Sashe 44
Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna shiga sashen gimbiya amina samira ta fa'da jikinta cike da murna..
Amina ta dago ta,ashe har kun iso?
Samira tace,goggo wai ina su Ammi ne?
Amina tace suna can sashen yar uwar taki.
Zainaba ta duka ta gaishe da amina..
Amina tace,sannunki da zuwa yan mata ku karasa can din mana bari na saka a kaiku..
Ai kuwa gimbiya amina ta saka wata baiwa ta kaisu can sashen juwairiya..
Suna shiga a falo suka iske yan biyu da firdausi suna ta hidimar su..
Samira na yin sallama yan biyu suka mike cike da murnar ganinta suka rungume ta..
Zainaba kuwa da kallo take binsu,ita addu'ar ta daya Allah yasa ta hadu Mustapha taji dalilin da ya saka ya daina aiko mata da wasikun sa..
Gabanta ne ya yanke ya fadi..
Ganin juwairiya ta fito tare da ammi daga wata kofa...
Ware ido tayi tana tsananin mamaki sosai..
Wuce su samira tayi da gudu taje ta rungume juwairiya tana kuka sosai..
Juwairiya kanta sai data tsorata da ganin zainaba..
Amma jin zainaba a jikinta tana kuka sai ta shiga shafa mata baya..
Samira kuwa mutuwar tsaye tayi..
Ammi ce tazo ta riko hannun tana fadin saukar yaushe? ..
Juwairiya tasa hannu ta dago zainaba suna kallon junansu..
Tace,haba uwar dakina wannan kuka haka?
Zainaba takai mata duka,ai nayi fushi dake..
Ammi ta jawo hannun zainaba din itama ta shige dasu daki ta fayyace musu komai.
Murna sosai sukayi.
Da saurinsu suka fito falon suka sake rungume juwairiya suna taya ta murna..
Zainaba tace,ni dama na zargi ya jalal wlh,ace farat daya mutum ya canza?ta kalli samira.. sai fa kinga yarda ya tsane ta a baya ,amma lkc guda ya koma me taimakon ta ya dauke min ita daga sashena..
Hassana tayi dariya,ke baki san soyayya ake ta sha ba?
Zainaba tace ina kuwa zan sani?dan na lura ita juwairiyar ma bata dauke ni a matsayin kawar taba..
Juwairiya tayi murmushi tana sake rungume ta..
Haba kawalli ta,kinsan fa a duniyar bani da kamar ki..
Duk suka saka dariya...
"Magaji ne ya kalli jalal da bayi ke ta faman shiryasa..cikin kayan sa na alfarma..
AMALE ka fada min gsky mana?kasan dai baka da kamar ni ko?
Jalal ya juyo yana kallonsa..
Wace gaskiyar kika son ji ne Anaci?
Magaji ya zauna a kusa dashi..
Ni na san ranar hawan nan baka tsaya ganin diyar sarki abu-turab ba,toh a ina ka hadu da ita har kuka kulla soyayya haka?
Jalal ya kwashe da dariya..
Kai fa ka cika tambayar tsiya kamar wani alkali..
Toh bari kaji in fada maka.......
A nan jalal ya kwashe komai ya fadawa magaji..
Magaji ya dafe kirjinsa..
Kai amma kayiwa maza dayawa shigar sauri..
Wato a yarda nake ganin ka saida kaji saida kaji..
Jalal ya amshe..toh saida rakum'ma ne ni...fadi da kyau..!
Magaji yace,ahh lallai...wlh ni kaina naso wannan yarinyar a baya..
Jalal ya daure fuska,yace..
hattara dai magaji mallakin AMALE ce..
Magaji ya daga hannu cikin surrender yace,ai na dade da janyewa ma...
Su Turaki ne ya shigo tare da khaleed..
Turaki Ya kallesu..
Wai har yanzu ango bai gama shirin nasa bane?jama'a na waje suna jira..
Magaji yace kasan fa yau AMALE jin sa yake kamar wanda akayi wa albishir da aljanna, gayunsa ma na daban ne Yau!
Khaleed yayi dariya..yace
Kuma duk diyata ce sanadi ba..
Turaki yace ban gane ba?
Khaleed yace ai bazaka gane bane abokina muje na warware maka kan zaren..
Yaja turaki suka fice...
"Karfe biyu da zabi na ranar JUMA'A ASHIRIN DA TARA GA WATAN DISAMBA..
Aka daura auren SARKI JALALLUDEEN ABDUL-JABBAR,da kuma amaryar sa SARAUNIYA JUWAIRIYYA ABU-TURAB..akan sadaki mai tsokar gaske............
@TEAM RUMFAR BAYI...
_Godiya ta musamman ga duk wacce ta samu halartar wannan bikin..
Kada ku damu akwai sauran event idan mun koma can masarautar Daura..
Dan haka ku ci gaba da kasancewa da ni AFRAH bhai.._
XOXO😘😘😘
*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 39
Wattpad @afreey101
**********************
""Bayan an gama daura aure sai kuma aka fara shirin daukar amarya zuwa can masarautar daura ..
Gimbiya amina ce ta kai juwairiya har sashen sarki abu-turab abbanta yayi mata nasiha mai ratsa jiki sosai..
Duk da ba wani shakuwa ce mai karfi ta shiga tsakanin su ba amma sai da juwairiya ta zubar da kwalla sbd tasan sai tayi kewar mahaifin nata sosai..
Daga wajen sarki sai kuma akayi da ita akayi sashen gimbiya jamila itama tayi mata nata fadan sannan ta bata kyautuka masu yawa.. daga nan gimbiya amina ta maida ita sashen ta don shirya ta kafin tafiyarsu..
Su zainaba ne akan gaba wajen zolayar ta..
Sun saka ta a gaba suna ta gulmar sarki jalal wai ance tunda aka daura aure bakinsa yaki rufuwa..
Ita dai amarya tunanin irin rayuwar da zatayi a can masarautar daura kawai takeyi...ya zasu dauke ta?bare surayya data nuna tsanarta karara..kila gara ma khadija,ooh ita dai ta shige su,wata zuciyar tace,kema fa idan kin koma a matsayin matar mijinsu kike ba baiwarsu ba...
"An shiryata tsab a cikin leshi me shegen tsada kalar light blue da peach,sannan aka rufa mata alkyabba ta ga'do wacce ake kai duk amaryar data fito daga cikin tsatson masarautar kano..
"Wayyo Zanso kuga gogan naku,wato sarki jalal..kenan..
Gaba daya murna da farin ciki sunyi masa yawa..
Yau dai Allah ya mallaka rabin ransa,ya basa farin cikin rayuwar sa...
Baki yaki rufuwa magaji na gefen sa sai zuba masa ruwan zolaya yakeyi amma ko a jikinsa..
Shidai hamdala kawai yakeyi wa Allah..
"An kawo motocin daukar amarya a nan sarki abu-turab ya zabi mutanen da zasu tafi kai ta..
G-amina ce tare da jakadiya,se hanne baiwarta da kuma AMMI,da yan uwa da suka zo daga kasar zazzau..
Dan shi kam Baya son yawan jama'a kada ace can a samu wata matsalar.
"""""Kuka sosai juwairiya tasha ganin an fito da ita daga cikin masarautar su ga bayi nan a bayansu sai wakar al'ada sukeyi na daukar amarya..(suna mata bankwana kenan)
Hanne kuwa murna kashe ta zata bi uwar dakin ta..
Zainaba dasu samira kuwa sunyi murna juwairiya zata koma garesu..
"Lkcn da suka fito dangin jalal na waje harma da abbansa..
A nan aka shiga motoci liman yayi musu addu'a aka dau hanyar DAURA...
**************
Lkcn da suka isa masarautar daura yamma tayi sosai..
Hamza da nafisa tare dasu fulani da gimbiya kilishi ne suka tare su cikin girgimawa..
Juwairiya babu abunda gabanta yakeyi sai faduwa,tana kunshe acikin alkyabba gimbiya amina da ammi na rike da ita..
Nan aka hau gaishe gaishe gimbiya kilishi ta hada su da jakadiya tace ba sai an kai amarya sashen ta ba,kawai su huce can sashen amaryar dan su samu hutawa sosai kafin anjima..
"Kilishi na barin wajen ta jawo hansai dake ta leken ko zata ga fuskar diyarta..
Sashen khadija sukaje dan kuwa kilishi ta fara jin haushin rainin hankalin da suke son suyi musu..
A hakimce ta tarar da ita tiren kayan kwalam a gabanta..
Rabi na gefe tana ji kamar tayi tsuntsuwa taje wajen tarar su amaryar da akeyi,dan tasan zata kwashi kallo bare ance diyar sarkin kano ce...wai!yanzu se de taji lbr a RUMFAR BAYI kenan?
Kilishi ta kalli khadija rai a bace..
Khadija ta mike da sauri tana fadin..
Umma sannu da shigowa..
Kilishi tace,rike sannunki..haka ake rashin lfyr dama?ni dama na zargi wani abu wlh..
Khadija tayi saurin sadda kai kasa tace,sauki na samu ne yau umma..
Kilishi tace,shine baki fito tarar bakin ba?
Ko duk haukan kishin naku ne haka?
Kuke son ku jawo mana wani sabon raini daga wajen mutanen nan..
Khadija tace,kiyi hakuri umma zanje yanzu nayi musu sannu..
Kilishi taja tsaki tayi gaba a fusace...
Sashen surayya ta sake nufa..
Surayya tasha gayunta ta cancare dan tunda ta tashi yau ciwon cikin da take faman ya ragu..
Ita kam ta riga tayi wa kanta fada..
Sam ba zata taba bari jalal ya gano halinta ba.
zata nuna masa har cikin ranta tana son wannan auren nashi da yayi..
tayi murmushin mugunta (ni kuwa nace manipulator kawai😂)
Umayma ce ta shigo dakin a rikice tace,ki fito ranki ya dade gimbiya kilishi ta shigo..
Surayya taja tsaki,ai nasan sai anyi haka tunda wannan yarinyar (khadija) tayi irin nata rashin yawon nakin zuwa tarar su..
Ai gashi nan ta jawo mana..
Fitowa tayi kawai da masifa kamar gaske..tana fadin..
Umayma ba sai dana ce miki idan sun iso kizo ki sanar min na fito bane?
Kilishi ta kalleta,ke yanzu har kin shirya amma fitowar ta gagare ki?
Surayya tayi fuskar tausayi..
Allah umma se da nace a sanar min ba gashi har shiri nayi ba,Ashe ma har sun iso?..
Kilishi taja dogon tsaki ban sani ba... ta juya cike da takaici ta fice hansai ma girgiza kai tayi itama dan sun san duk karya ta shirya indai surayya ce (fake)
Suna fita surayya taja tsaki,dan ma rainin wayo ni suke tsanmanin na je na taro kishiya ta mtsww...ai bazai sa'bo bane...!
********************
An gabatar musu abinci me rai da lafiya..
G-amina ta saka hanne ta diba wani a cikin dan kwano sannan ta amsa ta shiga uwar da'ka inda su juwairiya suke..
Gaba daya hankalinta baya wajen,ko firar dasu yan biyu suke tayi ba jinsu takeyi ba..
Ita dai a yanzu abubuwa dayawa ne acikin zuciyarta..
Ya zatayi rayuwa tare da jalal a matsayin matarsa?
Ya zatayi rayuwa da matansa..?
Ya kuma gimbiya kilishi zata dauke ta?
Sannan ga son ganin su ummata da takeyi..
Dafa ta da gimbiya amina tayi ne yasa tayi firgigit ta dago ta kalleta..
Zama tayi a kusa da ita tace..
Ki rage wannan tunanin juwairiya, addu'a da dogaro da Allah shine kawai ya kamata ki saka a gaba..
Zan baki wasu addu’o'i da zaki ringa yi sbd tsari,nasan rayuwa acikin GIDAN SARAUTA ba karamin hadari bane idan baka tashi tsaye wajen rokon Allah ba..balle ke mai kishiyoyi da har suka ki zuwa tarbar ki..
Juwairiya ta gyada kai tace nagode sosai..umma sai dai inaso dan Allah ki saka a kira min su ummana na nan,inaso na gansu...
Gimbiya amina tace toh shikenan dama mahaifinki ya bada sako a basu sbd nuna godiya ga rikon da sukayi miki...