← Book details Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 53

Sashe 26

Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tayi saurin gaishe shi..
Ya amsa mata a sake yana fadin..
    Kinyi mamakin kiran da nayi miki ko?
juwairiya ta gyada kai..
Yace dama ina so ne na baki wata yar kyauta..
Juwairiya ta dago ta kallesa..
Ya nuna mata bishiyar yace na baki wannan bishiyar mangoron...
Juwairiya ta kwashe da dariya.
Magaji yabi ta da kallo yana jin sa a wani a irin nishadi...

Kafin yace,ba wasa nakeyi ba fa?
Kinga wannan bishiyar duk lkcn(season) din mangoro toh sai kin samu wanda yafi na ko ina zaki a jikinta..kuma a yarda na lura ke mayyar mangoro ce ko?

Juwairiya tayi murmushi tace toh nagode ranka ya dade..
Magaji ya samu waje ya zauna..
Sannan ya nuna mata waje itama ta zauna a can nesa dashi..

Magaji yaja lumfashi kafin yace, na san rayuwar bauta acikin wannan masarautar ba karamin wahala ne da ita ba,amma zuciyata na son taji dan tarihin ki ko kadan ne..
Duk da nasan a tarihin bayin dake cikin masarautar nan kece kadai aka taba haifa a cikin RUMFAR BAYI...

  Juwairiya taja lumfashi, hakane ranka shi dade, amma ni rayuwata babu wani labarin da zan iya bada shi.. wanda baka sani ba..
Tun ina shekara goma na fara bauta..
   Magaji yaji tausayinta har cikin zuciyarsa..
Ya jinjina kai...(yana tunani a zuciyarsa,kodai ya fada mata sirrin dake zuciyarsa ne?sai kuma wata zuciyar ta hane sa)
Ya kalle ta yace..
zaki iya tafiya nagode da lkcn da kika banu..
juwairiya ta mike kawai tayi masa godiya kafin ta fice..

*******************
"Washe gari..

"Umayma ce ta kalli surayya,Allah ya kara miki yawan rai..
ina tunanin kawai yakumbo ta bamu damar zuwa wajen bokan ta,
tunda dai har wata daya ya shude babu wani alamun ciki a tattare dake..
kuma kar na fara jin kusun kusun daga bayin dake sashen gimbiya kilishi,wai ta fara mgn a rashin haihuwar ku har wannan lkcn..

Surayya cike da takaici tace,nima ina wannan tunanin umayma..kema kin sani bazan taba bari wata ta haifawa jalal yaron da zaya gaje shi ba sai ni!ta nuna kanta!ni surayya! Shiyasa har gobe bazan bar ciyar da khadija wannan maganin ba har sai na samu MAGAJIN'SARKI..

Taja lumfashi tace ya mgnr wannan yarinyar?
Ina fata kin dasa mana wacce zata saka musu ido dan ni wlh zuciyata bata kwanta da aikin da takeyi a sashen sarkina ba..
Umayma tace kada ki damu...koma miye sirrin da take boyewa muna daf da sanin sa..

Surayya zatayi mgn kenan sai ji sukayi ana sanar da shigowar khadija..
Umayma tace, ko wane gulmar ta kawo ta kuma?

"Cikin takon girma khadija ta shigo cikin falo tare da rabi a bayanta..
Surayya tayi murmushin yake,ah ah amarya da kanta da sassafe haka.?

  Khadija tayi murmushi,gani nayi kamar zumuncin dake tsakanin mu ya fara rauni..
Surayya ta tabe baki,zumunci?ta maimaita..
Khadija tace,daga sashen umma nake yanzu,tace nazo wajenki dan mu tautauna akan shirye shiryen auren su ya hamza da ya turaki..
Surayya ta gyara zaman ta,na dauka ai su umman ne zasuyi komai..
Khadija ta girgiza kai,mu a nan masarautar matan sarkine ke gudunar da duk shirye shiryen daya danganci gidan sarauta..
Surayya ta jinjina kai..

***************
"Ina jinki....
ina kika je jiya da safe?
juwairiya ta kalli jalal daya tsare ta da tambayoyi akan jiya daya tashi bai ganta ba..
  Ta dan sauke kai kasa tace...
Magaji ne yayi kirana..
Jalal ya daure fuska sannan bai ce mata komai ba kawai ya gama shirinsa yayi gaba..
Juwairiya ta saki murmushi,lallai yarima akwai shegen miskilanci..
Har ta mike dan ci gaba da gyaranta taga ya sake dawowa ya dauki hular sa ya sake ficewa..

*****************
"Biki ya matso ana ta faman shirye shirye masarautar ta cika tam da mutane sosaidaga kowane yanki na arewa..

"A yau ranar juma'a ne kuma Aka daura auren HAMZA DA NAFISA sai kuma TURAKI DA SAMIRA..

  "Yarima gaba daya ranar bai samu zauna ba ko kadan ba,dan Fada ma ba karamin cika tayi tba ab..bashi da ikon fita ko nan da  can,sai magaji dake ta kokarin ganin ya taimakawa amininsa nasa..

"A can cikin gida kuwa,matan sarki ne ke ta hidima da jama'a sai ka rantse da Allah kansu a hade yake,amma kowacce tana yi ne kawai dan burge sarki jalal da kuma gimbiya kilishi mahaifiyar sa..

"Amaryar hamza aka fara kawowa nafisa direct sashen gimbiya kilishi akayi da ita..
SAMIRA kuwa matar turaki sai yamma likis suka iso kasancewar daga kasar zazzau suka taho..
Ita kam a sasheen fulani diyya aka ajiye ta...

"Da daddare mai martaba sarki jalal ya shirya musu liyafa ta gani ta fada..
Gimbiya kilishi ta bukaci surayya da khadija dasu zaunaa wajen shirya nafisa..
     Surayya ta kalli kayan dake hannun khadija tana yatsine fuska,kina nufin wannan kayan zata saka?
Khadija tace eh mana..
Surayya taja tsaki sannan ta fito da wasu kayan tace,wannan na tanadar mata dan haka su zata saka bana son wani feleke..
Nan fada ya kaure a tsakanin su..
Nafisa kuwa sai kallon su takeyi cike da mamakin kishi irin nasu..

***************
"Jalal daga fa'da sashen baki suka nufa shi dasu magaji..
A nan ya tarar da yan uwan SAMIRA samari da manyansu daga kasar zazzau..

Khaleed ne kawai ya sani a cikin su..
Dan haka dashi ya fara gaisawa..haka nan kuma ya samu kansa da tambayar khaleed din ko ina AMMI?

Khaleed yayi dan murmushi,ai ka san yan mata kusan biyar aka daurawa aure a yau din,toh AMMI na can kasar bauchi sunje kai diyar wajen ya ladan..
Jalal ya gyada kai sannan ya karasa ciki ya shiga gaisawa da sauran....

"""A gajiye sosai ya shiga sashensa dan shiryawa kafin lkcn liyafar yayi..
Dakinsa ya shige Yayi wanka ya shirya cikin kayan sa da sukaji ado sosai,ga rawani na alfarma yasha..

Har sun fito tare da angona ya kalle su yace ina zuwa...
Komawa yayi cikin sashen nasa ya dauko wata sarka ta zinari irin chain dinnan,ya zura a cikin aljihunsa sannan ya fice..

"Zainaba ce ta saka ayi mata kiran juwairiya dan su shirya samira..
Juwairiya cike da murna ta shiga dakin na fulani..
Samira na zaune a gefen gado ta lullube kanta da babban mayafi..

Zainaba na ganin juwairiya tace,wai ina kika shige ne juwairiya ?
kinsan kuma dolene na bukace ki a kusa dani yau..
Juwairiya tayi murmushi tace..
kiyi hkr ranki ya dade ina can RUMFAR BAYI ne muna taimakawa a cikin madafa..
Zainaba ta jinjina kai,sanann ta kalli samira..tace..
Amaryar yaya bude fuskar taki mana mu gani?
Ko mu kike jiwa kunyar?

Samira a kunyace ta yaye mayafin..
Sai cin karo tayi da fuskar juwairiya..
Ware ido tayi tana kallonta kafin tace ,tana kama da AMMI wlh,ta fada tana nuna juwairiya, kallon rashin fahimta sukayi mata..
Samira ta shiga kallon tufafin dake jikin juwairiya, a take ta fahimci baiwa ce..
Mamaki ne ya kamata dan haka ta ja bakin ta tayi shiru...

"Cikin dan kankanin lkc zainaba, juwairiya da kuma laure suka shirya samira cikin kayan alfarma tayi kyau mutuka..

"Zainaba komawa tayi sashen ta ta shirya sannan ta bawa juwairiya kaya itama tace taje ta canza hakama zabba'u..

        Juwairiya komawa tayi rumfar bayi dan shiryowa..
  Lkcn da zata fito sai ta tarar kamar anyi shara a masarautar babu kowa duk an hallara acan wajen liyafar..
      Cikin sauri itama ta karasa wajen..
Angwaye da matansu ba karamin kyau suka kayi ba..

  Idanuwanta ne suka shiga neman inda zaga yarima..
Can ta hango sa tare da magaji suna mgn ta kura masa ido..
Kamar ance ya juyo sai hada ido sukayi da ita..
Murmushi ya sakar mata a fakaice..sanan da idanuwansa yayi mata signal akan ta bi bayanshi..kafin ya fara tafiya cikin takon kasaitarsa..

juwairiya ta kalli su umayma da rabi dake gefen ta tace dasu ina zuwa kafin tayi gaba...
Khaleed dake gaisawa dasu khadija ya hango ta kamar daga sama..
Kallo ya bita dashi,gefen fuskar ta kawai ya iya hangowa amma yaga dan kaminta da Ammi,da saurinsa ya sake binta da kallon tana kokarin wuce su sai hango dayan gefen fuskarta ta yayi a kone,nazari ya shiga yi,wacece ita????????

****
Juwairiya na tafiya...
Umayma ta bi bayanta da kallon zargi wata zuciyar tace mata ta bi ta kawai,ai da saurinta ta shiga bin bayan juwairiya..

Can nesa da inda ake liyafar jalal yaja ya tsaya yana juyowa dan ganin ko ta taho....

Juwairiya ta karaso wajensa da sauri tana mamakin irin kyaun da yayi yau se kace shine angon..
  Jalal yace wannan kallonfa?
Ko nayi miki kyau ne?

Juwairiya tayi saurin dukar da kai..
Jalal ya mika mata sarkar daya fito da ita daga cikin aljihunsa..
Amsa..
Ta bi sarkar da kallo sannan ta kalleshi..tace..
Ranka shi dade me yasa zaka bawa baiwa kamar ni irin wannan kyautar..
Ai bayi basu da ikon saka duk abunda ya danganci kwalliya...

Jalal yaji wani iri har cikin zuciyarsa. .....
Yana son ya sanar da ita sirrin dake cikin zuciyarsa amma yana ganin kamar lkc bayyi ba....
Sai ya tuna lkcn da ya fahimci cewa SONTA YAKEYI....

"_Suna zaune ne tare da magaji a cikin lambu da wani yammaci.._
  _Ya kalli magaji yana fadin..
Abokina dan Allah na tambaye ka mana?_
_Magaji ya ajiye tufar(apple)da yake ci ya maida hankalinsa wajensa..yace
Ina jinka AMALE fadi naji.._

_Jalal yaja lumfashi kafin yace..
Idan kamar haka mutum ya damu da wata sosai kuma a kullum zuciyarsa na muradin yaganta yana begen ta a kowane lkc...yana jin dadin mgn da ita,yana kaunar kasancewa da ita,yana tunaninta,amma ya kasa gane matsayin da zaya ajiyeta a ciki zu.....
Magaji ne ya kwashe da dariya sosai..
Jalal ya kallo shi yace meye haka?
Magaji yace,meyasa kawai ba zai gene cewa SON TA yake ba?.._

_Ko wanene shi dai bako ne a cikin soyayya nake gani, dan duk abubuwan da ka fada yanzu soyayya kawai ce ke kawo su..ya dai sake tunani,..._

_Dan ba karamin SON TA yakeyi ba,kuma ya kamata yayi gaggawar sanar da itama.._
_Jalal yabi shi da kallo kafin yace, idan kuma yafi karfin ta fa?ina nufin(level)dinsu ba daya bane.._
  _Magaji ya gyara zamansa,ni a ganina indai yana sonta har haka duk wani matsayi ba wani abun damuwa bane ,idan ya aureta ai duk sun zama daya ko?
Jalal ya jinjina kai yana nazarin kalaman magaji..."_
Chapter 26 · 0% Book details