← Book details Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 53

Sashe 50

Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayyo zo kuga murna kamar yayi mai..!dadi sosai ya mamaye zuciyarsa..
Ya kasa ma yarda wai juwairiyar sa ce keda cikin sa a jikinta?..
Ya mike babu shiri yayi waje..

Ko Kafin ya karasa sashenta sai da yayi kyauta har babu adadi duk wanda ya hadu dashi se ya bashi wani daga jikinsa...

Yana shiga sashen nata ya tarar da hanne a falon..
Tace masa ai uwar dakin nata na cikin uwar daki..

Ciki ya shige cike da murnarsa..
A lkcn juwairiya na tsaye ne tana daura zaninta..
Sai ji tayi kawai anyi sama da ita..

Jalal na dariya cike da farin ciki marar misaltuwa ya shiga juyawa da ita yana ta shi mata albarka..
Sosai take dariya itama tana rokon sa daya sauke ta kasa..

Jalal ya sauke ta kan gado yana kamo hannayenta duka biyun ya rike gam..
Yace..
Giwata na gode kwarai da gaske..
Juwairiya ta lumshe masa ido tace..
Amale ai Allah ne abun godiya bani ba ..

Jalal yaja lumfashi ya daga kansa sama yace..
Ya Allah na gode maka da wannan babbar kyautar da kayi mana,Allah kayi wa dan mu albarka ka kuma sauki matata lafiya..
Juwairiya na murmushi ta amsa da amin..

Jalal yace,wlh bakiji irin farin ciki da nake ciki bane yanzu..
Khadija zata haihu haka ma kema a cikin wannan shekarar zan zama baban yara biyu....

Juwairiya ta dan kamo hannunsa..tace
Amale ka kuwa samu lkcn tambayar surayya meke damunta?

Jalal ya girgiza mata kai abubuwa ne dayawa a kaina juwairiya..
Amma zan saka hamza ya dauko min me magani zuwa gobe se a duba ta..

Juwairiya taja lumfashi tace hakan ma yayi..
Jalal ya rungume ta yana fadin..
Na kagara naga dan'mu/yarmu ni dake Giwata..
Yadan rike habar sa🤔Ko dawa zayyi kama a cikin mu?
juwairiya tayi dariya..
Da ni mana tunda a cikina yake..
Jalal ya dago fuskarta yace..
Ke yarinya SARAKI da babansa zayyi kamanni..
Juwairiya tace amma ai a cikin mamansa yake ko?😛

Jalal yadan turo baki...
Wato ma zolaya ta kike ko?
juwairiya ta make kafada ni na isa nayi wa baban SARAKI zolaya?
Jalal ya mike yana fadin..
Toh bari naje wajen khadija tunda ita har addu'a takeyi danta/yarta yayi kama da ni..

Juwairiya tayi saurin mikewa tana fadin..
Nima ai na yarda..
Jalal ya kwashe da dariya yana sake rungume ta ciki da tsantsar farin ciki da nishadi...

Team RUMFAR BAYI
*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 42
Wattpad @afreey101

_"Fans please ina neman addu'ar ku,October dinnan zan fara exams dina inshaAllah,shi yasa zaku ga ina yanke lbrn dan na gama muku shi a cikin lkc na fara karatun jarabawata.._
_Thanks for all your love.._
_Ina Yin'ku sosai😘_

********************

"Surayya abun duniya ya taro ya fara yi mata yawa..
Girman kai gaba daya ya hana ta zuwa neman gafara a wajen juwairiya..

Gashi kuma yanzu jalal ya dauke mata kafa daga dukkan al'amuran ta ko sashen sa ya daina gayyatar ta..
tun ranar dayayi kiranta tayi masa alkawarin zata je ta nemi gafarar ta har yanzu bai waiwaye ta ba
Sai dai taji yaje wajen khadija da amaryarsa..

     Yau dai fada tayi wa zuciyarta sosai ganin bata da wata mafita..
ga kuma wannan ciwon cikin daya dawo mata kullum dare sai tayi fama dashi tun lkcn da tasha maganin malamin nan a kwanakin baya ta kasa ganewa jikinta gaba daya..
Ga mafarkai barkatai da takeyi,duniya dai tayi mata zafi sosai,taja lumfashi..
Gara naje na nemi gafarar ta wata kila na samu sausaucin abunda nake ji..

***************
"Abun mamaki juwairiya na zaune a sashenta dasu hansai sai ga surayya ta shigo da sabowar baiwar ta...
   Ga babban mamakin su juwairiya sai gani sukayi surayya ta dage sosai wajen neman gafarar ta..

Tayu mamaki sosai amma sai Tace.. babu komai ita ta yafe mata,Allah kansa ma muna masa laifi ya yafe mana balle kuma dan adam?..
Ita dama bata rike ta ba....
Surayya taji dadi sosai,dan gaba daya ma sai ji tayi juwairiyar ta burge ta bata dauki duniyar a bakin komai ba ita kuwa sbd shaidan ya tafi da tunaninta tayi ta wulakanta ta a baya oh?duniya kenan!..

Ai kuwa tun daga ranar sai surayya taji nauyin dake zuciyarta ya ragu sosai,sai dai wannan ciwon ciki da zame mata tilas kullum dare da kyal take samun barci...
Ta rasa mafita gashi yakumbo kanta bata kasar balle ta saka ta ta nemo mata magani..

Bayan wata uku..

******************
A cikin watannin nan da suka gabata ba karami shakuwa da zaman lafiya bane ya shiga a tsakanin  matan sarki jalal ba..

Abun mamaki Yanzu kam surayya sai  shige wa juwairiya takeyi  dan kafin kaganta a sashen khadija toh zaka kanta a sashen juwairiya sau ba adadi duk wani shawara wajenta take zuwa..
sai dai har lkcn ta kasa fadawa kowa abunda take ciki..
duk ta rame ko jalal ya tambaye ta sai tace masa kawai babu komai..kada ya damu..
shi kam ma abun har ya fara basa tsoro dan yanzu ya lura gaba daya surayya bata yarda ta kwana a sashen sa..
Ba kamar da ba da take matsawa sosai sai ya kwana da ita...

"Khadija kam ta maida juwairiya tamkar kawarta dan har dakinta inna (mahaifiyarta)tazo tayi mata kaca kaca akan ta samu lbr a gidansu wai goggo na kawo wa diyarta magunguna....
ba karamin tashin hankali ta shiga ba shine tazo da kanta tayi mata fada mai ratsa jiki..
Sannan ta bata shawarwari wadan da zasu amfane ta a zaman auren ta..

Tun daga lkcn khadija ta saduda sosai ta mayar da juwairiya kawarta..
sai su ringa hadewa a can sashen fulani suna shan firar su dasu zainaba...

"Kamar kullum magaji ne ya shigo cikin masarautar dan amsa kiran sarki jalal...
yana tafe ne yana mamakin neman gaggawar da Amale keyi masa..
Caraf ya hango ta tana tafiya da baiwarta a baya amma da gani hankalin ta gaba daya baya jikin ta..
ganin yarda tazo har ta wuce sa bata ko ma lura dashi ba..

    Juyawa yayi yabi bayanta da sauri yasha gabanta..
Duk da haka ko ganinsa ma batayi ba har sai data ci karo da shi..Bum!

  A tsorace sosai tayi baya zata fadi kasa..
Yayi saurin taro ta ya rike ta gam yana karewa kwayar idonta kallo..
Wani irin abune yaji yana yawo a cikin cikin sa..

Ita kuwa Ji tayi kawai kirjinta na bugawa da sauri da sauri..
Magaji ya kyara mata tsayuwarta sannan yace..
KANWARMU  lafiya?
Zainaba ta danyi kasa da kai tana jin hawaye na sauka akan kuncin ta..

A take hankalin magaji ya tashi yaji gaba daya yana son yaji meke damun ta haka..
Zabba'u ya kalla yace,ki jiramu a can muna zuwa...
Zainaba tayi saurin kallonsa..
Sai gani tayi kawai yaja hannunta yayi gaba da ita...
Haka nan taji ta kasa yi masa mgn sai bin shi da takeyi kawai har suka kawo cikin lumbu...

Ya zaunar da ita akan kujera sannan ya tsare ta da ido yace..
Kanwarmu ki sanar dani damuwarki dan Allah.?
Zainaba ta kura masa ido..
Hakanan taji zuciyarta ta aminta da sanar wa magaji damuwarta,dan kuwa ko juwairiya ta kasa fadawa meke damun ta duk da dai tuni juwairiya ta da'go inda damuwar kawar tata tayo asali..

"Lumfashi taja mai tsayi kafin ta fada masa komai dake tsakanin ta da Mustapha..
Magaji yayi shiru yana nazari a kalla har anyi wata hudu kenan zuwa biyar amma babu wasikar Mustapha? Kuma bai neme ta ba?

Tabbas akwai abunda Mustapha ke boyewa zainaba..
Magaji ya zauna a gefenta yace,ki kwanta da hankalinki kanwarmu na miki alkawari inshaAllahu zuwa gobe zan nemo miki amsoshin tambayoyinki akan dalilin da ya saka Mustapha na daina aiko miki da wasikun sa..

Zainaba ta saki murmushin murna tace nagode yaya magaji..
Yayi murmushin shima..yace
Kada ki damu kanwar mu yanzu dai bari na karasa can fa'da dan Amale ne ma yayi kirana..
Zainaba ta gyada masa kai tace..
nima sashen Giwar amale nayi yanzu..
Suka fito a tare sannan kowannen su yayi hanyarsa...

"Lkcn da zainaba ta shiga sashen na juwairiya sai tarar da gaba daya matan gidan tayi a ciki.
batayi mamaki ba dan dama duk ranar ta juma'a a nan suke wuni,sai kuma asabari suje sashen khadija,ranar lahadi kuwa sashen gimbiya surayya suke....

Juwairiya ta kalli zainaba tace..
Zauna nan kawata kiji...
ta nuna mata waje kusa da ita...
dan a Yau juwairiya tayi alkawarin fayyace wa zainaba abunda ake ciki dangane da mgnr Mustapha..
Cike da lallashi ta fara mgn..

"Zainaba inaso na fada miki wani abune dangane da Mustapha..dan na san duk wannan damuwar da kika shiga kwana biyu duk sbd shine..
ko nayi karya?
Zainaba taji gabanta ya fadi..ta girgiza mata kai a sanyaye..
Juwairiya taci gaba..
toh mgnr gaskiya na samu wasika daga wajen yarimaADO ne shekaranjiya dan na saka ya nemo min lbrn Mustapha..duk da dai ya taba fadamin zayyi auren biyayya ga iyayensa..
Toh Ado dai ya tabbatar min da cewa a jiya ne aka daura auren Mustapha da diyar sarkin kasuwa na kano..

Zainaba ta runtse ido sai ga hawaye shaaa..
Juwairiya ta rungume ta cike da tausayawa dan tafi kowa sanin yarda zainaba ta mutu akan wannan Mustaphan..
amma ita kam tunda Jalal ya sanar mata da lbrn alkawarin mai martaba na hada auren zainaba da magaji...
sai taji ma tafi son ta da magajin sau dubu shiyasa ta dauki alwashin sai ta san yarda tayi ta hada su suka fara soyayya..
kafin auren nasu na tashi....
sbd dai bata son zainaba tayi aure babu ko digon soyayya a cikinsa..

"A sanyaye tace..kada ki damu kawata,na tabbata Allah zai baki mijin da yafi shi....
Zainaba ta share yan kwallan ta..
tace
Ni dama naji a jikina akwai babban al'amarin da Mustapha yake boye min..
amma me yasa bazai fadi min gsky ba,menene amfanin soyayyar da yake min?ai bata da wani amfani..ta karashe mgnr cike da jin haushin Mustapha a cikin zuciyarta..ya yaudare ta dayawa..

    Samira ce ta dafa ta tace,ai dama shi yasa bin umarnin iyayenmu wata sa'in shi yafi wlh dan sun fi mu sanin abunda duk yafi dacewa da mu..
Chapter 50 · 0% Book details