← Book details Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 53

Sashe 45

Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gimbiya amina na fita daga dakin ta samu jakadiya ta wajensu knan tace taje ta samu jakadiya ta masarautar daura ta fada mata suna son ganin iyayen juwairiya..
    Ba'ayi minti sha biyar ba sai gasu sun shigo sashen...

   Juwairiya dake cikin daki ta fito da gudunta..
Sumewa ne kawai hansai,da laure basuyi ba..
Baki bude suke kallonta cike da mamakin canzawarta..
Juwairiya ta fada jikinsu tana kuka sosai..
Hansai ta shiga lallashinta hakama laure..

Ammi da gimbiya amina sukayi musu godiya sosai..
Sannan suka basu dukiya me tarin yawa daga sarki abu-turab..
Da kyal juwairiya ta saka suka amsa..
Gimbiya amina ta sake yi musu albishir akan gobe mai martaba tsohon sarki Abdul-Jabbar yace zai yantar dasu sbd dai mai martaba na zazzau ya fada masa komai akan juwairiya...

'Bayan an gama hutawa ne sai kuma aka shiga shiryawa dan gabatar da babbar liyafa dasu gimbiya kilishi suka hada musu...

     Juwairiya ta sha gayu kamar ba gobe,ta haska iya haskuwa..
Kayane Ammi da kanta ta saka ayi mata na musamman..

   Samira,zainaba da yan biyu sune a kan gaba wajen shigowa da amarya...
Ango jalal yasha gayunsa shima sai daukar ido yakeyi...cikin manyan kala na alfarma ga fuskar nan tayi shar sai sakin murmushi yakeyi,su turaki na zolayarsa..

Ga kuma khadija da surayya a can kusa da gefensa kowacce sai cika take tana batsewa..abun duniya ya taru yayi musu yawa amma babu halin nunawa..

    Gimbiya amina ce ta karaso wajen rike da hannun juwairiya fuskarta na rufe acikin babban mayafi me kyan gaske..
A kusa da jalal gimbiya amina ta zaunar da ita tana rada mata wani abu a kunnne..
Kamshinta ne ya daki hancinsa ya lumshe ido yana jin wani farin na mamaye shi..
Juwairiya kam addu'a kawai takeyi acikin ranta..tasan idan har fuskar ta bayyana mutane dayawa zasu girgiza..
Sai jin dumin hannun jalal tayi a cikin nata..
Taja lumfashi..
Yadan kai kansa kusa da ita kadan..
Yace..
Ki kwantar da hankalinki GIWAR AMALE sarki jalal na tare dake..
Ji tayi wani karfi yazo mata..
Ta sauke lumfashi mai nauyi..
A tare duk suka saki murmushi..

      Fulani ce ta mike tace,a bude mana fuskar sabowar diyarmu mu kanta..
  Zainaba tayi saurin fadin..
Ah ah umma se kun bamu kudin budar kai ko ya kukace?ta kalli nafisa da samira...
Samira tace,hakane kam se an biya mu zamu bude fuskar amaryarmu.
Yan biyu suka dawo kusa da juwairiya da jalal sukace..
Sarki muna jiran kyauta me tsoka daga gareka..

   Surayya ta tabe baki,umayma tayi mata rada a kunne,uwar dakina naji fa ana ta yaba kyawun wannan amaryar..
Surayya taja tsaki,toh sai me?nima ai kyakkyawar ce..
Ta banka mata harara..
Khadija dake gefe ta tabe baki..
Ita dai ta yanke shawarar duk wata kisisina se tayi ta dan samun soyyayar mijinta baza ta zauna wata amarya ta kwace mata shi ba,duk irin shekarun da tayi tana kaunarsa..

"Gimbiya kilishi cikin kasaita ta kalli jakadiya tace,a basu duk iya adadin azurfar da suke so..
Shewa suka hau yi..
Ammi ta karasa ta ya yaye lullubin dake kan juwairiya....

Faduwar gaba ce ya ziyarci gaba daya mutanen dake wajen...
Menene haka suke gani?
Ya akayi BAIWAR RUMFAR BAYI juwairiya ta koma diyar sarkin kano kuma matar sarkin su JALAL..
Ina TABON nata yake..
Ya akayi fuskarta babu wannan konewar...????????? (So many questions in different minds)

   Umayma ta ware ido cikin mugun mamaki tace..
Ranki ya dade ta nuna mata gefen da juwairiya take..
Surayya tayi saurin mikewa tana jin zuciyarta kamar zata tsaga kirjinta ta fito waje..

     Meye haka take gani?
Dama wannan baiwar ce jalal ya auro.?
Ya akayi hakan ta faru..?
Ina tabon fuskarta yake?inaaaaaaaa

Taji lumfashin ta na niyyar daukewa..
Taya akayi kaskantacciyar baiwar can ta zama diyar wani sarki?
    Zufa ta shiga keto mata...
Umayma ce tayi saurin zuwa ta kamo hannunta..
ta fakaici idon mutane ta fice da ita da sauri daga wajen dan kada tayi musu(creating scene)a wajen....

Jalal kuwa da juwairiya kallon juna sukayi..suna aikawa junansu sakon soyayya..

Gimbiya kilishi da fulani suka kalli juna cikin al'ajabi sosai..
Ammi na ganin halin da suka shiga sai ta nemi yin mgn dasu..
Gefe suka koma da gimbiya amina.. sannan cikin nutsuwa suka sanar dasu duk abunda ya faru..
Gaba dayansu sunyi mamaki sosai.
Wai jinin sarauta ce tayi bauta a karkashinsu..
Gimbiya kilishi ta jinjina mgnr sosai amma tunda dai har juwairiya jinin SARAUTA ce da sauki sosai...

"Ansha liyafa an gama lafiya, su magaji an gwangwaje hakama hamza da su zainaba abun dai ba'a magana...
Taro ya tashi lafiya kowa ya koma makwancinsa dan sauke gajiya...

************
Umayma ta dauko ruwa ta bawa surayya da sauri ganin yarda take fitar da lumfashi da kyar kyar

uwar dakina ki kwantar da hankalinki..kada mutane su ga'no me muke ciki har asirinmu ya tuno..

Surayya ta zube kasa tana rusa kuka..tana fadin..
Ni jalal zai yiwa haka?
Ace ya auro baiwar da nafi tsana a duk rayuwata a matsayin kishiyata?
Umayma bazan taba yarda ba ta mike da sauri tayi waje..
Umayma tabi bayanta da gudu tana fadin innalillahi...

"Jalal a gajiye yake sosai,yana shiga sashensa yayi wanka ya haye kan gadonsa..
Ba karamin kagara yake yi ba gobe tayi..
ya ganshi tare da amaryarsa juwairiya..ya jawo filo ya rungume..

Ji yayi kawai an banko kofar dakinsa an shigo..
Yayi saurin mikewa yana kallonta da mamaki..
Kamar wata zararriya..

Tayi kansa tana kukan bakin ciki..
Ta rirrike rigar dake jikinsa..
Yanzu ni zaka wulakanta jalal!

Ka auro wannan baiwar a matsayin kishiyata bacin kasan yarda na tsane ta..
Kasan BANA SONTA bana son ganinta!!!!..
Jalal ya ture ta daga jikinsa..
Bakya sonta?ya fada cike da takaici..
toh ni INASON TA KUMA INASON kasancewa da ita a tare dani..!!!!

Surayya ta mike cikin mugun fusata tace..
   Sbd wata baiwar banza ka ture ni haka jalal?
Jalal ya dawo inda take zaune a kasa ya nuna ta da yatsansa..

Kada ki kara kiran matata da sunan BAIWA..daga yau sunanta..GIWAR AMALE...gara ma ki koyi fadar hakan daga yau...Gimbiya surayya..

Sannan Ko baki lbrn diyar wacece ita ne?
Yayi murmushin gefen lebe..
Diyar sarki take jikanyar sarki..
Ya koma kan gado ya zauna..kuma matar sarki daga yau din nan...
Ya daura kafarsa daya kan daya..
Sannan ya fayyace mata asalin juwairiya..dalla dalla..

Surayya taji kamar ta nutsea wajen..
Zuciyarta tayi wani irin zafi...
Diyar sarkin kano ce dama wannan yarinyar?
Yau ta shiga uku ta lalace,yanzu miye abunyi?ya zatayi?
Muryar jalal ce ta katse mata tunanin da takeyi..
Jitai yace da kakkausar murya..
"zaki iya tafiya............

Jiki a sanyaye surayya ta fice daga dakin...tana tafiya kamar zata fadi dan gaba daya bata ganin gabanta..

_Sorry kunji shiru yau.
Bana dan jin dadi ne.._

_😘to my big fan data aiko min da credit(katin waya),I LOV U so much..
Afrah na godiya sosai..Allah yabar zumunci da kauna..._

Team RUMFAR BAYI
  *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 40
Wattpad @afreey101

*******************

"Washe gari.."

"A babban falon tsohon sarki Abdul-Jabbar duk aka hallara dan damka musu amanar amarya juwairiya..

   Tsohon sarki yayi godiya sosai sannan ya saka ayi masa kiran hansai da laure ...
   Suna shigowa falon a take ya cika alkawarin da ya daukarwa mai martaba sarkin zazzau...wato ya YANTAR dasu kenan..

Zo kuga murna a wajen juwairiya da ma sauran bayi...jakadiya sai taya su murna takeyi...hansai da laure kam ji suke tamkar mafarkine sukeyi...

    Fulani da gimbiya kilishi sunyi murna suma sosai saidai ba karamin rashin bayin nasu zasuyi ba sbd dai an dade tare..

  Lkcn da akazo rakiyar su Ammi..
Hansai ta tabbatar musu da cewa ba zata bar juwairiya ita kadai a masarautar nan ba,zata zauna tare da ita dan ta kula da diyarta..
Laure ma tace itama bazata bar juwairiya ba zasu kula da diyar su sannan zasu fara kasuwanci dan tallafawa rayuwarsu..
  Sosai ammi da gimbiya amina sukaji dadin kalamansu dan dama suma damuwarsu yarda juwairiya zatayi rayuwa acikin masarautar sukeyi
Sukayi masu godiya sosai kafin suka hau hanya..

"A sashen sarauniya JUWAIRIYA kuwa,hanne ce da zainaba zaune suna ta shan firarsu..
Hansai da laure suka shigo suna gu'da sosai suna rawa cike da farin ciki..
Juwairiya tayi dariya dan ta san yarda sukeji yau sun samu YAN'CINSU..

   Rabi ce shiga lekowa tana komawa..
Tunda taji lbrn juwairiyya ce matar da jalal ya aura take ta son tazo ta ganta....
zabba'u dake zaune a bakin kofar ta hangota ta mike tana fadin..
Ki shigo mana rabi..
Rabi ta shigo ta zube gaban juwairiya tana kwasar gaisuwa..
  Juwairiya tayi murmushi tace..
haba rabi nifa ce juwairiyar da kika sani a baya kawarki..
Rabi tace kai amma na tayaki murna sosai ranki ya dade, kingan ki kuwa?kamar ba juwairiyar mu ta RUMFAR BAYI ba..
Gaba dauansu suka kwashe da dariya.......

"Da yamma kuwa sai ga jakadiya ta shigo da sakon kilishi akan a shirya juwairiya dan yau kwanan sashen AMALE zatayi..

Jiki na rawa su hansai suka shiga shiryata..
Wanka sukayi mata cikin madara kamar yarda al'adar su take..
Aka turare ta ga mayuka kamsu sanyin kamshi an shafe ta dasu..
Samira da zainaba suka gyare mata gashinta sai santsi da kamshi yake..
laure kuwa murna takeyi sosai yau zata tsantsara wa diyarta kwalliya ba wannan TABOn a fuskata ..

"Sosai suka gyara juwairiya ta fito amaryar ta kyau kam ba'a mgn..
Dan har daukar ido takeyi😉..

Zainaba,samira da nafisa tare da jakadiya ne suka kai ta har sashen jalal..

Har cikin makeken dakinsa suka shiga.
Mamaki ne ya rufe juwairiya ganin da tayi kamar ba dakin data sani bane,..

Yasha gyara sosai da furenni (flowers) masu kamshi ga fitilu an kunna ko ina ya dau haske..
   Zainaba tace yadai Giwar Amale munyi kokari ko kuwa?

juwairiya ta juyo tana musu kallon mamaki..
Samira da nafisa suka tafa suna dariya..
  Jakadiya ta zaunar da ita kan gadon sannan ta kalli su zainaba tace..
Toh Ku Muje dan nasan duk inda mai martaba yake yana gab da shigowa..

   Zainaba ta rungume juwairiya tana rada mata wani abu a kunne..
Juwairiya ta waro ido tana kai mata dukan wasa...
Da gudu duk suka fice daga dakin suna mata dariya..
Chapter 45 · 0% Book details