← Book details Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 53

Sashe 19

Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Can kusa da rabi ta tsaya,sai ga umayma tazo taja layi kusa da ita,kallonta kawai juwairiya tayi batace komai ba,umayma kuwa murmushi tayi tace,zanso mu zama kawaye idan bazaki damu ba?
Juwairiya tadan yi murmushi tace,ai duk baiwar dake cikin Rumfar bayi yar uwa na dauke ta,umayma ta danyi yake tana ki'tsa wani abu acikin zuciyarta..

Na Afrah bhai
[9/18, 3:19 PM] Aysha Galadima:         *RUMFAR BAYI*
    (A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 19
Wattpad  @afreey101

*wannan naki ne didi @Fertyma Zarah*

**********
"An sha shagali sosai har kusan tara na dare kafin taron ya watse..
    Sarki jalal ne ya shiga babban turakar sa (sashen sa) inda aka canzawa tsari daga tsarin na mahaifinsa wato tsohon sarki kenan..

    " Jakadiya ce ta shigo da kuyangi har cikin makeken dakinsa,ta fada musu yarda zasu hada mishi ruwan wanka da sauran hidimarsa,kuyangi biyu ne suka shige cikin dakin suka gyara shi tsab dan kwanar amarya..

A can wajen khadija amarya kuwa,bayan ta dawo daga taro a gajiyenta, gimbiya kilishi ce ta aika mata da hansai da kuma sabowar baiwarta wato rabi, nan hansai ta shiga nunawa rabi yarda zata kula da uwar dakin nata,rabi sai washe baki akeyi tana murnar samun karin girman da tayi..

  An gama shirya khadija tsab cikin kaya na gani na fada.
suna shirin fitane dan zuwa kai ta can turakar sarki jalal sai ga surayya tare da umayma sun shigo cikin sashen..

   Wajen zama rabi ta nuna musu,sannan ta dawo kusa da khadija dake ta jin haushin tsaida su da akayi ta zauna..
   Surayya ce tace, su amarya an sha kamshi,dama nazo ne dan nima na bada tawa gudunmawar tunda dai ban samu lokacin bayar wa ba ko..

  Umayma ce ta ajiye tiren dake hannunta wanda dashi ne suka shigo.
surayya tadan yi murmushi kafin nan ta sake cewa,
wani tsumi ne dama da aka kawo min shi daga kasar Cameroon, nayi amfani dashi kuma na yaba sosai,tunda dai ba karamin rikita sarkina yayi ba a lkcn,ta karashe mgnr cike da kissa..

   Khadija taji wani abu ya tsaya mata a wuya,sarkinta?ya rikice?lallai ma wannan matar..
  Tadan dago kai tana murmushin yake kafin nan tace a takaice ,toh nagode..ta shiga kokarin mikewa..

Umayma ce tayi saurin fadin,ah ah gimbiya khadija ai  kamata yayi ki dan nuna karamci,ta shiga zuba tsumin a kofi..
Surayya ta amsa kofin ta mikawa khadija,kidan sha ko kadan ne na tabbatar miki gobe se kin gode mini..
    Khadija tadan kalli rabi,rabi tayi mana alama da kada tasha,khadija tadan tabe baki..

  Jakadiya ce ta rangwada sallama tana sake nanata musu sarki jalal na jiran amaryar sa..
Khadija data ka'gu sosai data tafi wajen rabin ranta...
cikin sauri da jawar jiki ta amsa kofin ta kafa kai ta shanye shi tass tana nunawa su surayya cikin kofin (irin am done zaku iya tafiya).

Surayya tayi murmushin murna,yauwa ko kefa kinga nima se naji dadi ai,rabi ce ta kamo hannun khadija sukayi gaba abunsu..
Umayma da surayya suka kalli juna suna murmushin mugunta  cike da gamsuwa..

**************
"A wajen Jalal kuwa yayi wankansa ya saka kaya masu saukin gaske,se kamshi yakeyi ..

  Yana zaune a saman darduma ta alfarma yaji sallamar khadija daga can falo..
  Bai motsa daga inda yake  ba har ta shigo dakin cike da yangarta ta sauke idanunta akan sa..
Wani irin kyau da kwarjini yayi mata har bata san lkcn da ta saki murmushi ba tana wani kafe shi da ido..

  'Idan kin gama karemin kallon se kije ki kwanta"

  Khadija tadan waro ido kunya duk ta lullube ta.
  Jalal ya mike cike da kasaitarsa ya juya mata baya..sai ji kawai yayi an rungumo shi ta bayan..

Khadija ta kwantar da kanta a bayansa tana fadin..
"Haba ya jalal meyasa kake bawa zuciyata wahala ne?kasan fa yarda na damu dakai tun muna yara...amma se ka ringa wani share ni..ta karashe mgnr a shagwabe..

Yarima yaji jikinsa yayi sanyi,idan har yace bai san khadija ta mutu a kansa ba toh karya yakeyi wa kansa..

    Lumfashi yaja sannan ya kamo  hannunta ya maido da ita gabansa yana kallon fuskarta har kwalla sun fara cikowa a cikin idanunta..

   "Meyasa kike Sona?
Khadija tayi saurin kallonsa,dama ya san tana sonsa kenan?
Meyasa?
Ya sake maimaita tambayar..
Khadija ta shagwabe fuska,nima ban sani ba ai,kawai dai komai naka wlh burgeni yakeyi tun bansan cewa sonka nake ba har na girma na fahimci hakan..

Yarima yaja lumfashi,sannan a cikin zuciyarsa yake ganin wautar tambayar da yayi mata,juwairiya ce ta fado masa a rai,meyasa ya damu ita sosai?shima dai kamar yarda khadija ta fada,bai sani ba..

    Jin khadija a jikinsa ne yasa ya dawo daga duniyar tunaninsa..
Rungume sa tayi tsam...
A take yaji wani irin yanayi a gaba daya jikinsa..
Ya lumshe ido ya bude su ahankali ,kafin ya dauke ta cak ya ajiye a kan gadon dake gabansa..

**************
"Juye juye kawai takeyi a kan taburma,ta rasa meke damunta, duk yarda taso tunanin jalal ya fita daga cikin kwakwal'warta kasawa tayi..

Mikewa tayi zaune tana kallon gefen da ummanta take a kwance,sai sharar barcinta takeyi..
   Fita tayi daga cikin dakin dan zuwa ta dauro alwala...tayi nafila ko zata samu nutsuwa.

   Motsi taji daga can cikin madafa,mamaki ne ya kamata dan kuwa duk mutanen dake cikin rumfar bayi a wannan lkcn sunyi barci..
   A dan tsorace ta karasa kofar madafar tana leke..

   Ba'kin ta kawai yasa ta gane wacece a wajen ,duk da kuwa babu wani isasshen haske a wajen..
Umayma ta furta a hankali me takeyi a wannan lkcn?

Gani tayi umaymar ta juye wani abu daga cikin jug,tasa ruwa da yawan gaske ta wanke jug din tas,sannan tayi murmushi me ma'anoni dayawa...
    Tana kokarin juyowa juwairiya tayi saurin barin wajen,tana tunanin wat is umayma up to?

***********
"Da safe jakadiya ce ta shigo dakin jalal bayan fitarsa.
Can ta hango khadija a kwance jikinta duk yayi tsami ga zazzabi me zafi ya rufe ta..

  Subhanallahi ranki ya dade!
Nan jakadiya ta shiga kiran kuyangi dan su taimaka mata..
Sai da aka kimtsa ta sannan jakadiya tace ko a kai ki sashen gimbiya kilishi ne dan ki dan samu shan magani?
Khadija ta girgiza kai,ah ah sashen fulani zani..
Jakadiya ta kalli rabi tace,taimaka mata kuje..

"Fulani diyya ce da kanta ta shiga kula da khadija,labari kuwa yaje har kunne kilishi, haushin khadija ne ya kamata sosai,wai tana so ta jawo mata raini.

"Juwairiya tare da zainaba ne suka shiga sashen fulani dan ganin jikin khadija kamar yarda lbrn ke ta yawo acikin masarautar.
   A daki suka tarar  da ita kwaryar magani a hannunta sai yatsine fuska take rabi na ta lallashinta tasha..

Zainaba ta zauna a kusa da ita..
Matar sarki jalal na zata ai ke jaruma ce ..
Khadija ta banka mata harara..
Juwairiya kuwa sai faman kallon khadija take tana jin wani abu yana tsirga mata acikin zuciyarta..

Khadija ta ware ido tana dafe kirjinta tace,wayyo Allah na yau na shiga uku?
,zainaba tace me ya faru kuma yanzu sarkin ra'ki?khadija ta matso kadan tayi mata a kunne (akan she forgot her underwears a dakin jalal)
Zainaba tayi kasa da murya,kada ki damu,ai su jakadiya zasu dauke miki komai,khadija ta girgiza kai nidai bana son ne wannan matar tasa taje ta gani na jawa kaina wani sabon rainin a banza..
Khadija ta jawo rabi tana mata rada akunne cikin mgn kasa kasa tace,ki koma sashen ya jalal a dakinsa ki dauko min wata bakar laya dana manta acan,kada ki kuskura wani ya gani!gyada kai rabi tayi sannan ta mike zata fita..
   "Zainaba ce ta kalli gefen da juwairiya take tace,juwairiya kuje tare da rabi sashen ya jalal din....

Khadija ta dan harare ta ki bari rabin taje ita kadai mana?
Zainaba tace,ah ah ai juwairiya tafi ta sanin jakadiya ,khadija ta tabe baki..sannan da ido tayi wa rabi gargadi...
juwairiya kam bama son zuwan take ba dan wani abu take ji yana mata yawo a makoshinta,
Ta kalli rabi tace muje,rabi tace toh sannan tabi bayanta suka fice.

khadija ta dafe kirjinta tana addu'ar Allah yasa jalal bai ga wannan layar data fadi daga jikinta ba jiya ,goggonta ce ta bata ita akan idan ta kwana dashi da wannan layar ajikinta toh tabbas zata samu waje acikin zuciyar jalal,ko innarta ma bata san sunyi wannan sirrin ba..

***********

""Suna shiga makeken sashen na sarki jalal suka tarar da jakadiya tare da wasu kuyangi suna ta hidimar su.

Juwairiya ta karasa wajen jakadiya ta gaishe da ita,jakadiya tace,meya kawo ku nan juwairiya,da fatan dai komai lfy ? kunsan fa baku da ikon shigowa turakar sarki ba tare da wani babban dalili ba..

Rabi ce tace, uwar dakina ce gimbiya khadija ta aiko mu daukar wani sako aciki data manta..
Jakadiya ta jinjina kai,sannan ta kira wata kuyanga tace takai su dakin jalal su duba amma kada su dade..

"Tunda suka saka kafa a cikin falon juwairiya ke kallon ikon Allah,lallai an kashe duniya me tarin yawa a wajen nan,wani ado ne na zinari ta hango daya mutukar burke ta sosai..

     Rabi kam da sauri ta shige dakin tana waiwayen juwairiya, can ta hango ta kamar an dasa ta a gaban wannan frame din,ta sauke ajiyar zuciya sannan ta shige da saurinta ta shiga neman inda zataga layar..

  Ita kam juwairiya tana nan a tsaye babu kowa a cikin falon sai ita kadai dan kuyangar data shigo dasu ma ta fice..
  Wata kofa ta hango a bude iska nata kadata..
   Hakanan take son ganin ina ne wajen shi kuma,tasan dai daga yau bazata taba sake samun damar shigowa nan din ba..
   A hankali ta karasa wajen kofar tana leke.....

      Bude baki tayi da idanu gaba daya cikin tsananin burge ta da wajen yayi tace,mashaAllah....

    "Dan karamin wajen shakatawa ne da aka gyara shi da flowers da fruits iri iri sannan aka saka mishi kujerar lilo,yayi mutukar kayatuwa..
      Sbd yarda ya tafi da zuciyar juwairiya bata ma san lkcn da ta saka kafa ciki ba tana karewa wajen kallo cike da ban sha'awa..
Chapter 19 · 0% Book details