Sashe 58
Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
yace mlm musa ka gode Allah yarannan basu rikeka ba mlm Musa yar guntun kwallanshi ya fito yace hakane shairin shaidan ne da kuma makiran matar dana samu , suna cikin magana sai ga dan jummai wasû samari sun rukoshi sun mai jina2 ga jummai kuma nata kuka mai gari yace lafiya? Matasan suka ce kanwar mu yama fyade kuma yasan yana da HIV nan mai gari ya Saki salati tare da kiran yan sanda aka tafi Dashi jummai nata bada hakuri akan a barshi mai gari yace idan ta kara magana sai an hada da ita taja baki tayi shuru tare da kokarin barin wajan mlm musa yace jummai ga indo koh baki ganeta ba ashe Allah ya taimaketa da yanzu danki ya kashe ta da sauri ta kalli indo sai kuma ta kara fashewa da kuka tace Allah sarki wlh yaso ya aureta lokacin nice na shiga na fita na hana auren mai gari yace kinga koh kin taimaketa ga tarin zunubi da kika tara ma kanki haka jummai tabar wajan jiki a sanyaye, Yusuf yace tunda A Majeed ya dauki komai shima ya bari ya samu lada yakai Tani asibiti hakan akayi a ranan aka samo mota aka tafi da ita asibiti su indo kuma suka koma Abuja dan A Majeed yace baza su kara kwana ba, bayan sun Isa Abuja taga A Majeed ya wani tamke fuska bata kulashi ba taja hannun yaranta sukai ciki tunda suka dawo bai shigo ba Dan yau gidan zainab yake, ta mishi uziri dan tace May be gajiya yayi ga yaranta sun dameta dady dakyar ta samu sukai bacci washe gari har wajan 5 bai shigo ba gashi ta kirashi yaki dauka sai wajan isha taji ihun yara suna daddy lokacin Tana kitchen batai fushi ba ta fito domin bai taba mata haka ba tace daddy lafiya kuwa inata kira kaki picking kodai gajiyan ne yasa haka? Wani irin kallo ya mata Da yasa tayi shuru Tana mamakin mai tayi wasa yayi da yaran sannan yaja su dakinsu yasa musu kayan bacci yace suyi bacci dare yayi dan kullum haka yake musu sai yasa jiya da bai zoba Suke ta rigima, bayan Ya fito ne ta nufeshi amma kallo daya ya mata ya kauda kai tace my one tafiya yaci gaba dayi bai tsaya ba da sauri ta nufeshi tayi hugging dinshi Tana kuka tare da fadin mai nayi mijina yake fushi dani kukan nata yaji har ranshi a hankali ya rikota tare da dago mata Kai yace aysha mai yasa kike kuka lokacin da kika ga saurayinki ya tashi dama har yanzu kina sonshi tace haba My One kasan Kai daya nake so dama akan wannan abun kake fushi kawai tausayi yaban saketa yayi tare da fadin sai kiyi tajin tausayin nashi ai kara rikeshi tayi ta fara rarrashin shi dakyar ya hakura tare da fadin baya son ma ya kara jin tayi maganan sulaiman dariya tayi sosai tace ta yarda ankai Tani da kwana biyar asibiti ta rasu wanda yasa indo dole ta koma kauyen kasancewan an fara aikin gidansu a gidan mai gari ake zaman makoki sam A Majeed yaki yarda indo ta kwana wai jalingo zasu koma hakan akayi dan su biyu suka zo yaran na wajan Zainab dan ta yaye su nono bai damesu ba, kwanan su uku suka koma taso ta dauki Abu amma yusuf yace gidanshi zata koma da zama tare da Abu Yusuf ya koma abuja, duk wannan abunda ake indo nada ciki bata sani ba dan tana period dinta rannan suna zaune da A Majeed yace Baby anya ban baki ajiya ba kalli yanda kika kara cika da kyau tace haba My One yanzu idan nayi ciki ai na shiga uku banfa manta wuyan da nasha ba kuma su zarah ko shekara biyu basu yi ba kaga aiko su sun ishemu yace Baby nifa ina son yara wannan ma Mum so take mu bata su naki ga Zainab itama Tana So kinga idan kika kara haiyuwa sai aba Mum da zainab tunda yan uku nake baki dariya tayi tare da fadin Na yafe tashi tayi ta nufi daki dan itama Tana dan jin canji aiko gwajin farko data gwada taga Ciki ne cikin tashin hankali ta koma inda ta barshi tace my one na shiga uku wlh ina da ciki dan Allah muje a zubar wlh banso in kara haiyuwa yanzu, daka mata tsawa yayi tare da fadin wlh idan kika zubar min da ciki saina Saba miki wlh yana fadin haka yabar falon rai bace ita ko kuka ta Saki mai karfi tare da fadin wlh bazan yarda ba inna mutu aishi kenan dama ba sona yake ba kuma ciki ne wlh bazan yarda Dashi ba koda A Majeed ya fita dakin Zainab ya nufa ya ganta Tana kuka da sauri ta Fara gogewa kallonta yayi tare da fadin Zainab lafiya kuwa? Cikin kuka tace A Majeed na kasance ina son haiyuwa naje asibiti da dama ina amsan Magani dan in haiyu duk bada saninki ba Amma daka baya sai akace bazan iya haiyuwa ba wai mahaifata ta sake inko na samu ciki komai zai iya faruwa Dani duk da bama sa iya tunanin zan haiyu kullum inna Tuna da wannan abun nakanyi kuka ina dana sanin shan...... Shuru tayi dan tunawa da tayi dawa take magana, yace Zainab shan me?? Shuru tayi lokaci daya kuma ta kara sakin kuka tace A Majeed shan maganin hana daukan ciki ya jefani cikin wannan Bala'in dan Allah ka yafe min wlh nayi maka laifi ina shan Magani ba tare da saninka ba gashi yanzu ina son haiyuwa ido rufe amma babu dama kukan da takeyi ne duk da ranshi a bace yake yasa ta bashi tausayi har ya fara rarrashinta tare da tunanin aysha na gudu ita gashi wannan Tana nema duk da ita taja ma kanta.