← Book details Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 53

Sashe 32

Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

TURAKI ya daure fuska sosai...
Ni banga wata hujjarki na hukunta ta ba dan kawai tabi umarnina...
Dan haka inaso kiyi gaggawar dauke hukuncin ki a kanta...
  Surayya cike da bakin ciki take kallon shi..
Toh miye alakar ka da ita?
Me kake yi da ita acikin dare kuma a lungu?

  TURAKI ya fusgar da iskan bakinsa..
Cikin kakkausar murya yace....
SONTA NAKEYI...
Gaba daya wajen aka kura masa ido ciki tsananin mamakin furucinsa..
Surayya ta runtse wata zuciyar na mata dadi wata kuwa bakin ciki takeyi,taso sosai juwairiya ta fadi sunan jalal dan ya tsane ta har abada..
Amma wannan turakin yazo ya bata mata shiri mtsw...

Turaki ko a jikinsa ya karasa gaban juwairiya da har ta suma sbd tsananin azabar data sha..
   Yana kokarin daura hannunsa a jikinta..sukaji shamaki na sanar da shigowar SARKI JALAL (wanda yaji furucin Turaki har cikin kwarewarsa )...............

Not edited

TEAM RUMFAR BAYI

 *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 30
Wattpad @afreey101

*****************

"A mutukar fusace sosai Jalaal ya shigo wajen cikin tsananin bakin ciki da konar rai.. zainaba na biye dashi a bayansa..

Ai gaba daya jikin surayya ya shiga rawa..
Batayi tsanmanin lbrn nan zai je ga kunnen sarki ba dan kuwa ba karamin laifi bane ace matar sarki ta yanke hukunci a kan bayinsa ba tare da izinin sa ko masaniyar sa ba akai ...

       Jalal bai yi wani tunani ba ya wanke ta da mari mai rai da lafiya...
  Surayya ta dafe kuncin ta tana kallonsa cike da tsananin mamaki da takaici..

Jalal fuskar nan a daure ya kalli sarkin dorina da shima jikinsa ya fara rawan...yace,
Wato harda kai za'a hada kai a aikata irin wannan (abomination)din a karkashin mulkina!!!!!?

Sarkin dorina yayi saurin zubewa a kasa yana neman gafara awajen sarki hakama sauran bayin dake wajen..
Jalal ya kallo gefen da juwairiya take a kwance bata lumfashi runtse ido yayi cike da kunci sosai...duk shine ya jawo mata shiga cikin wannan halin..dolene yayi abunda ya dace..

Har ya yunkura dan zuwa gareta wata zuciyar ta shiga gargaden shi...
"(Idan har kayi kuskuren aikata haka a gaban jama'a a yanzun,toh ba karamin bakin jini zaka jawo mata ba,a hakan ma surayya tayi mata wannan danyen hukuncin...
toh balle idan ka bayyana sonta a bainar jama'a,ai ko mahaifiyar ka gimbiya kilishi ta isa ta cutar da ita)"

   "Surayya ta kalleshi rai a bace..
Sannan ta juya da gudu ta bar wajen cikin bakin ciki da takaici ...umayma tabi bayanta..

Jalal ya kalli zainaba yace,ku dauke ta daga nan a kira me magani a duba ta..yana gama fadar haka ya fice da saurinsa dan bazai iya jure ganinta a cikin wannan halin ba..

"Hansai,laure,jakadiya da lbr yaje musu acan rumfar bayi ba kamarin tashin  hankali suka shiga ba,gaba dayansu damuwa da tausayin halin da juwairiya ta shiga sukeyi..

hansai na kuka sosai tace,dama ashe juwairiya ce ake fada? naji lbrn nan tun dazun a sashen gimbiya kilishi amma zuciyata bata kawo min juwairiya bace ko kadan?

'Dubu tace wlh nima naji lbrn nan yana yana ta yawo a tsakanin bayi acikin rumfar bayi amma ban taba tsanmanin juwairiyar mu bace tunanina tana can wajen aikinta..

Laure tace,ni abunda ban gane ba anan shine..
Me juwairiya tayi wa surayya haka ne?
Jakadiya ta jinjinar dakai sannan tace mu karasa can rumfar hukunta bayin na tabbata zainaba zata ceto mana juwairiyar mu..

Suna karasawa suka hango rabi da zabba'u dauke da juwairiya ga kuma zainaba da turaki a bayansu..
   Da sauri sukaje suka kama musu ita suna kuka sosai suka nufa rumfar bayi da ita....

*****
"Jalal na shiga sashen sa ya kasa zaune ya kasa tsaye,zuciyarsa yake ji tamkar zata fashe..

      Babu abunda ya ke dawo masa a kwakwal'warsa sai furucin Turaki na dazun..INA SONTA?
Yaushe turaki ya fara son juwairiya? Yaushe hakan ya faru?itama tana sonshi

Yanzu menene mafita a wajensa, yana nan a zaune kaninsa zai dauke masa macen da yakejin sonta kamar ransa?
Inaa bazai bari hakan ya faru ba,dan a yarda yake jinta acikin zuciyarsa,bazai taba iya hakura da ita ba...

Tunaninsa ne ya katse jin mgnr jakadiya a kusa da shi..
  A sanyaye take kallonsa tana tausayawa halin da yake ciki sosai..

"Dan kawai yana a matsayin sarki shine bazai iya samun damar fitowa ya nunawa masoyiyar sa irin son da yakeyi mata ba..
Sbd wani mulki... oh wasu kuma har kwadayin mulkin nan suke....taja lumfashi kafin tace..
      Ranka shi dade ka kwantar da hankalinka..
juwairiya na samun kulawa sosai a wannan lkcn..

Jalal ya juyo ya kalleta da idanuwansa da suka canza launi..
Jakadiya tace..
Dama wani bawa ne yazo daga sashen tsohon sarki Abdul-Jabbar,ana neman ka acan..
Jalal jiki a sanyaye ya sake shiryawa ya fita,yana tunanin me yasa mahaifinsa yake faman sa..

************
"Yana shiga makeken falon ya tarar da family duka a zaune..
Ga kuma surayya acan gefe tana ta kukan bakin ciki,har ita yarima zai daga hannu ya mara a gaban wasu kanskantun bayi?
Toh wlh baza ta sa'bo ba....tafi karfin a wulakanta ta haka!...

'Abban ne ya kallesa ya shigo yayi musu tsaye yana mamakin taron me akeyi haka?..

Ka Samu waje ka zauna AMALE...
yarima ya zauna a kilisar dake gefe fuskantar tasu hamza da turaki..
   Abban yayi gyaran murya yace..

Amale ko zaka iya fada min dalilin da yasa ka marin matarka?
Gimbiya kilishi tayi katsalandar fadin..
Dan ya isa da ita mana..
Abban ya daga mata hannu,ba dake nake mgn ba kilishi..kai kuma ina jiran amsar ka..

Jalal ya dauke kai gefe..sannan ya sanar ma abban duk abunda ya faru..
  Abban ya kalli surayya..yace,
Wai anyi haka?
Surayya ta goge hawayen ta,anyi haka abba,amma ni kawai nayi hakan ne dan na san meke tsakanin turaki da wannan baiwar...bawai nayi niyyar na yanke hukunci da kaina bane..

Abba ya kalli turaki..
Meke tsakaninka da wata baiwa?ko ba jiya bane aka daura maka aure ba?

Ko so kake ka nuna mana bamu isa dakai ba..

Fulani ta shiga hararar Turaki..cike da takaici..
Turaki ya lumfasa, ba haka bane abba..
Ni sonta kawai nakeyi abba kuma inaso ku bani dama dan na YAN'TAR DA ITA...

   Jalal yayi saurin kallon sa..
Zuciyarsa na mutukar harbawa..
Surayya tayi wani irin shu'umin murmushi dan tana lura da irin yanayin jalal ya shiga.

    Samira kanta tayi mamakin furucin sa,wai mijinta ne ke son wata baiwa har haka?
oh ashe shiyasa yake yawan zaman tunani?
ko a jikinta ita kam dan tausayi ma ya ke bata sosai yarda aka saka shi a gaba ana masa tambayoyi..

   Abbah yace,kasan me kake fada kuwa?
Turaki ya zube kasa...
Dan Allah abbah ku taimaka min..na dade ina fama da sonta..
tun tana yar karamar ta Allah ya daura min sonta..
Wata irin tsawa fulani ta daka masa..
"TURAKI!

Yayi shiru yana zubar da kwalla..
Jalal mutuwar zaune kawai yayi..
Dama haka turaki ke son juwairiya?

   Fulani ce ta mike tazo ta wanke sa da mari..
Baka da hankali ne?
Me na fada maka uhm!
Gimbiya kilishi ta hau murmushi,ai dama dolene mu ringa fuskantar irin haka...tarbiyyar gidan sarauta bata ishe ka ba turaki..ka yan'ta baiwa ka aure ka a matsayin me...?
   Turaki yace,MATATa mana..

Abbah yace duk ku tashi ku fita idan na yanke shawara zuwa anjima zan neme ku..
Gaba daya suka mike suka fita cike da al'ajabi...

     Da daddare abban ya sakeyin kiran su..
  Ya kalli jalal..
Inaso ka bada izinin ka,turaki ya yanta wannan baiwar a gobe...
     Ga baki daya sai da gabansu ya fadi..sunyi mutukar mamakin yarjewar mai martaba Abdul-Jabbar..

Mamaki sosai ne ya rufe su..
Zainaba kuwa murna kawai takeyi,ji take kamar ta tashi tayi rawa dan farin ciki..

  Jalal ya rasa meke masa dadi..
Yana nan zaune juwairiya na neman subuce masa..
Kamar me koyan magana a haka ya bada izininsa,ko ba komai ya samu yin abunda ya dade yanaso yayi mata,wato ya yanta ta daga bauta..
    Surayya bakin ciki sosai ya rufe ta..
Koda ta koma sashenta...
Umayma ce tare da tulin tambayoyin ta.
Surayya taja tsaki kafin kawai tace,ki shirya zamu fita yanzu....

************

"Juwairiya ba karamin jiki ta sha ba dan har se da tayi awa daya bata farfado ba..
Kuka sosai takeyi tana jin azaba da radadi a gaba daya jikinta..

Hansai kanta kukan takeyi tana lallashin ta data sha magani..
Rabi da zabba'u na gefe duk sun buga uban tagumi suna tauyawa kawar tasu..
juwairiya har cikin zuciyarta batayi nadamar rashin fadin sunan jalal da batayi ba..

Oh ! ko yana ina yanzu?a wane hali yake ciki?ta tabbata hankalinsa a tashe yake...

Jakadiya ce ta shigo da wata me magani a bayanta da yarima ya sakata taje ta dauko ta..
Me maganin ta hau duba juwairiya..cike tausayawa.

**********
"Samira ta kurawa turaki ido ganin yarda yake ta faman sauke ajiyar zuciya..

ba karamin fada yasha a wajen fulani ba wai yana son ya zubar mata da mutumci ya juyawa yan uwansa baya akan mace.
ita ba wai yantar da juwairiyar da yayi bane damuwarta,ah ah furta Auren ta da yayi shine bacin ranta,duka duka jiya aka daura masa aure ko yan uwan matarsa basu gama watsewa ba yake so ya ballo musu ruwa...

   Samira ta tausaya mishi sosai dama haka So yake?
  Ta dawo gabansa ta tsugunna tace..
Turaki inaso na baka wata shawara idan bazaka damu ba..
Turaki ya dago yana binta da kallo..
Tace na tambaye ka?
Yayi shiru..
Samira taci gaba..
Ita baiwar da kake so din ka tabbata tana sonka ne?
Ko kuwa dai nuna mata iko da mulki zakayi ka aureta a cikin rashin damuwa da(feelings)dinta..

   Turaki ya kura mata ido yana wani nazari,tabbas yasan juwairiya bata son sa,dan da tana son sa da zai gane tuni..,yasan dai ta dauke sa a matsayin yayanta ne amma baya tsanmanin tana SON SA...

    Samira ta jinjina kai,yanayin ka ya tabbatar min da cewa ba sonka takeyi ba...
Ta riko hannunsa..
Idan zan fada maka cewa kaima ba sonta kakeyi ba zaka yarda da ni?
Chapter 32 · 0% Book details