← Book details Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 53

Sashe 21

Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tunaninta ko barci yakeyi,dan haka tadan ja tsaki,ba haka taso ba ko kadan...amma ya ta iya..

  Kayan jikinta ta dan rage sannan ta haye kan gadon tana matsawa kusa da shi..
  Duk abunda takeyi yarima yana jinta amma yayi mata shiru..

   Rungume sa tayi tana daura kanta a kan kirjinsa me fadi..
Taja lumfashi kafin nan ta runtse idanunta..
"Yarima gaba daya yaji kamar ya ture ta daga jikinsa..

Ga tunani duk ya gama cika zuciyarsa, dazu da zainaba tayi wa juwairiya wannan tambayar yaso yaji amsar ta kwarai da gaske..amma bai san irin halin da zai shiga ba idan har ta fadi abunda zuciyarsa bazata so taji ba..

_zakuji update anjima inshaAllah_

Team RUMFAR BAYI

[9/18, 3:22 PM] Aysha Galadima:           *RUMFAR BAYI*
       (A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 22
Wattpad @afreey101

_gaskiya ina godiya sosai,my wattpad fans are rlly d best,hakama fans din rumfar bayi na whatsapp duk ina jin comments dinku wlh Allah bar zumunci amin_

"Ahankali ya bude idanuwansa...

ya kalli fuskar surayya da barci me nauyi ya dauke ta,
sannan ya saka hannu ahankali ya janyeta daga jikinsa ya sauko da kafafun sa kasa ya zauna a gefen gadon yana dafe kansa da duka hannayensa...

   Muryar jakadiya ce yaji yana sallamar bayin dake waje....
    Haka nan ya samu kansa da mikewa ya zura kaya a jikinsa..sannan ya saka takalmansa ya fito daga dakin..

Jakadiya da tsananin mamaki take kalle sa dan a duk tunaninta ya dade da yin barci.
tace,da fatan dai lafiya ko ranka ya dade?
Jalal yadan murmusa mata sannan yace,
lafiya kalau jakadiya zan dan fita ne na dawo ba da dadewa ba.
Ya sake yin kasa da muryarsa yace.. fitar sirri ce wannan dan haka ki rufa min asiri kinji?dan yasan jakadiya na iya sanar wa kilishi..

Jakadiya tayi murmushi, toh amma bari na saka a kira maka shamaki se yayi maka rakiyar ko?
Jalal ya girgiza kai,ah ah ki barshi kawai ni kadai zan fita,bana son ma kowa ya san fitar kin gane?
jakadiya ta jinjina kai kafin ta karasa ta bude masa kofa ya fice..

************
"Tunda suka ba'ro sashen sarki suke ta buga sauri...
kasancewar dare ne babu wani isasshen haske a hanyar..
  Juwairiya da aka baro can baya ta daga murya tace..
Wai baza ku jirani bane..?
Wata baiwa dake cikinsu tace,kema ki daga kafa dan Allah kina tafiya kamar wata me tausayin kasar kinsan dai dare ne atooh..

  Juwairiya kamar zatayi kuka ta karawa tafiyar ta ta sauri,dan ita kam tana tsoron duhun nan sosai..

     Sun sha kwana kenan kawai taji an damko hannunta da karfi....
A mutukar tsorace ta kware baki zata saka ihu..sai ji tayi wani abu me shegen taushi ya rufe mata baki,sannan aka shiga janta da karfi...
    Fitsari ne kawai batayi ba sbd tsananin tsoron da fargabar data shuga...

   Can bayan wani kango aka sake ta duhu ne sosai a wajen dan haka tayi yunkurin guduwa tana laluben hanya...

Sai ji tayi kawai taci taro da mutum bum!
Lumfashi me tsayi taja dan ko ba'a fada mata ba tasan waye...
Kamshin sa kawai data ji yasa ta gane YARIMA NE....

Jalal ya sake kama hannunta suka dawo saitin da kawai dan haske a wajen..
  Yana sakin hannunta ta dago da sauri suka hada ido dashi..

  Jalal ya harde hannayensa yana kara matsawa gabanta..
  Tadan ja baya kadan..tana fadin..
Ka ka kayi hakuri ranka shi dade..
  Yarima yaja burki yana fadin,hakurin me zanyi?

Juwairiya ta girgirza masa kai..
Jalal yace,"nazo ne dan ki fada min amsar ki ta dazun?
  Ta dan ware ido,amsata wace kenan?ranka shi dade..?

Yarima ya gyada kai yana matse lebensa na kasa..
Dariya yaso ya bata,wato dan kawai yaji amsatar ta ne.. shine ya fito da a cikin daren nan?sannan kuma har ya baro matarsa a daki?ya biyo ta ita baiwa?.

  Ina jinki?ya fada yana gyara tsayuwarsa...
Juwairiya ta rasa me zata ce masa,bakinta ya shiga rawa....
Ni ni ai babu wani zabi a gare ni,duk inda kuka kaini ai dolene naje nayi aikina..

    Mgnr da tayi ne yasa jalal yaji wani iri har cikin zuciyarsa,wato ita baiwar su ce duk inda suka ajiyeta a nan zata zauna..

  Juwairiya jin yayi shiru...
sai ta dan sace kallon sa da gefen idonta..
   Wai me yasa yarima ya fiya kyau ne haka?taji zuciyarta na tambayar ta..
  Jitai yace..
"Ki shiga dakina gobe ki gyara min shi"(hakanan ya tsinci kansa da fadin hakan,dan zuciyarsa na mutukar kwadayin ganinta a kullum)

Kafin ta bashi amsa ya juya ya fara tafiya..
Da sauri tabi shi tasha gabansa tana fadin..
  Ranka shi dade ba nan bane wajen aikina..,bazan iya samun shiga na gyara maka dakin ba..kayi hakuri..

  Yarima ya daure fuska..
Umarni ne nake baki a matsayina na sarkin ki.. dan haka bana son wani dogon zance..
Juwairiya ta samu kanta da langwabe masa kai gefe,sannan tayi kasa da kanta tace toh ranka shi dade..
   Jalal yayi murmushi kafin yace "wuce muje..

Ta kalleshi da mamaki,ina zamuje?
  Yace ina zaki je da?
Tace rumfar bayi zan koma ai..
Yace toh muje...
Tace,A tare zamu?ta waro ido..
Ka bari kawai zan tafi da kaina..
Jalal bai tanka ma ta ba ya shige gaba ya fara tafiya..
   Juwairiya da sauri tabi bayansa dan kuwa tasan bazata iya komawa ita kadai din ba a wanannan dare ga kuma duhu..

"Yana gaba tana biye da shi a baya..

Gani nayi juwairiya sai faman sakin murmushi takeyi tana kallon  yarda yarima ke tafiyarsa cikin kasaita da yanga kamar ba namiji ba..duk takun da zayyi cikin nutsuwa yakeyin sa..

  Ta shafa gefen fuskarta cike da nishadi..
ooh Allah me nasa ikon..wai yau kamar ta baiwa diyar bayi. SARKI da kansa yakeyi wa rakiya a cikin dare..
    Dadi ne fal a cikin zuciyarta, sai shakar kamshin da yake bazawa a hanyar takeyi.

"Shima din jalal murmushi yakeyi yana mamakin kansa,wani irin nishadi ke dawainiya dashi,ya rasa dalilin da zuciyarsa ke mutukar son kadaicewa wannan yarinyar..

Tafiya yakeyi kamar baya so..
Dan dama ba wani son suyi saurin yakeyi ba.
baya kaunar su iso rumfar bayi da wuri..

    Tsayawa yayi ya juyo dan ganin ko yayi mata nisa...(cike da kulawa kamar yarda ko wane gentleman zayyi." kun de gane😉)

"Juwairiya kam tayi nisa sosai a cikin nata duniyar..
dan ko kadan bata ma lura da tsayawar da yayi ba...sai ji tayi taci karo da wani mutum..bum!

  A tsorace ta dawo hankalinta..
sannan taja baya da karfinta..zanin jikinta ne ya ta'diye ta..ta tafi zata fadi..

   Yarima yayi saurin saka hannayensa ya taro ta..
Sauke lumfashi kawai takeyi dan ya shammace ta...

"Kurawa juna ido sukayi na wani lkcn me tsawo.. kafin ya gyara mata tsayuwarta yace..
   Tunanin me kikeyi haka?
Juwairiya ta samu kanta da fadin..

"Tunanin ka"!

Waro ido tayi da sauri jin abunda bakinta ya furta..ta zube kasa a mutukar kunyace..
   Jalal kuwa samun kansa yayi da jin dadin furucin ta"tunanin ka"ya lumshe ido...

    Juwairiya ta shiga bugun bakinta..
Kafin tace,kayi hkr ranka shi dade subutar baki ne nayi tunanin kaina nakeyi..me yasa ma zanyi tunanin mai martaba ai ban kai wannan matsayin ba..

  Yarima ya bude ido yana kunshe dariyar sa..dan ya fahimci kunya taji..

Mike!
Ya fada a daken sa..
Ta mike tsaye ta kasa ko kallonsa..
Muje....
Ya fada yana ci gaba da tafiya..
Har suka kawo kusa da rumfar bayi juwairiya bata daina jin haushin kanta ba..
  Ya tsaya yana juyowa gabanta..
Ki shiga..
Ta gyada kai..
Har ta fara tafiya ta sake dawowa da saurinta..

  Nagode kwarai da gaske ranka shi dade..
Ya jinjina kai kawai bai ce komai ba.
sannan ya juya ya fice...

  Juwairiya ta dafe kirjinta sannan ta juya dan shigewa cikin rumfar bayi sai murmushi takeyi..

  caraf sai hango umayma tayi a tsaye bakin kofar tana kare mata kallo..
   Gabanta ne ya fadi..
Kada dai umayma taga mai martaba yanzun nan?

Umayma ta kura mata ido cike da tuhuma.
fitowar ta kenan jin su hansai na jajen rashin dawowar juwairiya da wuri..
Waye wancan daya rako ta?umaymata tambayi kanta dan bayansa kawai ta iya hangowa sbd duhun wajen...,lallai kuwa akwai abunda wannan yarinyar ke boyewa..dole sai ta shiga jikinta sosai dan ta gano miye sirrinta..

    Da sauri ta kamo hannun juwairiya,kin dawo?dama neman ki zan fita yanzu wlh.. naji ne su laure nata cigiyarki ganin abokan aikin ki sun dade da dawowa babu ke..
  Juwairiya tayi murmushin yake,ai a baya suka baro ni ne..
Umayma tace Allah sarki muje ciki toh..
Juwairiya ta gyada kai suka shige ciki a tare..

************
Washe gari...
  Gimbiya kilishi ce tayi kiran surukan nata..
  Ta kallesu duka daya bayan daya kafin tace..

  Ina fatan ku duka kun samu labarin yarda al'adar masarautar mu take...
Idan har aka na'da sabon sarki toh dole ne idan ya cika sati na biyu a mulkinsa matansa ne da kansu zasu shiga madafa suyi masa girki...

     Khadija tadan murmusa dan dama ita jiran wannan ranar kawai takeyi,dan ta burge jalal ta samu yabawar sa..

surayya kuwa uwar son jiki cewa tai...
Umma amma dai na yau din kadai ne ko?
Kilishi ta gyada kai,yau da gobe ne tunda matansa biyu..
dan haka dolene ku raba rana kun yarda yayi muku.
wacece zatayi yau sannan wacece zatayi gobe..?

  Khadija tayi saurin fadin,ai umma tunda surayya ce babba ita ya kamata tayi yau din ni sai nayi gobe ko?
  Kilishi tace hakan ma yayi,ta maida kallonta kan surayya, kije ki shirya zan hadaki da du'bu dake Rumfar bayi..

Surayya tayi saurin yatsine fuska,umma a cikin RUMFAR BAYI zamuje yin girkin?

Kilishi girgirza kai tace,ai jinin sarauta baya shiga rumfar bayi..kanskanci a garemu hada jiki da bayin mu..

akwai madafa a can sabon bangare.. dan haka a can ne zakuyi girkin naku,sai ki zaba bayin da zasu taimaka miki..
Surayya ta gyada kai sannan ta mike cike da haushin wannan banzar al'adar ta fita..

***************
"Da safe"

"Koda juwairiya ta shigo sashen sarki,sai ta samu kanta da rasa taya zata shiga dakin na jalal.
taji dai ance tun asubahi surayya tabar sashen..

  Jakadiya ce tayi kiranta,da sauri ta karasa wajenta..
Kallonta tayi tana wani nazari kafin tace,ki shiga dakin mai martaba ki gyara masa..
Chapter 21 · 0% Book details