Sashe 12
Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Indo tunda ta shiga dakin ta kuma tsorata domin gadon dakin kanshi abun kallo ne, ita dai tasan gado na karfe mai rumfa irin na inna Tani amma yau taga wani daban, ga dakin katoto, ga carfet a tsakiyan dakin, a kasan tiles din dakin ta zauna Tana kuka, jin sanyi yayi yawa yasa ta tashi ta hau kan kujeran dakin ta kudun dune, bacci ne ya dauketa, saida Gari yayi haske sannan ta farka ganin har rana ta fara yi batai sallah ba, yasa ta tashi da sauri ta fara dube2 kofar dakin ta bude tana lambo kaman wata munafuka har ta karasa falo, ta bude kofar waje, babu kowa sai motoci a fake masu kyan gaske, famfo ta hango da sauri ta nufi famfo din ta bude tayi alwala, ta koma ciki, tana shiga falo taganshi a zaune yana kallo, tunda take bata taba ganin tv ba a rayuwanta ihu ta saki tare da kokarin bude kofar ta fita, amma saboda tsoro ta kasa budewa, A Majeed tashi yayi ya nufi inda take tare da daka mata tsawa kee miye haka? Bata daina ihun ba sannan bata daina kokarin bude kofar ba, tsaki yayi tare da janta yai hanyar dakinta da ita,ganin haka ta kara rudewa tana ihu tare da fadin dan Allah karka yanka ni, dan Allah kayi hakuri ka maidani gidan mu, wayyo yaya yusuf za'a kashe ni yau, zai shanye min jini..... Cak A Majeed ya tsaya yana kallonta cike da takaici yanzu wannan abun Mum ta auro min da sunan mata kai gskya Mum ta gama dani, jin kaman ya tsaya yasa indo ta sadakar an Kawo wajan da za'a yanka ta, idonta a rufe duk take wannan ihun, ta Fara fadin shikenan yau zan mutu rayuwa na yazo karshe an Kawo ni gidan yankan kai, A Majeed shi yama rasa abunyi dan takaici sake mata hannu yayi yabar wajan dakinshi ya koma yana ta kaiwa da komowa kaman Mai yin Parade, toh a ina Mum ta samo wannan yar kauyen yarinyar ita da bata san mutane sosai a kasar nan ba, duk inda Mum ta samo ta wannan ba damuwa na bane, dole in sallameta ta koma gidansu bada dadewa ba, wayanshi ne ya fara kara dauka yayi yaga Mum ce, gaidata yayi bayan ta amsa tace ya aysha? Shuru yayi tare da tunanin wacece aysha, Mum ta katse shi da fadin Hello son ko baka ji nane, yace inaji mum, sai yanzu ya Tuna da yarinyar da Mum ta aura mishi, wato itace aysha din, yace Mum ni gaskiya Mum yanzu duk matan da suke kasar nan,educated sai a rasa wanda za'a bani sai wannan illiterate din, yar kauye, gskya Mum zan sallameta ta koma gidan su, Mum kashe wayan tayi ba tare data gama jinshi ba, kallon wayan yayi tare da jefa shi kan gadon dakin, shiryawa ya fara yi domin gskya bazai iya kara kwana da wannan yarinyar ba a gidan nan, yau zai koma Abuja.
Indo jin shuru bata ga an yanka ta ba, yasa ta dan bude ido, taga ba kowa dan haka ta shige daki da gudu tana ajiyan zuciya tare da godema Allah da ba'a yanka taba, tunanin su inna jamila ya fado mata yanzu hala ma suna can an yanka su, Allah sarki inna jamila ta kuma fashewa da kuka, turo kofar da akayi ne yasa ta tashi da sauri tana yin baya, Mum ce ta shigo dakin duk da bata santa ba taga kaman su daya da A Majeed, cikin Fara'a Mum tace aysha mai ya faru kike kuka ji fuskan ki ya kumbura koh dukanki yayi? Indo jin maganan matan yasa hankalinta ya dan fara kwanciya domin ta tabbata ita bata yanka mutane amma shi namijin nayi, dan haka ta matsa kusa da Mum tana fadin dan Allah ki fitar dani in tafi gida karya yanka ni, Mum tayi dan murmushi tare da fadin babu mai yanka ki, ki kwantar da hankalinki kinji? Indo dai shuru tayi bawai dan ta yarda ba, Mum tace muje kici abinci, tare da rike mata hannu suka fita falo, TV din dai yana nan a kunne, nan indo ta kuma sakin ihu,mum ta riketa tare da fadin aysha lafiya kuwa?nuna ma mum TV din tayi da hannunta abun yaba Mum dariya tace haba aysha TV ne fah, bude idonki ki gani, a hankali ta bude idon tare da manne wa a jikin Mum tana gani, a BBC yake taga baturiya tana magana ta kalli Mum da take mata murmushi ta kuma kallon matan TV din taga basa kama kawai fari ne Iri daya sai dai na Mum yafi kyau kuma tafi matar TV din kyau, mum tace muje kici abinci kinji..... Dai2 lokacin A Majeed ya fito da akwati yana ja, Ganin Mum yasa ya tsaya yana mamakin yaushe tazo, Mum ido ta zuba mishi tana kallon shi.......
Taku Maryam obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
75to80
*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*MY TA GABAN GOSHIS UMMY ON TOP❣❣*
Ganin irin kallon da mum take mishi yasa ya ajiye akwatin tare da sosa kai yana fadin morning Mum Ashe kinzo? Tace inda ban zo ba tafiya za kayi kenan koh? Ta kafeshi da ido tana sauraranshi, indo tun ganin fitowanshi ta Kara makale Mum tare da rufe ido, ganin bashi da niyan magana yasa Mum taci gaba da fadin wai abdul-majeed yaushe ka koyi rashin jin magana ne? Yanzu duk abunda na fada maka kenan a banza koh? Toh bari kaji wlh idan kana son ganin bacin raina ka tsallake abunda na fada maka, jan hannun indo tayi Suka nufi dinning, ta zaunar da ita tare da zuba mata abinci, ganin yanda indo ta takure yasa mum ta kalleta tare da kiran sunanta aysha ki saurare ni da kyau, babu abunda zai faru dake ki saki jikinki nima mamanki ce kinji, sannan ki daina jin tsoro wancan mijinki ne, kinji kai ta daga alaman eh, sannan Mum tace ta fara cin abincin chips nd egg ne da Tea sai farfesun naman kaza, indo ci take sosai ganin tana ci yasa Mum tabar wajan ta koma kan kujeran falon A majeed dake tsaye yana kallonsu wani irin takaici yake ji, wai waccan yarinyar ce matarshi wanda inda ya haiyu da yanzu yana da Sa'anta, ganin Mum ta zauna yasa ya matsa kusa da ita yace Mum..... Daga mai hannu tayi alaman ya kyaleta, yace plz Mum listen to ur son yana maganan ne kaman zaiyi kuka, bata kuma ce mishi komai ba ganin haka ya fara magana Mum plz ki fahimce ni, bawai bana son auren bane, yarinyar ce bana so duk maganan nan yana yine cikin turanci, yace mum she's young mai zata min and batayi karatu ba, kwata2 bata da wayewan da nake bukata a wajan mace, Mum ido ta kafa mishi yanda yake bayani har yakai aya, tayi ajiyan zuciya tare da fadin ka gama? Shuru yayi bai ce komai ba, shurun nashi bai dameta ba, ta fara magana idan kai ka manta ni ban manta ba, dan haka bari in Tuna maka, na baka zabi akan ka kawo Mata, kace in zaba maka, ko ka manta da anyi haka? Yace mum yes but amma ba irin wannan nake So ba..... Mum cikin tsawa tace mishi ya isa haka A Majeed inma irinta kake so ko ba irinta ba wannan ya rage naka, bai kuma cewa komai ba sai daure fuska da yayi yana hararan indo yanda yaga tana cin abinci, Mum ta tashi tace indo ta biyota, daki, Indo binta tayi cikin dakin data kwana bayan Sun shiga, Mum ta zauna akan kujeran dakin tare da cema indo ta zauna itama akan kujeran, indo zama tayi a kasa, Mum tayi dan murmushi tare da fadin a kai nace ki zauna, tashi indo tayi ta zauna a kai, Mum ta dan kafe indo da ido, ta aiyana a ranta yarinyar fara ce kyakyawa sai dai farin ya boye saboda wahala, Mum tace aysha bari kiji ki saki jikinki sosai nan gidan mijinki ne, nan Mum ta fada mata yanda akayi har danta ya aureta, lallai abdul ya taimaketa a rayuwa domin shine ya rabata da auren dan jummai, wani irin waje mai mahimmanci ta ajiye abdul cikin zuciyarta, Mum ce ta katseta da fadin yanzu abunda nake so dake duk wani abu da yake damunki ki fadamin kinji kar ki boyemin komai sannan akwai kaya a wardrobe sai dai basu da yawa,anjima za'a kawo miki akwatin ki,sannan za'a hado da tela ya gwada ki, sannan zansa a kawo miki mai tayaki zama, duk wani abu da baki ganeba zata nuna miki, kai indo ta daga domin yanzu ta yarda da Mum tasan ita da A Majeed ba yan yankan kai bane, nan Mum taita kwantar ma indo da hankali sannan tayi mata sallama akan za'a kawo abincin rana bada dadewa ba, koda Mum ta fita a falo taga dan nata fuska a daure bata kulashi ba tazo zata wuce ganin haka yasa yace Mum zan koma gobe akwai Office Monday mum tace zanyi tunani akai sanna ban yarda ka tafi ba har sai kaji daka gareni, tana gama fadin haka ta fita ba tare da ta jira amsan dan nata ba, A Majeed ji yayi kaman yasa kuka dan takaici yanzu Mum ta bashi wannan yar kauyen sannan dan ya nuna damuwa akai shine take fushi dashi, wannan wani irin abune yake faruwa dashi wanda ko a mafarki bai taba tunanin za'a mishi auren dole ba, yes auren dole mana tunda shi baso yake ba, dan tsaki ya ja tare da fadin gskya zai je ya sami Dad dinshi akan yayi ma Mum magana da Wannan tunanin ya danji sanyi a ranshi.