, dakyar ta tashi jiki babu kwari ta amshi kudin sannan ta fita, bata wani dadeba ta dawo, tani ta watsa mata harara tare da fadin maza kije ki hadamin huta kafin yan sa ido suce bana baki abinci, ta amsa da toh, ta nufi murhun, wata mata ta fito daka dayan dakin Tana fadin wlh tani kiji tsoran Allah, yarinya bata miki komai ba kullum ki kamata ki jibga, anya tani kina tuna mutuwa kuw...... Dallah dakata munafuka ke har kin isa ki dinga shiga sabga ta wlh ahir dinki, ni nafi karfinki wlh, kuma karki manta a karkashina kike domin nan gida nane, matar tace gidanki ko gidan marayu? Nan Suka dunga gayama juna magana ita dai indo tuwo ta daura amma ji take kaman a tsakiyan kanta suke wannan ihun,..... Wacece Indo?
WACECE INDO
Mlm aminu shine mahaifin indo, mazaunin taraba ne a karaman hukuman karan lamido, fulani ne na taraba, yana da mata daya maryam, mlm aminu talaka ne bashi da kudi, domin nanin takalmi yakeyi, gidansu gidan kasa ne,duk da talaucin shi, gidanshi Alhmdlh suna ci koda babu dadi ciki zai dauka, domin mlm Aminu yace TAMBARIN TALAKA CIKINSA, koda ba'a sami tuwo ba za'asha fura ko gari,cikin farin ciki, Mlm Aminu suna zaune da kanin shi a gidansa mai suna musa, yana da mata tani, tana da yara biyu mata, bintalo tayi aure sai abu, Sa'ar indo, tani azabbar Mace ce domin sai abunda tace ma musa yakeyi, ita kuma maryam Tana da hakuri sosai sai yasa mijinta ke sonta, yaran mlm Aminu biyu, yusuf wanda saida ya shekara biyar kafin aka haifi aysha indo, wanda suke kira da indo, aysha tun Tana jaririya take dakyau gata fara sol, Tana da shekara 7 a duniya mahifinsu ya rasu, tun daka lokacin rayuwa ya canza musu, musa ya kanaye gidan duk da bashi da Gado domin Yusuf ya musu katanga, wannan abun yasa Mlm musa tsanan maryam da yaranta musamman ma Yusuf, maryam tun rasuwan mijinta take ta fama da ciwo sosai, wata rana Tana zaune da yusuf da indo a daki bata jin dadin jikinta, ta kalli yusuf wanda ya kusa gama secondary, tace yusufa dan Allah koda bayan raina inaso ka kula Min da indo karka bari tayi maraici domin bata da kowa sai kai, Yusuf jikinshi yayi sanyi yama kasa magana yana sauraranta idonshi ya kada yana zubar da hawaye, itama indo duk da batayi wani wayau ba ganin halinda suke ciki yasa itama ta nutsu Tana hawaye, maryam taci gaba da fadin yusufa duk rintsi ka kulan min da ita karka bari tayi zaman kadaici ka zame mata uwa da uba, domin bata da kowa sai kai, ni nasan ciwan nan bazai barni ba, naso inyi tsawan rayuwa dan in kasance daku, amma bana jin hakan zata faru, Tana zuwa nan ta fara hawaye taci gaba da fadin sannan inaso kabar indo tayi karatu dan Allah domin tayi alfahari da kanta wata rana,rayuwan Mace kalilan ne, Tana fadin haka ta kamo hannun yusuf dana indo ta rike tana murmushi, lokaci daya bakinta yayi motsi Tace ga garinku nan, Allah ya mata rasuwa, Yusuf da indo sunsha kuka sosai har tani ta tausaya masu, haka rayuwa ta kasance musu tun daka lokacin rikonsu ya dawo hannun kanin babansu mlm musa da Matar shi tani, mlm musa ya kane naye gidan ya zama nasa, dan haka ya kullama Yusuf shairi kan cewa yana neman kanwarsa, mai gari ya kori Yusuf daka garin kan cewa duk sanda ya sake zuwa sai an kashe shi, wannan ne sanadin barin Yusuf garin mlm musa da tani Suka kanai naye gida Suka sa yar haya mai suna jamila, tana tausaya ma indo sosai sai dai babu yanda ta iya, tani taci gaba da musguna ma indo bata zuwa islamiya balle boko sai daukar ma tani tallan kayan sana'a yau tani tayi wannan gobe tayi wancan kuma idan Indo bata saida ba sunanta sorry, domin ranan sai taci duka sosai, kuma ta hanata abinci, mlm musa idan ya dawo shima ya kara mata wannan shine rayuwan Indo.....
Taku Maryam obam😘
[13/10, 22:52] Maryam Muhammad Fkb Hausa Novels Kd: 💅 TAMBARIN TALAKA 💅
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
5to10

Indo ta kammala tuwan ta kwashe sannan ta daura miyan kuka, bata jima ba, ta kammala miyar koriya shar dan ban tunanin ansa manja a ciki, dakin tani ta nufa da sallama, kaman dai kullum tani bata amsa ba dan haka tace inna na gama, tani tace toh dan uwarki a bakin kofar zaki tsaya ba zaki shigo ki Kawo min ba? Cikin sauri ta bude bakin labulan daya canza kala daka fari zuwa milk colour, ta Shiga jiki a sanyaye bayan ta ajiye ta dan tsaya ko zata bata nata, tani tace uban Me kike jira kuma mayya mai bakin hali, Ai yau tunda kika ja wancan bakar matar tamin tujara wlh baza kici wannan abincin ba , ta sakar mata rankwashi mai zafi tare da fadin fitar min a daki kar ki tasar min y'a, simi2 ta fice hannunta nakanta Tana hawaye dan taji zafin rankwashin sosai, dakinta ta shiga ta kwanta akan tabarman ta, kuka takeyi Tana fadin yusufa dan Allah kazo ka tafi Dani tun kafin inna tani ta kashe ni, duk da inda Tana yarinya lokacin da mamanta ta rasu ta rike wasu abu, musamman burin mahaifiyarsu na indo tayi boko, amma gashi babu islama balle boko, duk da itama indon tana so amma babu dama dan tani fur tace talla zata dinga mata domin kan indo bana boko bane, na daukan kayan tallah ne, haka indo ta kwana da yunwa duk da baccin da tayi rabi da rabi ne domin yunwa ga yunwan dare bashi da hankali amma duk nacinta haka tabar indo,