← Book details Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 53

Sashe 9

Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Surayya tace,toh miye ?
Ba zobe bane kawai...
Ko fa a yau dinnan kace a yi maka wani sabo a cikin daren nan za'a kawo maka shi,toh miye na wani tashin hankalinka,ta karashe mgnr tana kallonsa (giving him i dnt care look)...

Yarima ya banka mata harara kafin cikin sauri yabi inda zoben ya tafi...surayya se kwala masa kira takeyi yayi banza da ita..

'Tafiya kawai yakeyi ga ruwa ya fara yawa a lkcn...
  Bai taba zaton kogin yana tsawo haka ba...

   Wata murya ce yaji ana ta rera waka cike da nishadi..
Ya dago kansa cike da mamaki...

  caraf sai Hango ta yayi tana ta tsalle tsallen ta tana rera wakarta hankalinta akwance....
Har zai dauke kansa'kawai idonsa ya sauka akan fuskar ta...

   Wani irin ware ido yayi yana mamakin ganinta a wajen...
Wai wacece wannan yarinyar?
Gabansa nata faduwa kallonta kawai yakeyi ya kasa dauke idonsa..

Ita kuwa juwairiya bata ma lura dashi ba a wajen,tana gama tsalle tsallen ta ta kwashe wankinta dan dama batayi shanya ba ganin hadari,ta dauki kwal'lar ta tayi gaba...

      Yarima yaja lumfashi, ina ne can din data shiga?me yasa wai ya damu da sanin wacece ita?me yasa bazai mance fuskarta ba?meke damunsa haka?

      Ganin tunani na neman yi masa yawa ne ya dauke kansa da sauri yaci gaba da neman roben sa,da kyal ya ganshi wani dutse ya tare shi ya dauka yayi gaba yana waiwayen hanyar da ta bi...

*********
"Bayan kwana biyu yarima ne yayi kiran magaji zuwa sashen sa_(magaji yaron waziri ne kuma babban aminin jalal ne)_

  Magaji daya gaji da jiran yarima yayi masa mgn'yayi gyaran murya yace..
Yadai ranka shi ya dade?ka kirani kuma naji kayi shiru..da fatan dai lafiya ko?

  Yarima yaja lumfashi kafin gyara zaman sa yace,magaji ko kasan iya inda ruwan kogin mai martaba yake kaiwa?

Magaji yadan yi tunani sannan yace idan bazan manta ba naji ance ruwan har fa RUMFAR BAYI  yake kai wa..da wani abun ne?

Yarima yadan girgiza kai "rumfar bayi fa kace?
Magaji yace kwarai kuwa..
Yarima yadan yi shiru,amma shi fuskar da yake gani batayi kama da wata baiwa ba sannan ma ranar ai da kayan alfarma sosai ya ganta..
      Magaji ne ya katse masa tunanin sa..
Wai yarima meke damun ka ne? Ka sanar dani mana ko zan iya taimaka maka..

Yarima ya kalleshi,babu komai magaji tashi ka tafi..
Magaji ya jinjina kai sannan ya mike ya fice..

Yarima ya mike shima,bawansa ya kira ya fada masa yaje ya sanarwa surayya a dakinta zai kwana yau...

Bawan na fita kuyangi suka shigo dan hada mishi ruwan wanka..
Suna hadawa yace dasu zasu iya tafiya..
  Kayan jikinsa ya rage sannan ya shige cikin bahon wankan yana lumshe idanuwansa..

***************
  "Surayya na cikin cin abinci ne bawan yazo ya isar da sakon yarima..

Zo kuga Murna a wajen surayya tu're abincin dake gaban ta tayi dan a take taji ta koshi,bayinta ta kalla sannan tace dasu su shiga su sake gyara mata dakinta...

   "Ba karamin gyara suka sha ba,surayya jiki na rawa ta shiga ban daki da wasu bayin aka wanke ta tas sannan ta fito ta turare jikin ta ta saka rigarta mai santsi ta barci sannan ta zauna jiran yarima..

Shiru shiru babu yarima ,surayya taja tsaki,wannan kuma wane irin salon wulakancin ne?
Har sha dayan dare babu shi.. surayya na nan zaman jiran sa sai gyangyadi takeyi..can taji ana sanar da zuwansa..

  Ta mike da sauri ta zauna tana daure fuskarta..
   Yarima na shigowa dakin kamshi ya daki hancinsa..
Ya lumshe ido hade da saukesu akan surayya data harde hannayenta ta juya masa keya..

    Tabe baki yayi kafin yace..
Badai ni ake jira ba har aka kai wannan lkcn ba'a kwanta ba?
Ta juyo tana kallonsa shima ita din yake kallo..

   Cike da masifa tace,wai me yasa kake jin dadin wulakanta ni ne uhm?
Yarima ya cire alkyabbar jikinsa..yace,
Menene wulakanci a ciki?
"Sanar dake na yi zuwana?ko kuwa zuwan nawa sashen ki bayan shudewar kwanaki biyar..

"Surayya ta turo baki,sannan tazo ta haye saman gado tana tunanin yarda zata aiwatar da shawarar yakambo data aiko mata da wasika jiya..

    Gadon shima ya hau sannan a natse ya jawo bargo ya rufe jikinsa..
  Surayya ta runtse ido sannan ta shige cikin bargon itama ta matsa daf dashi ta sa hannu ta rungume sa ta baya..

  Yarima najinta a jikinsa yaji wani abu ya tsarga masa a gaba daya jikinsa...
Surayya ta na fitar da lumfashi ta kai bakinta saitin wuyan sa ta sumbata,cak yarima yaji wutar sa ta dauke,a take ya juyo suna kallon junansu dan akwai dan hasken fitila a dakin..

   Me kikeyi hakan....ya fada da muryarsa da ta canza amo (sauti)
Surayya ta kura masa ido batace kome ba..

Yace ko bakya jina ne eyeh?..
Ta sake motsawa kusa dashi,wai yarima ni ba matarka bace ba?meyasa ne kake min haka...ta karashe mgnr a shagwabe..
Yarima ya kamo hannunta...me nake miki?
Surayya ta zunburo baki,kaima ka sani ai wulakan.....bai bari ta karasa ba ya hade bakinsa da nata yana sumbatarta cikin salon sa..
   A wannan daren ne yarima da surayya suka san minene aure...

***********

"Juwairiya ta kalli khadija da zainaba dake ta muhawara akan zuwansu sashen matar yarima..

    Zainaba ta rike kugu tace,kedai kawai khadija ki ce kishi ne ke damun ki kuma duk tsiyar ki se naje ganin matar yayana ehe..

Khadija ta banka mata harara, ai dama nasan duk abotar karya kike dani..
Zainaba tayi dariya tana rungume ta,haba kawalli kema miye naki dan Allah ba gwara kije ma ki ga yarda take ba ma dan kisan inda kika dosa..

Khadija tace kuma fa haka ne,duk da dai naji ana ta wani fifita kyawun ta..
Zainaba tace yanzu dai muje mu ganewa idonmu ko?...

  Shiryawa sukayi juwairiya dai jinsu kawai takeyi....
   Suna kai wa sashen juwairiya taja ta tsaya a waje,zainaba ta juya tana kallonta muje mana?

Juwairiya ta girgiza kai ku shiga kawai ranki ya dade zan jiraki anan..
Khadija ta harare ta ai gwara ki tsaya a nan din kam tun kafin ganin ki ya jawo mana wani rainin..

Ko tanka ta juwairiya batayi ba ta samu wani dan dutse ta zauna a kai...
*********
Bayan anyi musu iso ciki ne suka shiga suka zauna a falonta suna jiran fitowarta..
Khadija tabi kwalliyar falon da kallo tana yatsina fuska lallai kam an kashe kudi a nan ...

'A wajen Surayya kuwa kwana biyun nan cikin wani irin farin ciki take,ganin yarda yarima yake dan kula ta ba karamin dadi hakan ke saka taba..

   Cikin tafiyarta ta yanga ta shigo falon..
Sannunku kawai tace musu ta zauna..
Zainaba tace,nayi fushi dake matar yaya..
Surayya ta danyi murmushi dan ta fahimci kanwar yarima ce zainaba diyar fulani diyya..

   Haba kanwar mu ni ce ai ya kamata nayi fushin,tunda nazo baki ko leko ni ba..
Zainaba tayi murmushi hakane kuma gsky,kinsan halin mijin naki ne sai muna bi a hankali..

Surayya tayi dariya jin ance mijinta..
Khadija kuwa se kare wa surayya kallo takeyi..
Can dai tace,matar yaya nidai nasan baki sanni ba,sunana khadija kawar zainaba ce sannan diyar waziri..
Surayya tace,kanwar magaji kenan ko?
Khadija tadan murmusa kawai..
Surayya ta kalli baiwarta,ya baki kawo musu abun tabawa bane?
Baiwar tayi kasa kai sannan ta mike ta fita..

************
"A can wa'je kuwa juwairiya na nan a zaune tana wasa da kananun duwatsu kanta a sunkuye,tana rera yar wakarta dan debe mata kewa..

      Magaji ya kalli yarima 'lkcn suna tafiya ne dan zuwa sashen surayya'
   Lallai ango ka ganka kuwa?wannan hasken da kake ta yi lallai gimbiya surayya ta iya ki'yo..

Yarima ya tabe baki,ta iya ki'yo fa kace?wa'to ni din wani dabba ne ma kenan da har ake ki'yona ko?

Magaji ya kwashe da dariya..maida wukar abokina..
Yarima yace,ba wannan ba,ya kake gani zamu bul'lowa mgnr da mai martaba ya fada mana dazu?
Magaji ya lumfasa gsky al'amarin kamar da girma kaga fa se munje har can chadin mun hadu da wannan mutumin..

Yarima ya jinjina kai yana shirin mgn ne kawai yaji wannan muryar da ko a mafarki yaji ta sai gabansa ya fadi...(muryar juwairiya dake dawainiya da zuciyar yarima)

    'Da sauri yabi inda sautin muryar ke fitowa da kallo..
Hango ta yayi can gefe a zaune tana wasa da duwatsu kanta a sunkuye..
   Cikin saurinsa ya karasa gabanta...

   Bai tsaya wani tunani ba yasa hannu a ha'bar ta(chin) ya dago da fuskarta....idanuwansa kamar zasu zazzago kasa..

*********
Juwairiya a tsorace take kallonsa dan kuwa ji kawai tayi an dago da fuskarta..
   Yarima na ganin fuskarta ya ture ta gefe da karfi cikin zafin rai..

"Ba ita bace"
Ya fada a zuciyarsa, ya runtse ido cike da takaicin ganin fuskar juwairiya dake saka tsikar jikinsa tashi..
ya juya bai ce komai ba yayi gaba..fuuuu
  Juwairiya tabi bayansa da kallo cikin mamaki tace,miye kuma hakan?

********
  "Ko gama sanar da isowarsa bai bari anyi ba ya shige ciki abunsa,magaji dake biye dashi yana tambayar sa miye hadin sa waccan baiwar ya tsaya yana bin bayan sa da kallon mamaki ...

   cike da tunanin abunda yarima yayi yanzun nan magaji yace,a ina kuwa nasan waccan fuskar?
Girgiza kai yayi,kai ba ita bace gsky,dan waccan fuskarta ba haka take ba..
Yana cikin wannan tunanin shima ya shige ciki..

***********
Surayya na ganin yarima ya shigo ta mike tsaye itama cikin zumudi dan baya zuwa sashen ta da rana haka..

  Ko kallon inda suke bayyi ba ya shige cikin daki abunsa..
   Zainaba ta tabe baki ko ma ya tsaya su dan gaishe shi..

Magaji ne ya shigo yana fadin , ah ah ashe yan matan suna nan suma..
Surayya tayi murmushi,ai kuwa dai sunzo ganin yayarsu ba..

Magaji yace ai sun kyauta,nima bari na karasa wajen umma babba,ya fice..
   Surayya duk ta kagu su khadija su tashi su tafi dan ta shiga wajen mijin nata,tayi tsaye ita taba bi yarima dakin ba ita kuma  bata zauna ba..

  Zainaba ce ta fahimci kamar su take jira su wa're..,dan haka ta zunguri khadija dake ta tabe baki,tashi muje khadija nasan fulani na can na jiran mu tunda fada mata zamuje sashen ta ko?
Chapter 9 · 0% Book details