← Book details Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 53

Sashe 39

Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A yau ne su yarimaADO suka dawo daga tafiyar su...
Sashen ummansu amina suka fara sauka..
Tayi farin ciki sosai da ganinsu..
Cike da zumudi take sanar dasu zuwan  juwairiya...
sanan ta fada musu duk lbrn ta tunda tasan basu san ta ba..
   Sunyi mamaki sosai wai suna da yaya mace?
Amina tace kuje ku dan huta sai ku shiga sashen na ta ku ganta..

"Sai da suka huta sukaci abinci sannan suka nufi sashen nata..
A lkcn juwairiya na zaune a falon ta hanne na gefenta suna yar firar su..

Sai jin sanar da shigowar su YarimaADO sukayi..
   Hanne ta kalleta da sauri..
Yan uwanki ne yaran gimbiya amina..
Juwairiya taja lumfashi, ashe itama tana yan uwa?
    Cikin takon kasaitarsu suka shigo...
Juwairiya ta kura musu ido..
Zama sukayi a gabansu cikin sanyinsu..
Hanne tace,sannunku da shigowa ranku ya dade..

YarimaADO ya jinjina kai kawai yana kallon juwairiya, yace..
Mun same ki lafiya?
Juwairiya mamakin irin nutsuwar su takeyi..
Tace lafiya,kun dawo lafiya?
Abdullahi yace lafiya kalau yaya,gashi har munzo miki da tsaraba ma..
Juwairiya ta bude baki,ni?

YarimaADO ya kalli hanne yayi mata alama akan ta fita ta shigo da sakon..
Juwairiya dai kallon su kawai takeyi,tasan zata girmewa Ado da shekara daya amma ji yarda ya fita girman jiki sai kace shine babba a cikinsu..

Hanne ta ajiye dan akwatin a gaban juwairiya..
Ado yace,ki duba ki gani ko yayi miki..
Juwairiya tasa hannu ta bude..
Ware ido tayi ganin turaruka ne da sarkar lu'ulu'u...

Tunda take bata taba mallakar irin wannan kyautar ba..
Hawayene suka shiga fita daga cikin idanunta..
  Ado ne ya mike ya dawo kusa da ita..
Ji tayi ya sa hannu ya juyo da fuskarta saitin da yake..
Ta kura masa ido..
Ya girgiza mata kai..
Kada ki damu yaya,munyi miki alkawarin kula dake..
Zamu nuna miki soyayyar da kikayi rashi a baya..
Dan haka kada ki sake zubar da kwallar ki kinji?
juwairiya ta yaba da hankalinsa sosai..

Murmushi tayi tace,bazan sake ba..
Ado ya dauki sarkar ya koma bayanta ya saka mata ita..
Juwairiya a take ta tuna da jalal,ta runtse idonta...
ina fatan dai bai fara mantawa dani ba?ina fatan bai manta da alkawarin da yayi min ba..
  Ji tayi Abdullahi ya rungume ta,ta saki murmushi cike kaunar yan uwan nata...

Satin ta daya a masarautar kano..
Yau ta shirya musamman dan zuwa gaida gimbiya jamila a sashenta..
    Tafe suke ita da hanne..
Duk inda ta wuce sai bayi sun gaishe da ita..
Juwairiya sanin itama ta taba irin wannan rayuwar..
Duk bawan daya gaida ita sai ta tsaya ta amsa masa cike da sakin fuska..hakan kuwa ba karamin dadi yake yi wa bayin ba.

"Gani tayi wani kawai yasha gabansu..
Ta dago suka hada ido dashi..
A tare suka nuna junansu cike da mamaki..
MUSTAPHA  ta fada cikin mamaki..

Mustapha ya kura mata ido..
Lallai ashe dai ke dince JUWAIRIYA..
Juwairiya tayi murmushi nice kuwa..
Mustapha yace,Allah me iko ashe dai ke din yar kasar muce..

Naji ana ta zancen sabowar sarauniyar mu data bayyana ashe kece...
Juwairiya ta gyada kai nice kuwa Mustapha..ina kawata zainaba?
   Mustapha ya dukar dakai yana fadin ni kaina ban samu rubuta mata wasika ba kwana biyun nan..
Juwairiya tace,yooh me ya faru?
Mustapha yace,kinsan abbana har ya kai kudin aurena can gidan sarkin kasuwa toh wlh na rasa da wace kalma zan iya sanar da zainaba..
Dan banyi mata adalci ba ko kadan kin sani..

Juwairiya ta jinjinar dakai..
Kada ka damu Allah zai kawo maka mafita..
Mustapha ya kalleta..
Amma fa kin canza sosai,kin ganki kuwa kamar wata sarauniyar kyau?
Juwairiya ta murmusa..
Hanne dake sauraren su tace..ai sarauniyar kyaun ce ranki ya dade.
Mustapha yayi dariya yanzu sai ina?
Juwairiya tace sashen gimbiya jamila zani je..
Yace toh muje na taka miki...

"Ta shiga sun gaisa da jamila,macece me saukin hali sosai,da diyarta firdausi yar kimanin shekara goma..
A take jininsu ya hadu dana juwairiya sai fira suke tayi mata...

*************

Masarautar daura...

Shekara ta zagayo abubuwa dayawa sun faru a cikin wannan masarautar...
     Shirye shiryen bikin BABBAN SALLAH sukeyi dan haka masarautar ta cika tam da mutane...

Gimbiya kilishi ce ta saka hansai tayi mata kiran matar sarki dukkansu..
   Batayi wani tunani ba kawai ta sanar dasu abunda ke cikin zuciyarta..
Wato na rashin haihuwar su har zuwa wannan lkcn..
Surayya ji tayi kamar ta hau laka'da wa kilishi duka,lallai ma duk kokarin da takeyi?
Lallai dan Matar nan bata san cewa dan nata bane baya basu wani hadin kan kirki shiyasa ta tsare su da irin wannan mgnr ta rainin hankali...

Kilishi ta sake fadin,idan har baku samu haihuwar nan zuwa karshen shekarar nan ba toh aure zan karawa JALAL sannan na zaba masa kwarkwarori..dan ina son dana ya samu MAGAJINSA tun ina da raina..
Ku tashi ku tafi...

Surayya kamar zata tashi sama..
Khadija kam jiki a sanyaye ta fito..
Surayya ce ta tare ta,tace..
ke yanzu ya zakiyi ne?kina dai jin matar nan ko indan bamuyi a hankali ba se ta saka jalal duk ya sallame mu,se kace mune zamu yiwa kanmu cikin...

Khadija ta jinjinar dakai kawai dan kuwa ita duk kwanankin nan bata wani jin dadin jikinta ko kadan..
ga amai da kasala da take fama dasu..
   Surayya ta shiga binta da kallo,ina mgn kinyi shiru..
Khadija na yunkurin mgn sai ga amai yazo mata...
   Rabi ce tayi saurin rikota tana fadin..
Ranki ya dade mu koma sashen ki a kira me magani ta duba ki..

   Surayya taji gabanta ya fadi..
Muryar umayma ce taji a bayanta..
Uwar gidana ina kyautata tsanmanin matar nan cikine da ita fa?

Surayya taji zuciyarta tayi baki,tace nima ina tunanin hakan..umayma..

Amma Ki shirya yanzu dole ne mu koma wajen malamin nan,dan bazai taba sabuwa ba ace khadija ta rigani haihuwa a cikin masarautar nan...

"Magaji ne ya bi jalal da kallon mamaki..
Me kake nufi ne AMALE ?ban gane..
bayan sallah na shirya zamuje kasar zazzau ba? Me zamuyi a can din?

Jalal dake zaune a saman kilisar sa ya daure fuska..yace..
Magaji me yasa ka cika shegen gardama ne..
Idan bazaka je din ba ai sai ka fadin min kawai..
Magaji ya girgiza kai,haba WANDARA kasan fa ni mai bin umarnin kane,kawai dai mamaki nakeyi me zai ka kasar zazzau haka cikin kurarren lkc ..?
Jalal ya tabe baki..
Magaji ya gyara zama yace...
yauwa kama tashi muje ka zabi DOKIN ka na hawa,dan su turaki da hamza kai kawai suke jira ka zaba kafin su zabi nasu suma..

  Jalal ya kwabe fuska..yace
Bana fa bana jin zanyi wani hawa a wannan shekarar...
Magaji ya saki baki yana kallon shi (kwanankin nan gaba daya ya lura jalal ya canza,bai cika yawan fara'a ba ga sai fadan tsiya abu kadan sai ya hau mutum da masifa bacin ba haka ya yake da ba)

    Kana nufin a wannan shekarar daura zasuyi hawan sallah babu sarkinsu kenan?
Jalal ya daga kafada bai ce komai ba..
Magaji yace,toh bari kaji ma na fada maka abbanka da nawa har sun amshi takardar gayyata daga kasar kanon dabo...

Jalal yace gayyatar me..
Magaji yace hawan daushe mana,kasan fa duk shekara ana haduwa kasashe kasashe ana  gasar hawa...
  Jalal yaja tsaki ni babu inda zanije,na fada maka dai,bayan sallah da kwana biyu kasar zazzau zamu je kallas...

************
Masarautar kano...

Suma a can din shirye shiryen kawai sukeyi,dan sarki abu-turab ba karamin shiryawa wannan bikim sallar yayi ba dan yanaso ya gabatar da diyar sa juwairiya ga al'ummar kasar ta sa..

Ado ne ya shigo sashen juwairiya..
Ya same ta tare dasu firdausi da hanne suna firar su cikin nishadi..
   Yaya taso muje ki zabar min dokin da zan hau yau..
Juwairiya tayi dariya..sannan ta mike suka fita zuwa can wajen dawakai..
  Wani fari dokin ta zabar masa,yayi murna sosai daga nan sukayi sashen amina..
Anan ta tarar da tulin kayan da abbanta ya saka akayi mata na cin sallah..
Godiya sosai tayi wa amina..sannan ta je har fada ta tayi wa abbanta nata godiya..

*YAU TAKE SALLAH...*

Gaba daya masarautar a hargitse take..
Baka jin komai sai Kide kiden ALGAITA DA bugun TAMBARI..
Hanne ta shirya juwairiya cikin kaya na alfarma sosai taci ado har ta gaji kyau kam ba'a mgn..

Sashen amina taje a nan ta tarar da su ADO da Abdullahi sunsha gayun su suma...
Abinci me rai da lafiya aka gabatar musu sukaci...
Sannan sarki abu-turab ya saka azo ayi masa kiransu..zuwa fadarsa..

Team RUMFAR BAYI

Team JULAL...kuci gaba da hkr in the this page JALAL N JUWAIRIYA will surely meet..
.[9/25, 7:53 AM] 0mer Farouk:            *RUMFAR BAYI*
       (A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 36
Wattpad @afreey101

***************

     "Mutane ne cike a cikin masarautar kano..
Sarakai daban daban daga kasashen nigeria dama na tsallake..
Taro kam ya hadu iya haduwa..

       "A can na hango wani kamar sarki JALALLUDEEN akan wani doki yasha gyara na alfarma..
Mamakine ya kamani,nayi saurin karasawa wajen ina kare masa kallo,wannan tabbas shine...jalal ne...

      "Magaji dake gefensa saman nashi dokin yace..
AMALE ko kai fa?
Yanzu da baka zo wajen nan ba ai da ka ja mana raini..wlh

Jalal ya yatsine fuska,yace..
kasan fa in ba dan abbah ya saka baki ba akan sai nazo da bazan zo wajen nan ba kasan bana son hayaniya dayawa...

Magaji yayi murmushi yace,gsky sarki abu-turab yayi kokari mutuka,kaga yarda wajen nan ya kayatu kuwa?gashi ina jin ji'te ji'te akan yau zai gabatar wa jama'a  diyarsa data bayyana..

  Jalal yaja tsaki,kasan dai bani da wannan lkc da zan  bata..
da mun gama zagayen da ya zaman min dole babu wani abunda zan jira a nan..
Magaji yayi dariya....yace...
An gama...

"Sun sha zagayen hawan na daushe..
Mutanen kano sun sha kallo,jama'a ne kamar ba gobe..

Lkcn da suka koma cikin masarautar suka tarar da sarki abu-turab da iyalensa yana gabatar dasu ga al'ummar tasa..
  Jalal ya juya ya kalli magaji daya ja ya tsaya yana maida hankalinsa wajen da su sarki abu-turab suke..

    Tsaki yaja ya juya dogarai na rufa masa baya..
Har yayi taku daya zuwa na biyu ne kawai yaji ana anbaton sunan SARAUNIYA JUWAIRIYA...

Ji yayi gabansa yayi muguwar faduwa.....Juwairiya?
Yaji gaba daya zuciyarsa na mutukar son ganin fuskar me irin sunan juwairiyar sa..
Chapter 39 · 0% Book details