← Book details Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 59

Sashe 52

Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Yau satin indo biyu gidan Mum A Majeed kullum yana sintiri gidan shi duk ya kosa matarshi ta dawo Gida itama ta gefen indo din hakane dan Tana son ta jita jikin mijinta musamman kamshin jikinshi da take masifar so, yanzu ta rage yawan bacci sai dai kwadayi dason abu mai yaji, Tana zaune A Majeed ya shigo dakin da take tace yauwa my one rogo nakeso plz, yace rogo dan shuru yayi tare da tunanin miye shi dan bai san abun ba, tace eh yace a ina ake saidawa? Tace nima ban sani ba ni kawai shi nakeso, yace toh naji wani iri ne abun nan ta Fara fadin zaka ganshi fari kaman doya ana saidawa a kwano yace oh na ganeshi baby plz ban san ciye ciyen irin wannan abun kar yaja miki matsala, bata fuska tayi tare da fadin nima babu abunda zai min kawai ka siya min, kallonta yayi yanda take wani daurewa yace ok naji toh zan siyo sai a dafa miki a nan tace toh tare da sakin murmushi tashi yayi ya fita driver yaba kudi ya siyo mata bayan an kawo yasa aka dafa mata bayan ankai mata ta fara ci sosai kallonta yake tayi yanda take ci Tana jin dadi kaman wani nama amsan kwanon yyi tare da fadin ya isa haka tace plz ka bani wlh ban koshi ba, mum ce ta shigo Tana fadin lafiya yace Mum tun dazu take tacin abun nan kar ya mata wani abu, mum tayi murmushi tare da fadin kaga ka bata kayanta taci babu abunda zai mata badan yaso ba ya bata ta zabga yaji da garin kuli, yace mum kin gani koh dariya Mum tayi tace babu abunda zai mata kasan duk mai ciki akwai abunda take so bai dade ba ya wuce, Gida ya nufa Zainab ta tareshi tare da fadin wai ina aysha ne tunda nazo ban ganta ba, yace Tana gidan Mum bata jin dadi cikin kulawa tace waiyo maike damunta? Yace she is pregnant wani irin duhu ta gani tare dajin wani dum lokaci daya kuma ta Saki kuka tare da fadin shikenan na rasa ka har abada bazaka taba dawowa gareni ba har abada kallonta yayi tare da fadin Zainab Wannan wani irin magana ne haka? Tace Ciki fah kace Tana Dashi shikenan yanzu zanga canji a gidan nan tunda ni Allah bai ban ba kamota yayi tare da rungumeta yace kiyi hakuri Zainab haiyuwa na Allah ne kema karki fidda tsammani Allah bai manta dake ba insha Allah kema zaki sami ciki ki haiyu kaman kowa, nan yaita rarrashinta tare da fadin idan aysha ta haiyu zai bata rikon dan data haifa, jinshi kawai take amma zuciyarta babu komai sai takaici da bakin ciki tare dayin dana sani nashan maganin hana daukan ciki da takeyi dan a yanzu taji Tana sha'awan haiyuwa tunda akace Indo nada ciki, tashi tayi tare da nufa daki danta kwanta binta yayi yana kara bata hakuri akan zata samu itama insha Allah....... Watan indo daya cif ta dawo Gida ranan A Majeed ji yake kaman ya goyata dan murna Mum ta bata masu aiki har biyu wanda zasu dinga mata aiki, bayan ta shiga gefenta tayi wanka tare da zama dan ta shafa mai da sauri ta rufe dan taji warin mai din har kanta lokaci daya kuma tayi toilet tana kwarara amai a wannan halin ya shigo ya sameta hankali tashe yaita mata sannu idanta yayi ja dan wuya cikin tausayawa ya wanke mata fuska da baki sannan ya kamota suka fito waje bayan ya zaunar da ita ya koma toilet din dan ya gyara wajan, saida ya gama ya fito sannan ta kalleshi tace my one ka siyo min wani mai nawa yayi expire, yace ba akwai mai cikin akwatin dana miki ba tace oh na manta bude wardrobe yayi ya janyo mata akwatinan tare da budewa har ya bude namai ciki harda kalan wanda ta bude yasa ta amai shita dauka aiko Tana budewa ta jefar tare dayin toilet da gudu amai ta kuma sakewa shigo hankali tashe yace Baby muje hspt kai ta girgiza alaman a'a tace wannan ma yayi expire wari iri daya sukeyi dauka yayi ya duba expire date din yace da saura baiyi expire ba, bude mata Vaseline yayi na oil yace shafa wannan shiya fara shafa mata tace kaga wannan baya wari dariya yayi tare da fadin dama Mum tace yanzu abubuwanki ba irin namu bane sai kin zaba dariya tayi tare da ture mai hannu tace toh ba Baby dinka bane yasa na canza yace kar ayi ma baby dina shairi dariya ta Saki yanda taji yayi maganan wai nan ya kwaikwayeta ne, wayanshi ne yayi kara dauka yayi tare da karawa a kunne yace ok shigo bari ta sauko, kallonta yayi tare da fadin Zainab ce tazo gaidaki gabanta taji ya fadi amma haka ta daure tasa wata doguwar riga ta fito masu aikinta tace suje su jera mata kayanta cikin wardrobe na cikin akwati, a falo taga Zainab kallon2 sukama juna kafin indo tayi murmushi tare da fadin sannu da zuwa, amsawa tayi duk yanda taso ta boye kishinta saida ya fito domin taga indo ta kara kyau duk da sau daya ta ganta ran da sukayi rigima amma hakan bai hana ta gane ta kara kyau ba kishi kumallon mata bata wani dadeba ta tashi tare da fadin idan kina bukatan wani Abu saiki fadamin in Kawo miki dan nasan masu ciki akwai ciye2 indo dariya kawai tayi shiko gogan yaji dadi sosai Zainab na fita ta Fara kuka tare da alwashin saita zubar da cikin indo kota wani hali.

Taku Maryam obam😘

*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*

*NA*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*

*WWW.maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

235to240

*DEDICATED TO....*

*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*

Ranan Zainab taci kuka tare da tunanin hanyar da zata salwantar da cikin indo domin tunda ita bata haiyuba haka indo ma bata isa ta haiyu ba sai dai kowa ya rasa a hakan ma yata Kare balle ace aysha ta haiyu tsanar indo take taji tare dana Mum wacce take ganin duk ita ta shirya komai dake faruwa yanzu a hankali ta furta saina rabaki da dan naki inga ta tsiya haka taita kuka Tana sambatu
Chapter 52 · 0% Book details