Sashe 2
Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Washe Gari tunda asuba indo ta fara share tsakar gidan wanda babu suminti sai 'Kasa, duk da garin bai gama haske ba, domin tani tace indai ta fito batai shara ba sai taci ubanta sai yasa takeyi daka ta idar da sallah, bayan ta gama sharan ta dauki bokiti domin dibo ruwa a rijiya, gidan da take dibo ruwan basu tashi ba dan yar kofar kyauran nasu a rufe yake dan haka ta nufi rafi domin ta dibo rafin akwai nisa sosai kuma yawanci maza Suka fi zuwa, domin yan iskan garin anan suke taruwa in Suka ga mace har fyade suke mata, haka indo ta nufi rafin dan tasan indai ta koma tani taga babu ruwa toh kashinta ya bushe , Allah ya taimaketa bata ga kowa ba harta gama diba, sannan ta fara hada kayan wanke2 a lokacin tani ta fito Tana hamma kaman za taci mutum, gefen murhu ta kalla sannan ta kalli indo tare da fadin amma ke ko matsiyaciya yanzu murhun ma baki hada ba, dan iskanci, indo tace kiyi hakuri inna So nake idan na gama wanke2 in hada, tani tace au yanzu har sai kin gama wanke2 bayan Kin san abu bata da juriyan yunwa, wlh kafin in fito daka bayi ki hada murhun nan, indo da sauri ta nufi murhun Tana hadawa bata dadeba wutan ya kama danma itacen busashene, tani ta fito daka bayi ganin wutan naci tace maza ki daura ruwan kunu tunda kullum ke sai an fada miki, Daura tukunya tayi,tare da hada kayan wanke2 Tana cikin yi abu ta fito Tana fadin tani an gama kunun? Tani tace ina fah wannan mai idon kaman na mayu ta tsaya bata lokaci kuma tasan sarai bakya jure yunwa, Abu tace wlh tani laifinki ne aida kinci ubanta nidai yanzu yunwa nakeji gaskiya, tani ta tashi ta nufi indo wai dan uwarki ba zaki duba ruwan koya tafasa ba, Indo jiki na rawa ta tashi dan kar tasha duka ga yunwa Tana ji, bude tukunyan tayi ruwan yana alaman tafasa, ta kalli tani tace inna yanzu zaiy....kafin ta karasa taji saukan mari ke wace irin yar iska ce, kunu tun dazu kin kasa gamawa, bayan kin san sarai abu bata da hakurin yunwa shegiya mai bakin hali, dakikiya komai sai anyi ta nanata miki, bakya daukan komai, indo data rike fuska dan zafi ta nufi tukunyar dan taga alaman ya tafasa, daukan ruwan tayi ta juye a kunun tare da rufewa, tani ta dauki kunun tayi daki dashi ,indo taci gaba da wanke wankenta, duk wannan abunda akeyi jamila na daki Tana ji amma babu yanda ta iya, bayan indo ta gama aikinta ta nufi dakin tani tare da fadin inna na gama, mlm musa yayi tsaki tare da fadin wannan yarinya ko mayya naso ace itama ta mutu tabi iyayenta matsiyaciya ita dai kanta na kasa dan bata san yana ciki Bama, tace ina wuni abba, yace ni ba abbanki bane ki kirani da musa na, mara mutunci kawai, tani ta tura mata kunu dan kadan a kofi tare da fadin gashi mayya dan nasan danshi kikeyi, indo ta amsa tare da fita daka dakin tunda ta kafe kanta a kofin saida ta shanye kunun sannan ta ajiye, jinta take kaman bata sha komai ba, domin kunun dan kadan ne, Tana zaune a dakinta tani ta bude dan kyauren Tana fadin au ba zaki zo ki fere rogon ba, indo tashi tayi tani ta kai mata rankwashi akai, tare da fadin mayya kawai, indo fere rogon take tayi, sannan ta daka, bayan ta daka ta dauko karamin abun nikansu na dutse, haka ta dinga nikawa yana laushi sannan ta kwashe tasa wani, bayanta da hannunta babu abunda yake sai ciwo kaman zata mutu dan azaba domin bayanta yayi mugun rikewa, ga rogon da yawa, bayan ta kammala tani ta fito ta hada tare da mummulawa harta gama sannan ta kirga tace ma indo ta soya, bayan ta gama suya tani tace na dubu biyu da dari hudu da ishirin ne wlh ki tabbata kin dawo mun da kudina dai2 sannan karki dawo min gidan nan in baki siyar ba, indo ta amsa da toh sannan ta dauki buta dan ta wanke Jikinta tani tayi saurin cewa ajiye min buta uban me za kiyi dashi? Indo tace zan wanke jiki nane, tani ta tabe baki tare da fadin dama kinzo kin wuce dan banga amfanin wanke jikin ki ba, haka ta ajiye butan ta fita, hanyar tasha ta nufa domin tasan anan zata fi saurin yin ciniki wata mota ce ta danno da gudu indo garin saurin ta matsa wainar rogo ta kife a kasa.......
Taku maryam obam😘
[14/10, 20:53] Maryam Muhammad Fkb Hausa Novels Kd: 💅 TAMBARIN TALAKA 💅
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
10to15
https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/
DEDICATED DIS PAGE TO AYSHER HUYMERAH LIKYMO❤
Indo kuka ta Saki Tana kallo ganin babu komai a roban domin duka ya zube a kasa, gashi mai motan bai tsaya ba, yara ne Suka fara wawa suna diba, indo ta tashi Tana kuka Tana kora yaran idan tabi wannan ya gudu wani ya dawo haka Suka maidata kaman mahaukaciya, ganin yaran Sun kwashe duk da kuwa akwai kasa a kai yasa indo zama a gefen titi Tana kuka kaman wacce akace mamanta ta mutu, duk wanda yaga yanda take kuka saiya tausawa mata, sai dai kuma duk masu tausaya mata babu wanda zai iya biyan kudin domin kowa nata kanshi, duk wanda yaji abunda ya faru sai dai yace mata Allah ya kyauta ko kuma yace yara basa duba hanya sai suyi ta sako kai bakin titi, indo saboda tashin hankali yasa ko yunwa bata ji duk da kuwa ta diba lokaci mai tsawo a wajan Tana kuka, domin bata ma tunanin Zuwa gida, dan tasan yau in taje gida kwananta ya kare domin tani kasheta za tayi, indo ta tsine ma mai motan nan yakai sau dubu tare da fadin ko waye wannan ya cuceta
Tani keta faman surfa ashar Tana fadin wlh yau saina ci uban wannan yarinyar yanzu har an kira magrib bata dawoba, kai wannan ko yar iska, kullum sai ta Sani surutu yau zanyi maganinta wlh saina nuna mata ni tani bani da imani wlh, abu tace yoo tani bakece kike Raga mata ba, sai yasa ta raina ki ba, inda kina dukanta kullum kaman sau goma a rana aida tabar miki iskanci, Tani tace kin san gidan akwai yan tsurku masu jira ayi suyi ta yayata ka, kaman ka kashe mutum ko an Kama ka da kato, abu tace tani yasin mu kori wannan jamilan munafuka ce, rannan fah da kika fita har daba indo abinci tayi ina daki ina ji, Tana cewa tayi sauri taci Kafin ki dawo, tani tace bura uba yaushe akai hakan shine baki fada min ba, abu tace rannan mana, tani ta tashi fuuu tayi kofar jamila ta fara fadin fito bakar munafuka, jamila dake daki duk Tana jin abunda suke fada,ta fito Tana fadin karki balla min kofa wlh tani ki fita a idona, tani tace jar uba, ni kike fadama haka toh wlh yau sai kin kwashe kayanki kin bar min gida, bakar munafuka, jamila tayi dariya tace saiki dawo min da kudin hayan dana baki, nan tani tayi shuru domin ta rasge kudi, ganin tani tayi shuru yasa jamila fadin wlh tani kiji tsoran Allah yarinyar nan marainiya ce, bakya jin tsoran hakkinta ya kamaki duk kin kanai naye dukiyar su keda Mi...... Dallah yimin shuru ina ruwanki wlh jamila ki fita daka idona wlh ni da kaina ina tsoran kaina wlh karki hasala ni wlh idan baki fita daka idona ba saina maidaki abun tausayi, jamila tayi murmushin takaici tare da fadin wlh tani ina guje miki hakkin yarinyar nan ya kamaki amma tunda kince haka kije kiyi tayi kema Ai kin haifa, tani tace toh mai bakin baki babu abunda zan gani Dani da yarana sai alkhairi, nan tani taita zagin jamila ganin haka yasa jamila ta koma daki tare da fadin kudinsu na karewa zasu bar gidan dama mijinta tun tuni yake cewa su tashi amma tace ita tafi son zaman nan, yaso ta bishi cikin taraba inda yake aiki tace a'a, amma wannan karan zata bishi ko kuma su canza Gida.