Sashe 51
Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A baya naso naki auren turaki sbd yarda aka hada auren namu ko sanin irin halittar sa fa banyi ba..
Kakata ce (hajiya ta zazzau)ta taimaka min sosai wajen bani shawarwari gashi a yanzu ina alfahari da mijina dan kuwa bani da kamar sa a duniyar nan..
Nafisa ma ta murmusa tace itama..
Ko ni da baba ya sanarwa inna cewa Hamza ne zan aura ba karamin bakin ciki mukayi ba dan kuwa a gari gaba daya babu inda lbrn rashin tarbiyyar sa bai je ba..
Mutane dayawa sun sha zuwa har gida su ba'ta sunan hamza a gaban mu,wai yana bin matan bayi wanene wanene...gulma dai iri iri..
Baba kam ya toshe kunnuwansa..dan alkawari ya daukar wa sarki..
Na hakura nima Akayi auren mu.. gashi yanzu muna tare lfy kuma duk sai na gane cewa wasu maganganun ma da akayi a kansa duk karyar banza ce..
"Surayya ta gyara zamanta..(a wannan lkcn idan ku ka ganta se kun rantse da Allah ba ita bace ba duk ta rame sbd ciwo amma har yau babu wanda ta sanarwa abunda ke damunta)
Tace..
Nikam da abba da ya sanar min mgnr aurena da sarkin daura..
Da farko a gsky ban amince ba dan ina da manema sosai a lkcn..
har sai da jalal yaje har kasar mu muka hadu dashi..
Sannan ne na amince dashi..
Juwairiya tayi murmushi....
Khadija zatayi mgn..
Zainaba da juwairiya suka kwashe da dariya..
Ta watsa musu harara wato dan kunsan sirrina ko?
Juwairiya tace,mun san komai kuwa masoyiyar ya jalal..
Gaba daya suka saka dariya..
****************
Yau juwairiya da kan ta taje har sashen jalal ta same shi ya fito daga wanka kenan..
Kyallen da yake goge jikinsa ta amsa..
Ya sakar mata murmushi yana fadin..
Kamar kin san tunanin ki nakeyi wlh..
Juwairiya na goge masa jikinsa tace..
Ni kaina tunanin ka nakeyi amale amma kasan abunda ya kawo ni yanzu?
Jalal ya girgiza kai yana kura mata ido..
Taja hannunsa suka zauna a gefen gado..
Tace amale ni kuwa ko surayya ta samu fada maka meke damun ta?
Jalal ya girgiza kai,nayi nayi ta fada min amma taki..
har fa kwana a sashena ma ta daina yi se de tazo ta gaishe ni ta tafi abunda ni kaina al'amarin nata yana daure min kai...
ko umma zan sanarwa ta tambayeta oho..mutum sai karewa yakeyi babu wani dalili..
Juwairiya tadan jinjina kai..
Tace...
ni kaina ramar da takeyi ta fara bani tsoro har fa baiwarta na kira na tambaye ta ko surayya bata cin abinci ne sosai amma se ta tabbatar da cewa tanacin abinci...
Na kasa gane daga ina damuwar take har yanzu?
Jalal ya jawo ta jikinsa yana zame dankwalin dake kanta..
Tabbas kin cika me kyakkyawar zuciya juwairiya..
duk abubuwan da surayya tayi miki a baya amma kin damu da ita haka?
Juwairiya ta kwantar da kanta a kirjinsa..
Ni ban rike ta da komai ba amale sbd nasan kishi babu abunda baya haddasawa mutum bare mu mata..
Jalal ya sumbaci goshinta,shiyasa nake son ki sosai...
juwairiya ta dago itama ta sumbaci goshinsa kafin tace..
nima haka Amalena...
Yace kada ki damu dolene mu tuntubi surayya dan ceto rayuwar ta...
duk da dai zan iya cewa abunda ta shukane take girbewa yanzu..
Juwairiya tayi saurin rufe masa baki tana girgiza masa kai..
Yayi dariya yana fadin..
to uwar hakuri..
Nidai ba kamar ki bane dole na fadi gsky abuna...
******
"Magaji ne ya kalli juwairiya da tsabar mamaki..
Ta gyada masa kai tana fadin kaji fa abunda daya faru kenan..
ashe wai har yayi aurensa wannan Mustaphan gashi yanzu ni kaina na kasa lallashin zainaba dan ta saka damuwa sosai a cikin ranta kasan yaudara babu dadi ko kadan..
Magaji ya gyada kai cikin jimami..
ni ma a jiya nayi aike can kasar kanon don a gano min meke faruwa dashi ashe shi gayen har yayi auren sa Allah sarki haka kaddarar su take..
Juwairiya ta gyara zamanta..tace
Shine nake so dan Allah magaji ka taimaka min wajen saka zainaba ta rage wannan damuwar da ta jefa kan ta a ciki..kaga kaima yayanta baza so ta kamu da wata cutar ba ai ko?
Magaji ya jinjinar da kai dan kuwa shima ya tausayawa zainaba sosai..
Yace babu damuwa zan gwada na gani..
Juwairiya tace nagode sosai magaji..
Ya mike yana fadin..
Ai GIWAR AMALE duk abunda kika ce nayi miki ya zama dole nayi miki shi ai.
Juwairiya tayi dariya..
Ai kuwa godiya nake sosai..
*******
Tunda ga wannan lkcn magaji ya zage sosai wajen farantawa zainaba har mamakinsa takeyi..
kullum Shine duk safiya kafin ya shiga fada sai yayi (branching) a sashen ta sun gaisa..
Da yamma ma haka kafin ya tafi gida sai ya leka wajenta sun yi sallama..
Zainaba tun abun yana isar ta har dai ya zamo itama ta fara jiran zuwan nasa a kullum..
Kamar yau jiya har alkawari yayi mata akan zai zo su fita wajen masarauta tare suyi yawo amma taji shi shiru wannan lkcn abunda bai saba ba..
Ta kalli zabba'u tace..
Kije ki duba min a fada ko magaji yana can..
cike da damuwa tayi mgnr..
Zabba'u tace toh ranki ya dade..sannan ta fita da sauri..
Tana fitane sukaci karo da rabi da khadija su kuma zasu shiga sashen.
Zabba'u ta gaishe su tayi gaba abunta..
Su kuwa suka karasa cikin sashen..
Suna shiga zainaba ta mike a tunanin ta ko magajin ne yazo..
Tana Ganin khadija ce sai taja tsaki..
Khadija da cikinta har ya fito sosai tace..
Ai dole ne kiyi min tsaki tunda naji lbrn kin fara mallake min yayana..
Zainaba ta waro ido..
Ni ? yaushe?
Khadija ta kalli rabi sukayi dariya..
Ai duk masarautar nan bayi sun gama dauka soyayya kukeyi da yaya magaji wai kullum ashe se yazo sashen ki...hakane?khadija ta kashe mata ido..
Zainaba taja tsaki,ai dama gulma bata yiwa yan masarautar nan kadan..
Khadija ta kalleta da gefen ido kafin tace..
Ai shikenan dama tunda babu abunda ke tsakanin ku dama wani sako ne ya aiko min na fada miki amma....
Ai zainaba bata san lkcn data riko khadija gaba daya ba tace..
Me ya fada miki dan Allah?
Dama wlh neman sa nakeyi..
Duk yau bai zo ba..
Khadija ta kwashe da dariya..tace
Toh taya kike so marar lafiya yazo nan din ?bacin yana can a kwance..
Zainaba hankalin ta duk ya tashi..
Ta mike babu shiri tace..
Dan Allah khadija kizo muje gidanku mu duba sa..
Khadija tace,lallai ni da wannan cikin? bazan iya wata tafiya ba gsky..kije ke kadai ai masoyinki ne ko?
Zainaba taja tsaki ai dama ke ba mutumci bane ya ishe ki,bari naje samira tayi min rakiyar.
Khadija tace,yarinya wlh gwara ni..
samirar da laulayin cikin zata miki rakiyar?bari ya turaki ya kamaki..
Zainaba taja tsaki tayi gaba abunta da sauri...
"hansai ce ta kalli laure sun saka juwairiya a gaba wai su ala dole dubata sukeyi..
Ace anyi aure har ya kai wata uku kenan amma shiru babu wani lbr?
Juwairiya ta shagwabe fuska tace..
Umma na fada muku ni bani da komai wlh..
Laure tace baki da komai shine duk kika canza cikin yan kwanakin nan..
kece shan mangoro kullum fa sai Amale ya aiko jakadiya da rabin buhu kuma baifi kisha biyar ba..
sai dai mu dau sauran mu kai rumfar cab bayi a shanye shi.
Hansai tace, gashi yanzu bakya cin abincin kirki se kin amayar dashi..
Laure tace,ranar ma du'bu cemin tayi kin aika hanne wai danwake kike son ci..
Juwairiya tayi wiki wiki da ido..
Toh umma dan kawai inason danwake shine inada wani ciki?
Sallamar gimbiya kilishi ce sukaji..
Duk suka mike dan gaishe ta..
Ta kallesu tace..
Me naji kuna fadane?
Kun tsare min diyata da wasu tambayoyin ku..
Ina ruwanku idan ma cikin ne da ita?
(Dan taji komai kafin ta shigo dama jakadiya ce takai mata lbrn kuma tabbas ta gano juwairiya ciki ne da ita,ba karamin murna tayi ba )..
juwairiya ta rufe fuskarta cike da kunyar kilishi..
Hansai da laure sukayi murmushin murna..
Kilishi tace,yanzu dai ina so kulawar ku a gareta ta linku dan yanzu muke bukatar kulawar ko? Ta kalli juwairiya..dake ta sunne kai..
Hansai tace,ai gimbiya kada ma ki damu da wannan dan ya zama dolen mune mu kula da diyarmu.
Kilishi tayi murmushi tace toh mun gode sosai..
***********
Labari ne yaje wa SARKI JALAL har fa'da..
Dan dama kowa burinsa yaje yayi masa wannan albishir din ko zai samu wani abu daga wajen sa na tukwici...
Wayyo zo kuga murna kamar yayi mai..!dadi sosai ya mamaye zuciyarsa..
Ya kasa ma yarda wai juwairiyar sa ce keda cikin sa a jikinta?..
Ya mike babu shiri yayi waje..
Ko Kafin ya karasa sashenta sai da yayi kyauta har babu adadi duk wanda ya hadu dashi se ya bashi wani daga jikinsa...
Yana shiga sashen nata ya tarar da hanne a falon..
Tace masa ai uwar dakin nata na cikin uwar daki..
Ciki ya shige cike da murnarsa..
A lkcn juwairiya na tsaye ne tana daura zaninta..
Sai ji tayi kawai anyi sama da ita..
Jalal na dariya cike da farin ciki marar misaltuwa ya shiga juyawa da ita yana ta shi mata albarka..
Sosai take dariya itama tana rokon sa daya sauke ta kasa..
Jalal ya sauke ta kan gado yana kamo hannayenta duka biyun ya rike gam..
Yace..
Giwata na gode kwarai da gaske..
Juwairiya ta lumshe masa ido tace..
Amale ai Allah ne abun godiya bani ba ..
Jalal yaja lumfashi ya daga kansa sama yace..
Ya Allah na gode maka da wannan babbar kyautar da kayi mana,Allah kayi wa dan mu albarka ka kuma sauki matata lafiya..
Juwairiya na murmushi ta amsa da amin..
Jalal yace,wlh bakiji irin farin ciki da nake ciki bane yanzu..
Khadija zata haihu haka ma kema a cikin wannan shekarar zan zama baban yara biyu....
Juwairiya ta dan kamo hannunsa..tace
Amale ka kuwa samu lkcn tambayar surayya meke damunta?
Jalal ya girgiza mata kai abubuwa ne dayawa a kaina juwairiya..
Amma zan saka hamza ya dauko min me magani zuwa gobe se a duba ta..