← Book details Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 53

Sashe 23

Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Surayya taji gabanta ya fadi tace a rikice me kike nufi jalal?
Yasa hannu ya ture plate din daga gabansa... ya tura mata shi yace..
Dandana kiji ma kanki mana!wannan ai muguntar banza ce..

Surayya hannu na rawa ta dauki tsokali ta soma dandana abincin..
   Da sauri ta zubar dana bakinta..tace..na shiga uku!
Meye haka?wallahi ba haka abincina yake ba..ta fadi kamar zata rusa kuka..
  Jalal yaja tsaki hade da mikewa cike da haushi ya fice daga sashen abunsa..

************
"Juwairiya gaba daya ta kasa tsaye ta kasa tzaune,tunanin halin da yarima yake ciki kawai takeyi,ta kagu duhu ya fara taje ta same sa a inda yace su hadu..

laure ce ta kawo mata kwanon abincinta da bataci ba.
kewai ban gane miki ba?tunda kika dawo kike a nan zaune kin buga uban tagumi sai kace wacce ta ka'yar da uwar miji..lafiya ?

Juwairiya ta girgirza kai tace,babu komai goggo laure amma ni na koshi da wannan abincin ki koma dashi..
Laure ta ajiye kwanon hannunta,nasan dai bakici komai ba dan haka ki ajiye zuwa anjima idan kin gama muraja'ar,tana gama fadar haka ta fice..
Juwairiya ta mike itama tana kallon jikinta,a haka zataje wajen yariman?taji zuciyarta ta fada ..
Wasu kayanta masu dan haske ta canza sannan ta lallaba tayi waje da gudu..

**************
"Tunda ta fito Gaba daya tunani takeyi,Allah dai yasa babu wani abunda ya faru da shi..

    Tana isa wajen ta samu wani dutse ta zaune akai tana buga uban tagumi..
Daga kai tayi ta kalli sama,garin yayi duhu amma hasken taurari ya kayatar da daren..

   Ta dade a wajen zaune,zuciyarta na gargadinta ko dai yarima bazai samu zuwa bane?wata kilan ma ya manta da haduwar tasu a nan..
    Ta mike a sanyaye, dama mai take tunani wacece ita da yarima zai zo ya same ta,wata zuciyar tace mata,toh ai shine ya bukaci ku hadun?
Mtsww....(whatever )

***************
"Koda ya fito daga sashen sa da hamza sukaci karo a hanya..
Hamza ya bishi da kallon tuhuma yace..
Yaya sai ina ne haka da daren nan?gashi babu wani bafade a tare dakai..
Jalal yadan dafa kafadarsa,hamza kenan kasan fa ko sarki yana son sirri..shiyasa ban gayyaci kowa a fitar tawa ba..

  hamza ya mishi kallon rashin fahimta..
Jalal ya murmusa..
Hamza..ya kwashe da dariya yana cewa ooooh sai yanzu na gane ai yaya,amma kasan dai duk inda zaka wuce a masarautar nan indai a haka kake... (ya nuna shigar alfarmar dake jikin yarima) to dole ne mutane su shaida ka.. kaga ba wani batun sirri kenan...

Jalal ya jinjina kai ganin lkcn da dan sauran haske ko ina zai wuce sai an lura dashi..

Hamza yace,kana son taimako na?
Jalal yace,wane irin taimako zakayi min kanina?
Hamza yace duk da bansan ina ne wajen sirrin naka ba amma ina tunanin da ka batar da kama zai fi..

Jalal yadan kwabe fuska,ni da masarauta ta ina matsayin sarki sai na batar kamanni na dan na samu sirri..
Hamza yayi dariya,ka yarda dani yaya..
Jalal ya danyi shiru,baya son kowa yasan inda zayaje,kuma da gskyr hamza, idan ya fita a haka akwai yan gulma da kai rohoto..
Na amince...
Hamza yace toh muje..
Sashen hamza suka shiga..
Hamza ya saka wani bawansa da ya kawo masa kaya irin na low class dinnan,ya mikawa jalal gashi ka saka..
Jalal ya yatsine fuska ni zan saka wannan?(ya yastine fuska yana kallon kayan dake hannun hamza)

Hamza ya zauna a gefensa,haba yaya ai a hakane kawai zaka iya fita cikin masarautar nan babu wanda zai gane ka..
Jalal ya jinjina kai kafin yadan ja tsaki ya amsa yaje ya saka..
Yana fitowa hamza ya kwashe da dariya..
Jalal ya harare shi..kafin ya fice abunsa cikin sauri yana jin haushin tsaida shi da hamza yayi..

*******************
"Juwairiya kuwa har ta fara tafiya abunta dan komawa rumfar bayi sbd dai ta cire rai da zuwan nasa...

   Jalal kuwa na can sai buga sauri yakeyi..(duk inda wuce se yaga kamar za'a gane shi,amma ga mamakinsa ko kallo bai ishe kowa ba).

Yana karasowa wajen ya hango ta tana tafiya zata bar wajen..
Karasawa yayi zuwa bayanta yace..

"Ji mana yan mata...."

    Juwairiya ta juyo da sauri tana kare masa kallo daga sama har kasansa..
     Waro ido tayi cikin mamaki tace..
Mai martaba kai ne haka?

Jalal ya samu kansa da murmusawa..
  Juwairiya tayi kasake tana kallonsa..

Yace mu karasa can..
da ina zaki tafi?
Juwairiya tayi kasa da kai tace..
na zata ai ka fasa zuwa ne..
   Jalal ya samu waje ya zauna..
juwairiya ta kura masa ido tana godewa Allah da babu abunda ya same sa..

   "se Ki zauna idan kin gama tunanin.."

juwairiya tayi dan firgigit..ta nemi waje itama ta zauna,gaba daya dadi ya lullube ta,wai ita juwairiya ce zaune da sarki guda a waje daya kuma a kadaice...
   Jalal kallonta kawai yakeyi..
Shiru har kusan minti talati bai ce komai ba..

juwairiya ta dago ta kallesa,gani tayi ita yake kallo,tace,mai martaba kace na same a nan..?
Jalal ya gyada kai...jitai yace..

Ina so na sake baki wani umarnin ne...
Juwairiya tace ina jinka..ranka shi dade..
Jalal ya gyara zamansa..kafin yace..

Akan tambayar da kikayi min ne jiya na son sanin dalilina na kyautata miki da nakeyi..
Juwairiya taji gabanta ya hau faduwa..
Yaci gaba..
A gaskiya ni kaina ban san dalili ba..
Amma inaso kiyi min wata alfarma..ko nace umarni nake baki,ki zauna tare dani (stay by mu side) har sai na samo amsar tambayar,dan ni kaina tana ci min tuwo a kwarya..

    Juwairiya taja lumfashi ,na zauna tare da shi?kamar ya kenan?

Jalal kamar yasan me take tunani..
Yace,ki zauna a sashena kiyi min hidima har lkcn da zan samu amsar..nake nufi..
Juwairiya ta gyada kai,ai ni dama bani da wani ikon barin sashenka mai martaba dan haka kada mai martaba ya damu..
  Jalal ya saki murmushi me kayatarwa sannan ya kalli jikinsa..yace..
Ban taba saka kaya irin wannan ba..
Juwairiya ta kalleshi itama tana dariya kasa kasa sai kace ba yarima dan gwalisa ba..yasha wasu tazarce..

   Jalal ya kura mata ido,
"ni kikeyi wa dariya?
Baki san duk sbd ke bane... !
Juwairiya ta waro ido...sbd ni?ta nuna kanta..
Jalal yaji haushin furucin da yayi..
Ya dauke kai kawai yana kallon taurarin dake sama..
Juwairiya ta mike tace..
Ni zan taf...
Mgnr ce ta yanke mata jin kukan da cikin yarima yayi..kululululu...

   Da sauri ta kallo shi..
tace ranka shi dade yunwa kake ji ne?
Jalal ya runtse ido, dan rabonshi da abinci tun da safe.. wai duk dan sbd wata al'adar masarauta..mtsww..
juwairiya da mamki tace a zuciyarta ,na zata ai se yafi kowa cika cikinsa a yau?,duk wadannan kayan dadi?ko bai ma ci bane?saboda yazo wajenta?inaaa ah ah ! Ai bata da wannan mahimmanci a wajen sa..

Jalal ne ya mike bai ce mata komai ba sai kawai ya shiga jan hannunta..
  Juwairiya a tsorace tace ina zamuje?ranka shi dade?

Yarima yaja burki kafin ya sakar mata hannun yace..
Rakiya zakiyi min,
kuma umarni ne nake baki..
Juwairiya tayi kasa da kai kafin tace,toh muje..
  Jalal ya juya cikin kasaita suka fara tafiya....

Muje zuwa...👇
TEAM RUMFAR BAYI

[9/18, 3:22 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 24
Wattpad @afreey101

I Pherty dedicate dis chapter to Zauren Biebie Isa Group, Sameena Aliyu Novel Group and Pherty Novel Group, Afrah na godiya❤

*********************

"Tafiya kawai sukeyi amma juwairiya sai ta tsinci kanta a cikin farin ciki sosai..
    Yarima ne zata yiwa rakiya?
Uhmm lallai ta samu wuri kam..
Tuntube ne tayi hakan yasa ta dawo hankalinta..

Sai Can ta hango sa yayi mata dan nisa..
kuma sai ta taga ya nufi hanyar fita daga masarautar ..
  Ai da gudun ta ta karasa gefensa tana fadin..
Allah ya kara maka yawan rai,dama wajen masarautar zamuje ne?naga dare yayi ne?

   Jalal ya tsaya tsak yana kallonta,kafin yace da ita kai tsaye..
tsoro kike ji?
Ta dago ta kalleshi itama..
Ta girgirza masa kai..
Yace,baki yarda dani bane?
Ta kafe shi da ido,kafin ta sake girgiza masa kanta..
Ya jinjinar da kai kawai yayi gaba..
Itama tabi shi a baya da saurinta...

"Sun sha uwar tafiya me nisa kafin suka kawo babban gate din fita....
Fadawa ne sun kai biyar dake gadin wajen..

"Tsayar dasu akayi..
"Kai sai ina!!
Jalal da juwairiya suka ja suka tsaya..
Fadawan suka sha gabansu..
Baku ji me akace muku bane? sai ina?
Jalal har ya dago a fusace dan yayi musu rashin mutumci sai kuma ya tuna da shifa a yanzu ba sarkin su bane....

Sunne kai ya shiga yi dan baya so su gano shi..
Juwairiya ta lura dashi dan haka tayi saurin dawowa gabansa dan ta kare shi...
kafin nan ta hada duk karfinta tace..
  'Umarni ne aka bamu daga wajen fulani,
masu fataucin kayane suka shigo kasar shine aka tura mu dan amso sakon ta sbd juyawa zasuyi da asuba..
   "Fadawan suka shiga gyada kai cike da gamsuwa kafin nan suka bude musu gate din sukace,kuyi hanzarin dawowa...
Juwairiya tayi musu godiya kafin nan suka fice..

"Cikin gari suka shiga,
juwairiya dai bin sa kawai takeyi tana mamakin abunda ya kawo su har cikin gari da daddaren nan..

  A gaban wani me gasasshen kifi da dankalin hausa ya ja ya tsaya..
Juwairiya ta kalleshi,uhm yunwar dai yaji kenan..

Gani tayi yayi tsaye kawai bai ce komai ba sai faman kallon kifin yakeyi..
  Kusa dashi ta dan matsa tace,ranka shi dade ba siya zakayi bane?
  Ya gyada mata kai..
Murmushi tayi dan ta fahimci cinikin ne bai ma san yarda akeyi yinshi ba.
(She don't blame him tunda dai komai yake so yana dashi a ajiye ba sai ya fita ya nema ba)

   "Me siyar da kifin ta kalla,malam a bamu kifi biyu da dankalin biyu shima..
Jalal dai kallonta kawai yakeyi,gani ma yayi ta shiga zabar musu manya mayan kifin tana fadawa me siyar da kifin su take so..

Me kifi ya saka musu acikin takarda..
juwairiya ta amsa ta mikawa jalal..
Ya amsa yana kallonta..
Tace mai martaba kudin sa fa?.
Ya saka hannu cikin aljihun sa yaji wayam..
Chapter 23 · 0% Book details