← Book details Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 59

Sashe 16

Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Zabe yana ta gabatowa domin his excellency wannan karan Senate yake son zuwa, anata campaign, Mum Tana Bussy kwana biyu domin akwai masu taya mijinta campaign mata da ita take basu duk wasu abu da suke bukata, indo itama takan taya Mum da bata shawara musamman da taji his excellency yace yana son a kara yawan titi ayi a layi2, indo ta sami Mum a daki tana zaune ita daya, Mum tace aysha dazu nazo ai naga kina bacci, indo tayi murmushi tare da cema Mum barka da hutawa, Mum ta amsa da yauwa, nan indo tace ma mum akan titi din da his excellency taji yana fada idan aka karayi zaisa talakawa suji dadi, indo tace Mum inaga shi talaka baya bukatan titi ta kofar gidansa indai akwai a babban hanya, shifa *TAMBARIN TALAKA* rumbun sa, indai talaka zai ci ya koshi bashi da matsala domin shine burin shi, inaga da ayi wannan titin gwara an raba musu jari koh da babu yawa, Mum da tunda indo ta fara magana take kallonta da mamaki yanda har tayi wannan tunanin mai kyau, Mum tace kai aysha gskiya kinyi tunani mai kyau, anya ma Ba political science zaki karanta ba? Indo dariya tayi kawai, Mum tace hakan za'ayi gobe zan kira meeting sannan anjima kadan zan gayama his excellency wannan shawaran, koh da Mum ta sanar ma his excellency wannan shawaran yaji dadi sosai tare da cewa gskiya kinyi tunani mai kyau, Mum tace bani nayi wannan tunanin ba aysha ce, yace wace Aysha? Tace matar A Majeed, yace yauwa suna nan lfya dai koh, dan ina tsoran wannan yaron, kwanaki yazo ya sameni akan a raba auren naki yarda, mum taba his excellency labarin abunda yayi tare da gaya mishi yarinyar tana nan gidan, ranshi ya baci sosai tare Da fadin dan mai yasa Mum bata gaya mishi ba sai yanzu, daukan wayanshi yayi ya kira A Majeed, bayan ya dauka yana gaidashi amma his excellency bai amsa ba sai ma fadin da yayi kazo jalingo gobe da safe sannan ya kashe wayan, his excellency yace ma mum tunda ya aureta dole ya zauna da ita ban yarda da zancen saki ba, gobe dole ya tafi da matarshi in yazo Mum za tayi magana ya dakatar da ita tare da fadin ban san jin komai naga In akabi ta Yaron nan saiya zubar min da mutunci tashi yayi tare da cema Mum ina da meeting sai na dawo.

Taku Maryam obam😘

*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*

*NA*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*

*WWW.maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

95to100

*DEDICATED THIS PAGE TO....*

*ZAINAB ZEE BABY😍*

Mum shuru tayi tama rasa abunyi, harga Allah itama Tana son indo ta koma gidan mijinta sai dai tana gudun irin zaman da za tayi a abuja din, haka taita tunani kala2, tare da tausayama indo din, domin tasan tunda A Majeed ya iya bude baki yace baya sonta a gabanta tasan tabbas idan aka matsa mai akan indo din zai iya yi mata wani abun ko matarshi, Mum gaba daya ta kasa sukuni zama tayi tana jiran mijin nata ya dawo suyi magana, koda his excellency ya dawo Mum ta mishi magana akan a bar indo a nan yace hakan bazai yihu ba, bawai an aurota bane dan ta zauna dasu ba, dole gidan mijinta zata zauna, ganin tashin hankalin da matar tashi ta shiga yasa ya kamo hannunta yace kiyi hakuri babu abunda zai faru nasan abunda kike gudu, insha Allah babu abunda zai faru zanja mai kunne sosai karki damu, Mum ajiyan zuciya tayi ta danji dama2.

A Majeed duk da yau monday amma haka ya tawo jalingo tare da tunanin lfya dad yake neman shi, karfe goma da wani abu ya sauka a jalingo, gidan shi ya sauka sai da ya kimtsa domin baya tunanin ko yaje gida zaiga Dad dinshi yanzu, wajan 12 ya nufi gidan nasu koda ya isa anata kiran sallah masallacin dake kofar gidansu ya nufa mutane ancika sosai ciki harda mai girma governor, bayan an idar, his excellency yana ta gaidawa da mutane yana jin matsalan su, wanda hakan ya zame mai jiki kullum in yana kasar yana sauraren kukan mutane, tare da dan nasa Suka shiga gida, a falo suka sami Mum a zaune tana karanta news paper, A Majeed wajanta ya nufa yana fadin sannu da hutawa my mum, mum murmushi tayi tare da fadin yauwa ya hanya? Ya amsa da lafiya his excellency zama Yayi Mum ta tashi ta nufi kujeran daya zauna tare da fadin food is ready fah, yace ok tashi yayi Suka nufi dinning wasu manyan kuloli ne Sun kai goma akai kana ganin hummer din kasan masu tsada ne, abinci kala2 na gida dana waje, Mum ta zuba ma mijinta da dan nata, suna ci suna taba fira sama2 A Majeed shidai ya kosa yaji ko miye Dad ke neman shi, har Dad ya kammala ya kalli A Majeed yace ka sameni falon sama inka gama, Mum ta tashi tabi mijinta saman itama, A Majeed kasa cin abincin yayi tare da tambaya toh maiya faru wata zuciyar tace may be Akan campaign dinshi zasu tattauna dan haka yaci gaba dacin abincin shi, sannan ya haura sama, A kan kujera yaga Dad Mum na gefenshi, shima samun waje yayi ya zauna, Dad yace Abdul-majeed Ashe baka da kirki? Dam A Majeed yaji gabanshi ya fadi dad yaci gaba da fadin dama har yanzu baka hakura da maganan aurenka ba, toh wlh baka isa ba domin ba zaka maidamu mutanan banza ma, mum dinka tamin bayanin komai dan haka in zaka tafi zaka wuce da matarka sannan wlh kar inji kar in gani in naji ka mata wani abu wlh sai nayi mugun saba maka, Dad yaja mishi kunne sosai daka karshe yayi mishi nasiha, A Majeed gaba daya takaici ya isheshi koda zai koma gidansa Dad yace su tafi tare da matarsa babu yanda ya iya, nan Mum tasa indo ta fito su tafi tare dasa masu aiki su hada mata kaya, gaba daya an hadama indo kayanta, Mum tace ta tafi da kadan sauran driver zai kawo Mata abuja din Indo babu abunda take sai kuka domin bata son rabuwa da Mum ga karatun ta,sannan bata san zuwa gidan A majeed, domin harga Allah tsoranshi take ji sosai, Mum tayi mata nasiha sosai tare da fadin komai ya mata ta kirata ta fada mata, ta dauko waya taba indo tare da fadin akwai number dina a ciki, indo ta amsa tare da godiya,mum tace zata sa a bata transfer na skul dinta sai ta farayi a abuja, indo taji dadin hakan sosai, har mota Mum ta rakata A Majeed yana mota a baya fuska daure kaman ance mamanshi ko babanshi ne wani ya rasu, Mum baya ta bude ma indo itama ta shiga tare da fadin aysha komai aka miki ki kirani ki fadamin kinji tana fadin haka ta rufe musu motar, driver yaja, indo kuka take kasa2, A Majeed wani irin takaici yake ji gashi baya son yin wani abu a gaban driver direct gidanshi Suka nufa, fita yayi ya shiga ciki da sauri, itama fita tayi ta dauko akwatin ta karami taja tai ciki, dakinta na gidan ta shiga, ruf da ciki tayi akan makeken gadon dakin tana kuka, tare da tunanin wani irin rayuwa za tayi a gidan A Majeed, karan wayanta ne yasa ta dan tsagaita kukan tare da dauka taga Mum ce ,shuru tayi tare da kara goge hawayen fuskanta ta dauki wayan mum tace aysha baiyi miki komai ba koh? Tace eh Mum, mum tace toh shikenan indai ya miki wani abu ki fadamin zan dauki matakin daya dace akai, tace toh Mum sannan sukai sallama.
Chapter 16 · 0% Book details