← Book details Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 53

Sashe 47

Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Jalal dake tsaye tsaye yana ta ka're ma ta kallo ya zauna a kusa da ita sosai yana fadin..

Da gani dai har kin warware daga gajiyar jiya tunda har kika zauna fira dasu magaji ko?ya karashe mgnr a shagwabe cike da kishi..

juwairiya tayi masa murmushi tace..
naji sauki kam ko kallon shi ta kasa yi..
Jalal na lura da ita dan haka ya jawo ta zuwa jikinsa...yana fadin..

ALLAH yayi miki albarka giwar amale.....dan jiya ba karamin faranta kikayi ba..
Ki fada min duk me kike so nayi miki shi..
ko wacce irin kyauta kike so nayi miki alkawarin zan baki ita a yau din nan..
dan kin cancanci kyauta mai girma daga gareni masoyiyata..

   Juwairiya ta dan dago suna kallon junansu cike da so..
Tace..
Nagode da kulawarka amalena..
Amma nikam bani da wani abu da nake bukata daga gare ka a yanzu..
Soyayyarka kawai ma ta ishe ni..nayi rayuwa me cike da farin ciki..
Jalal har cikin zuciyarsa yaji dadin kalamanta...

Ya shafa gefen fuskarta..yace
KE TA DABAN CE juwairiya shiyasa kike kasheni da soyayyar ki..
Juwairiya ta murmusa cike da farin ciki tace..

Sai dai Amale ina so na baka wata shawara idan ba zaka damu ba..
Jalal ya gyara zamansa yace..
Ina jinki tawan..
juwairiya ta kalleshi cikin ido kafin tace..
Ina so ne ka daina share matan ka sbd ni..!sbd na fara jin wasu maganganu suna fitowa daga zuwana..

Kasan dai yin hakan da kake ba karamin jawo min tsana zayyi ba a wajensu..
Ni kuwa nafi son muyi zaman mutumci dasu..

Jalal ya jinjina kai ,tabbas ta fadi gsky amma shi har cikin zuciyarsa yafi son ta dasu,kodan su ba auren soyayya yayi dasu ba?..

Ya jawo hannunta ya shi rike gam..kafin yace..
InshaAllahu zanyi kokari nayi adalci a gareku duka kinji?..
Ta sakar masa murmushi tace..
nagode sosai Amale ALLAH yaja zamanin ka..

*******************
Bayan kwana biyu..

"A cikin kwanakin nan biyu kacal da juwairiya tayi da jalal ba karamin soyayya da shakuwa ba ce ta shiga tsakanin su..
Yana nuna mata soyayya me tsabta,sannan komai take so yana yi mata shi,baya barin ta cikin tunani ko kadan..
Gashi tana samun kulawar su hansai,kullum sashen ta cikin zaman fira sukeyi,samira da nafisa ma suna shigo mata..
Taje har sashen gimbiya kilishi da fulani diyya ta kai musu gaisuwa,ba karamin murna sukayi dan laure da hansai sai da suka fada duk yarda zatayi ta siye(ex)iyayen gidan nasu..

"""""""Yau sati su daya kenan da aure
A yau ne kuma juwairiya ta gama kwanakin ta na amarci da aka basu ita da jalal..
"sai kuma girkin al'ada da gimbiya kilishi ta sanar mata zatayiwa jalal..
Dan haka suka hau shirye shiryen su..

Hansai da laure ne suka zabar mata duk kalar abincin alfarmar da zatayi wa jalal..
Hanne ce ta shige gaba wajen taimaka mata tare dasu zainaba da samira dan suma cewa sukayi baza'a bar su a baya ba suna tare da ita..

Ko da umayma ta samu wannan lbrn a cikin RUMFAR BAYI ba karamin bakin ciki bane ya lullube ta ba,wai wannan juwairiyar dai da sukayi wa wulakanci suka tozarta suka kore ta daga masarautar nan yanzu itace matar SARKI giwar amale? Ta cije yatsa da saurin ta tayi sashen gimbiya surayya...

Tana shiga ta sanar wa surayya lbrn abincin da juwairiya ke yiwa jalal.
Ta kara fadin..
Yanzu shi kenan ita kadai ce zata samu ya'bawar sarki kenan?

Ba karamin kishi bane ya turnike suryya sai dai babu abunda zata iya yi,ita yanzu ta kanta takeyi,ta samu ciki ta haihu da sarkina..
Ta kalli umaymah cike da rashin mafita tace..
Yanzu wacce hanya ce zamu bi dan mu tarwatsa wannan abincin da take yiwa jalal..
Sai kuma taja tsaki,kai ni duk wannan ma bashi ne gaba na ba,dan maganin malam dai shiru kakeji..

Umayma tayi murmushin mugunta tace..
Ki bar min komai a hannuna ranki ya dade..ni nasan abunda zanyi..

*************
"Sun kammala dukkan abincin da zasuyi ko ina a madafar ya dauki kamshi..
Zainaba ce ta matsa wa juwairiya akan taje tayi wanka ta shirya su zasuje su shirya abincin a sashen jalal..

"Sunje sun shirya komai a sashen na jalal ko ina ya dauki kamshi..
Zainaba ta kalli samira..
Munyi kokari,sukayi murmushin murna kafin dukkannin suka fice da zuwa sashen su...
juwairiya na can sashenta tana shiri hanne na tayata..

  a lkcn ne Umayma ta lallaba cikin sashen na jalal akan surayya ce ta aiko ta..
   Tana shiga falon tayi wajen abincin da sauri ta dauko wani kulli daga cikin zaninta ta bude kwanon miyar tana kokarin barbada maganin a ciki..

"Jakadiya da jalal ne suka shigo sashen...
daga can fa'da suke aiken gimbiya kilishi yaje masa akan ya koma sashensa yaci abincin amaryarsa..
Murna sosai yakeyi zai ci girkin Giwarsa..
Sai sauri yake bazawa,magaji ya kalleshi yace,gsky kayi gaba Amale ni kam bazan iya wannan saurin naka ba..
Jalal ya harare shi,toh a gaida su inna dai..
Magaji yayi gaba yana fadin,zasuji..
Jakadiya tayi murmushi tana jin dadin yarda jalal ke son juwairiyar su..

"Caraf suna shiga sashen sai kuwa sukaci karo da mutumiyar ta ku wato umayma tana ta barbada garin maganin ta a cikin lwanon miya..

  Kallon juna sukayi cike da Al'ajabi. .
Jakadiya ce ta da'ka mata tsawa..
A daburce ta juyo cike da tsananin fargaba...
Jikinta na rawa ta zube a kasa..

Jakadiya tace..
Me kike zubawa a cikin Abincin SARKI...!
Umayma ta shiga girgirza kai..
Wlh tallahi babu abunda na zuba a ciki jakadiya ,kawai dai naje ne na gyara zaman kwanokan..

Jalal ya cike da mamakin waye yake son kashe shi a cikin masarautar sa?ya rasa abun fadi..
    Jakadiya tace karyawata zakiyi?bacin da idanun mu muka ganni ki..kina barbada magani acikin abincin Amale..
Toh Yau taki ta kare!dan kuwa dole ne ki fuskanci hukunci mai tsauri!

Jalal ya dagawa jakadiya hannu sannan ya karasa wajen umaymah yace..
Kince baki zuba komai ba a ciki ko?
Tace wlh mai martaba ni babu abinda na zuba a ciki..

"Juwairiya da hanne ne suka shigo sashen sai tarar da su sukayi a tsatstsaye..
Jakadiya ta matso kusa da juwairiya ta fada mata duk abunda yake faruwa.
A tsorace juwairiya ke kallon umayma..
Ita dama tuni wannan yarinyar batayi mata ba..
Toh menene hujjar ta na saka magani acikin abincin jalal?
Kodai surayya ta aiko ta ne?
Juwairiya ta girgiza kai babu kyau zargi..
Toh me yasa umayma zata zuba wani abu a cikin abincinta?

Jalal ne ya kalli jakadiya yace,kije ki kira min dukka (family)din gidan nan,ni SARKI JALALLUDEEN ina son ganin kowa a nan Yanzu!!!!!

Jakadiya ta fice da sauri...
Juwairiya dake tsaye mamaki yasa ko koda motsi ta kasa yi..
Jalal ya karasa wajen ta ya kamo hannunta..

Hanne ta karasa wajen umaymah ta rike ta gam wai dan kada ta gudu..

    Jalal yaja juwairiya zuwa dakinsa..
Ya kalleta yace..
Ki kwantar da hankalinki zamu gano gsky yanzu inshaAllah..
Juwairiya ta gyada masa kai a sanyaye...kafin tace..

Amale na tambaye ka?
Jalal ya gyada mata kai yana jawota jikinsa..
Me ya hana ka cin abincin surayya a wancan lkcn?
Jalal yadan yi jim irin tunanin nan kafin yace..
Kasa ci nayi kawai sbd tsamin da yayi dayawa..
Juwairiya tadan murmusa tace..
Ai a lkcn dani akayi wannan girkin kuma tabbas na kama wata baiwa tana zuba wani abu a cikin abincin sai dai dana tunkare ta sai ta karyata kamar umayma take karyawata a yanzu...

Jalal yaja lumfashi yace...
Ni na rasa meke damun ku mata wlh..
Yanzu sbd son zuciyarku kun kwanmace ku cutar da mijinku dan kawai kada ya yabi kishiyar ku..?
Dan a take ya tuna abunda ya faru a lkcn khadija,yaci abincinta babu taste amma da magaji yaci cewa yayi masa lafiya kalau abincin yake..

  Juwairiya ta jinjinar da kai..
Jalal ya girgiza kai shima cikin wani irin yanayi..
juwairiya ta yakaci hancin sa..
Ya kalleta..
Ta sakar masa murmushi..tana shagwabe masa fuska..
Ya sumbaci lebenta..
Lkcn ne jakadiya ta shigo ta sanar dasu kowa ya hallara..su kadai ake jira..
juwairiya ta rike hannun jalal,jalal ya lumshe mata ido yace..
Kada ki damu nasan abunda zanyi..

************
Suna fitowa suka tarar da gaba daya an hallara..a cikin a falon..
Tunda ga kan gimbiya kilishi, fulani, hamza,nafisa,samira,zainaba, turaki,hamza,khadija..

Idanuwa akan juwairiya dake bayan jalal har suka samu waje suma suka zauna..
Gimbiya kilishi ta kalli jalal tace..
Amale ya mukaji kira haka daga sama ne?

Fulani tace da fatan dai lafiya dai ko?
Jalal ya kalli surayya da gaba daya jikinta yayi sanyi ganin umayma a wajen kuma da alamu bata da gsky dan kuwa jikinta gaba daya rawa yakeyi...

   jalal yace..
"Kada ku damu dama so nakeyi ne ku taya ni ganin wani abu..
Jakadiya!
Ya kira sunanta..
sannan ya umurce data zuba abincin a cikin plate ta mikawa umayma taci..
   Umayma faduwar gabanta ta tsananta sosai..
Jakadiya tayi yarda sarki yace sannan ta ajiye plate din a gaban umayma tace..
Maza ki ci!

Su dai sauran mutanen wajen kallonsu kawai sukeyi...
dan sun kasa fahimtar abunda ke faruwa a wajen..
Zainaba ce tace..
Haba yaya ya zamu gama wahalar hada maka abincin nan sai ka bawa wata baiwa can taci!

   Hamza yace,shine ai na gani nima kuma duk an tara mu a nan sbd mu ga cin abincinta..
Kilishi ta daka musu tsawa..
Sukayi shiru a tsorace ...

   Umayma ta kurawa abincin dake gabanta ido tana dana sanin zuwa sashen jalal yau din nan da tayi...

Gashi magani ne ta amso daga wajen wani bokanta dan itama Sarki jalal ya kaunaceta ta zama matarsa kamar yarda juwairiya ta zama..
Ta mallake sa ta raba shi da matansa ta zama(apple of his eyes😅)

Tsoro ne ya shige ta sosai dan kuwa boka sai da ya tabbatar mata da cewa idan wani yaci wannan maganin ba sarki jalal ba,toh kuwa tabbas sai ya haukace...!!

Jalal ya kalli hanne..yace
Zauna ki tura mata wannan abincin dan naga bata san menene umarnin sarki ba yanzu..

  Hanne kuwa ta sa hannu ta debo abincin nan me uban yawa..
Jakadiya ta saka wasu kuyangi suka kama umayma suka rirrike ta aka shiga tura mata abincin nan tana hadiye shi da kyal kyal...
Chapter 47 · 0% Book details