← Book details Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 53

Sashe 48

Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     Sai gani sukayi kawai ta fara dariya kamar zararriya..
Ta kalli jalal tace..
Sarkina....bazaka so ni ba nima?
Duk falon hankalinsu ya tashi ciki kuwa harda surayya data gama tsorewa..

   Umayma ta sake yin dariya..tace
Nima fa ina sonka?
Inaso na zama matarka kamar yarda juwairiya tayi kokarin zama itama..
Shiyasa ma naje can wajen boka na amso maganin da zai saka ka ka so ni..
Ka aureni..na zama gimbiyar ka...
Abun sonka!
Na haifa maka ya'ya
Kamar uwar dakina surayya take ta kokarin zuwa wajen malam dan ta samu haihuwa...!

Dum dum dum..
Surayya hankalinta ya mugun tashi..
Yau ta gama yawo..
Kowa yaji tana zuwa wajen malam..

Khadija da juwairiya duk suka mike tsaye cike da al'ajabi..

Fulani ta mike itama tana kallon jakadiya tace,fita ki kirawo fadawa  a dauke mana wannan mahaukaciyar daga nan..

Jalal kansa se dayaji abun kamar wani almara...
Wai baiwarsa ce ta amso magani dan ya sota..
Sannan uwar gidansa har wajen malamai take zuwa..

Kilishi rai a bace take kallon surayya kafin ta wanka mata mari..masu kyau .
Take ta zube kasa tana kuka me ciwo..
Gaba daya falon kallonta sukeyi..

  Surayya na dafe da kuncinta tana hawayen bakin ciki..
ko a mafarki bazata taba tunanin wai baiwarta ta hannun damar ta zata ci amanar ta haka ba......kai mutum ba abun yarda bane ba...kwata kwata

Kilishi tace,wannan ba baiwarki bace?
Tana a karkashin ikon ki shine zaki bari har ta ringa mafarkin kasancewa da Sarki?
Surayya na kuka tace..
Wlh umma bani da saniya da wannan danyen aikin da tayi,ni kaina ban san tana da niyyar mallake min miji ba.

Kilishi tace,ai duk dake din kuke zuwa wajen bokayen..
Surayya tace..
Umma ni wlh nayi nadamar zuwana wajen wannan malamin,kuma wlh ita ke kaini,ku yafeni dan Allah
ta zube kasa tana kukan bakin ciki da nadama...

Dama haka umayma take?shiyasa take ta zuga ta akan hallaka juwairiya da khadija?ma kenan?
Wayyo Ashe itama nan gaba ita zata hallakar ta mallake musu jalal..

Jalal ne ya zo gaban kilishi yace..
Umma ki kwantar da hankalinki,tunda da dai asirin ta ya tuno yanzu,hukunci ne kawai zamuyi mata..

Turaki yace wannan hakane..dan ya zama ishara a wajen Bayi gaba daya..
Wannan ai (abomination )ne....
Kuma raini sosai ne a wajen SARKI..

****************

An kai umayma can rumfar hukunta bayi,an rufe ta acikin kurkuku (dakin duhu)ga hauka tana fama dashi sai surutai takeyi barka tai...
Sarkin dorina ya zane ta tasa tayi lakwas aka jefata cikin dakin aka kulle (oooh ke kuma haka karshen ki yake?)

Wannan al'amarin ba karamin ladabtar da surayya yayi ba..
Kullum tana sashenta zaune shiru tana mamakin irin munafuncin umayma..

Yau dai jalal da kansa ya saka a kira masa ita..
  Tana shigowa dakin nasa yabi ta da kallo duk ta rame tayi baki..
Zama tayi akan kujera tace..
Gani mai marbata ance min kana nemana..
Jalal ya mike ya dawo kusa da ita ya zauna..

Surayya ta dago ta kallesa..
Jalal yace..
Meyasa zaki ringa saka kanki a cikin damuwa ne haka?
Duk fa abunda ya faru ya gama faruwa...se dai Allah ya tsare gaba..

Surayya taji kwalla ta taro mata acikin idonta..
Tace...
Jalal bazaka gane bane..
ka yarda da mutum amma ashe munafukin ka ne(backstabber)...
Duk irin muguntar da take saka ni inayi ashe tana da wata manufar ta ta a akai..
  Jalal ya sauke ajiyar zuciya..
Yanzu dai ai kinyi hankali..ko
Se ki nemi gafarar wadan da kika zuluntar..
Tayi saurin kallonsa..
Yace kwarai kuwa..
Surayya tace..ta zube kasa..
Ka yafe ni sarkina...
Nasan nayi maka laifuka masu yawa..
Sannan...
Ka tayani neman gafarar juwairiya dan Allah..

Jalal yaji dadi har cikin ransa..
Yace..
Zan tayani rukon ta amma inaso kema keje da kanki ki nemi gafarar ta kinji..
Surayya ta gyada kai..zanje..
Jalal ya dagota ya jawo ta jikinsa ya rungume ..
Ta saki lumfashi me nauyi tana jin dadin kasancewa a jikin Sarkin nata..

Love you all
Sorry kwana biyu i hv nt been updating regularly..
Kunsan yarda abun yake sai a hankali. .

Team RUMFAR BAYI
    *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 42
Wattpad @afreey101

_"Fans please ina neman addu'ar ku,October dinnan zan fara exams dina inshaAllah,shi yasa zaku ga ina yanke lbrn dan na gama muku shi a cikin lkc na fara karatun jarabawata.._
_Thanks for all your love.._
_Ina Yin'ku sosai😘_

********************

"Surayya abun duniya ya taro ya fara yi mata yawa..
Girman kai gaba daya ya hana ta zuwa neman gafara a wajen juwairiya..

Gashi kuma yanzu jalal ya dauke mata kafa daga dukkan al'amuran ta ko sashen sa ya daina gayyatar ta..
tun ranar dayayi kiranta tayi masa alkawarin zata je ta nemi gafarar ta har yanzu bai waiwaye ta ba
Sai dai taji yaje wajen khadija da amaryarsa..

     Yau dai fada tayi wa zuciyarta sosai ganin bata da wata mafita..
ga kuma wannan ciwon cikin daya dawo mata kullum dare sai tayi fama dashi tun lkcn da tasha maganin malamin nan a kwanakin baya ta kasa ganewa jikinta gaba daya..
Ga mafarkai barkatai da takeyi,duniya dai tayi mata zafi sosai,taja lumfashi..
Gara naje na nemi gafarar ta wata kila na samu sausaucin abunda nake ji..

***************
"Abun mamaki juwairiya na zaune a sashenta dasu hansai sai ga surayya ta shigo da sabowar baiwar ta...
   Ga babban mamakin su juwairiya sai gani sukayi surayya ta dage sosai wajen neman gafarar ta..

Tayu mamaki sosai amma sai Tace.. babu komai ita ta yafe mata,Allah kansa ma muna masa laifi ya yafe mana balle kuma dan adam?..
Ita dama bata rike ta ba....
Surayya taji dadi sosai,dan gaba daya ma sai ji tayi juwairiyar ta burge ta bata dauki duniyar a bakin komai ba ita kuwa sbd shaidan ya tafi da tunaninta tayi ta wulakanta ta a baya oh?duniya kenan!..

Ai kuwa tun daga ranar sai surayya taji nauyin dake zuciyarta ya ragu sosai,sai dai wannan ciwon ciki da zame mata tilas kullum dare da kyal take samun barci...
Ta rasa mafita gashi yakumbo kanta bata kasar balle ta saka ta ta nemo mata magani..

Bayan wata uku..

******************
A cikin watannin nan da suka gabata ba karami shakuwa da zaman lafiya bane ya shiga a tsakanin  matan sarki jalal ba..

Abun mamaki Yanzu kam surayya sai  shige wa juwairiya takeyi  dan kafin kaganta a sashen khadija toh zaka kanta a sashen juwairiya sau ba adadi duk wani shawara wajenta take zuwa..
sai dai har lkcn ta kasa fadawa kowa abunda take ciki..
duk ta rame ko jalal ya tambaye ta sai tace masa kawai babu komai..kada ya damu..
shi kam ma abun har ya fara basa tsoro dan yanzu ya lura gaba daya surayya bata yarda ta kwana a sashen sa..
Ba kamar da ba da take matsawa sosai sai ya kwana da ita...

"Khadija kam ta maida juwairiya tamkar kawarta dan har dakinta inna (mahaifiyarta)tazo tayi mata kaca kaca akan ta samu lbr a gidansu wai goggo na kawo wa diyarta magunguna....
ba karamin tashin hankali ta shiga ba shine tazo da kanta tayi mata fada mai ratsa jiki..
Sannan ta bata shawarwari wadan da zasu amfane ta a zaman auren ta..

Tun daga lkcn khadija ta saduda sosai ta mayar da juwairiya kawarta..
sai su ringa hadewa a can sashen fulani suna shan firar su dasu zainaba...

"Kamar kullum magaji ne ya shigo cikin masarautar dan amsa kiran sarki jalal...
yana tafe ne yana mamakin neman gaggawar da Amale keyi masa..
Caraf ya hango ta tana tafiya da baiwarta a baya amma da gani hankalin ta gaba daya baya jikin ta..
ganin yarda tazo har ta wuce sa bata ko ma lura dashi ba..

    Juyawa yayi yabi bayanta da sauri yasha gabanta..
Duk da haka ko ganinsa ma batayi ba har sai data ci karo da shi..Bum!

  A tsorace sosai tayi baya zata fadi kasa..
Yayi saurin taro ta ya rike ta gam yana karewa kwayar idonta kallo..
Wani irin abune yaji yana yawo a cikin cikin sa..

Ita kuwa Ji tayi kawai kirjinta na bugawa da sauri da sauri..
Magaji ya kyara mata tsayuwarta sannan yace..
KANWARMU  lafiya?
Zainaba ta danyi kasa da kai tana jin hawaye na sauka akan kuncin ta..

A take hankalin magaji ya tashi yaji gaba daya yana son yaji meke damun ta haka..
Zabba'u ya kalla yace,ki jiramu a can muna zuwa...
Zainaba tayi saurin kallonsa..
Sai gani tayi kawai yaja hannunta yayi gaba da ita...
Haka nan taji ta kasa yi masa mgn sai bin shi da takeyi kawai har suka kawo cikin lumbu...

Ya zaunar da ita akan kujera sannan ya tsare ta da ido yace..
Kanwarmu ki sanar dani damuwarki dan Allah.?
Zainaba ta kura masa ido..
Hakanan taji zuciyarta ta aminta da sanar wa magaji damuwarta,dan kuwa ko juwairiya ta kasa fadawa meke damun ta duk da dai tuni juwairiya ta da'go inda damuwar kawar tata tayo asali..

"Lumfashi taja mai tsayi kafin ta fada masa komai dake tsakanin ta da Mustapha..
Magaji yayi shiru yana nazari a kalla har anyi wata hudu kenan zuwa biyar amma babu wasikar Mustapha? Kuma bai neme ta ba?

Tabbas akwai abunda Mustapha ke boyewa zainaba..
Magaji ya zauna a gefenta yace,ki kwanta da hankalinki kanwarmu na miki alkawari inshaAllahu zuwa gobe zan nemo miki amsoshin tambayoyinki akan dalilin da ya saka Mustapha na daina aiko miki da wasikun sa..

Zainaba ta saki murmushin murna tace nagode yaya magaji..
Yayi murmushin shima..yace
Kada ki damu kanwar mu yanzu dai bari na karasa can fa'da dan Amale ne ma yayi kirana..
Zainaba ta gyada masa kai tace..
nima sashen Giwar amale nayi yanzu..
Suka fito a tare sannan kowannen su yayi hanyarsa...

"Lkcn da zainaba ta shiga sashen na juwairiya sai tarar da gaba daya matan gidan tayi a ciki.
batayi mamaki ba dan dama duk ranar ta juma'a a nan suke wuni,sai kuma asabari suje sashen khadija,ranar lahadi kuwa sashen gimbiya surayya suke....

Juwairiya ta kalli zainaba tace..
Zauna nan kawata kiji...
ta nuna mata waje kusa da ita...
dan a Yau juwairiya tayi alkawarin fayyace wa zainaba abunda ake ciki dangane da mgnr Mustapha..
Cike da lallashi ta fara mgn..
Chapter 48 · 0% Book details