← Book details Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 53

Sashe 38

Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

********
"Rayuwa tayi wa juwairiya dadi..
ba karamin canzawa tayi ba a cikin yan kwanankin nan..
gashi kuma har tana neman kusan wata daya kenan mai martaba bai bada izinin tafiyar ta kasar kanon dabo ba..
Yau dai da kyal ta samu Ammi ta hada ta da wata baiwa suka fito zuwa sashen khaleed..
Suna shiga suka tarar dashi shima ya fito cikinsa..
juwairiya ta gaishe shi tana murmushi,KAWU irin wannan gayun haka?
Khaleed yayi dariya,diyata zance zani ..ko zakije ne ki gaisa da matar Kawu..
Juwairiya tayi dariya, khaleed ya kamo hannunta muje zakiji dadin haduwa da ita..
Wani bangare taga sun shiga duk a cikin masarautar..
Ta kalle shi da mamaki..
Kawu matarka acikin masarautar nan take itama?
Khaleed yace,kwarai kuwa diyar kanin me martaba ce fa..
juwairiya ta jinjinar dakai,ashe kuma a nan kuna auren hadi..
Khaleed yace,tsoro kikeji?
Juwairiya tayi dariya tsoron me?
Khaleed yace,a hadaki da wani mana..
Juwairiya taji gabanta ya fadi, a hada ta da wani?AMALEN ta fa?ta cije harshenta,zuciyarta JALAL take so bazata taba iya rayuwa da wani ba,ba zata maimaita irin rayuwar da mahaifiyar tayi ba.....

Budurwar khaleed,me suna sumayya tana da kirki sosai,a take shakuwa ta shiga tsakanin su da juwairiya...

Washe gari....

da yammacin ranar talata suka fito ita dasu hassana da hussaina..
    Juwairiya ta kallesu,wai na tambaye ku mana?
  Hassana tace muna jin ki..
Juwairiya tace,idan kamar mutum yana son ya aikawa wani wasika da baya cikin kasar nan taya mutum zayyi hakan?
Hussaina ta rike baki..badai diyar tamu har ta samo mana suriki ba?

  Juwairiya ta ware ido tana nuna kanta..
Ni ah ah wlh uwar dakina..ah ah zainaba kawata ce nayi wa alkawarin aikawa wasika shine nake son na cika mata alkawarin..

Hassana tace,nidai ban taba aika wasika ba amma muje bangaren hajiya na tabbata ya mas'ud zai sani..
Juwairiya tace toh muje dan Allah..ai kuwa duka dunguma suka tafi..

Suna shiga bangaren hajiya sukaci karo da yasira...
Yan biyu suka gaida ita juwairiya ma tayi yarda sukayi..

  Yasira ta kurawa juwairiya ido tana tuna kanwarta zarah'u da sukafi shakuwa sosai a baya...
Hawaye ne suka ciko mata a ido,ta dauke kai tayi gaba ko mgn kasa yi musu tayi..

Juwairiya taji jikinta yayi sanyi..
Hassana ta dafa ta..
Kada ki damu kanki,bawai dan sun tsane ki bane kawai dai kina tuna musu da yaya zarah'u ne..

Juwairiya ta jinjinar dakai kafin suka shige ciki...
   Hajiya uwar gidan mai martaba ce itama ta manyanta sosai..
A cikin falonta suka tarar da ita bayi na ta mata hidima..

   Duk suka gaishe ta cikin girmamawa ..
Ta amsa a sake tana fadin..
Sai yau kuma yan matan suka tuna dani?
Hussaina tace,ah ah wlh hajiya kina ran mu..
Hassana tace,hajiya wai ya mas'ud fa ya na nan kuwa?
Hajiya tace,kun bani ajiyarsa ne?yaron da sai nayi sati ban saka shi a idona ba..
Hassana tayi dariya ai dadin autancin kenan..
Hajiya tace,ku duba sa dai can bangaren maza kila ku same shi..
Juwairiya tace,mun gode hajiya..
Hajiya tace,ai duk kin fi iyayen naki hankali..
Suna dariya suka mike suka fice..

Sbd rashin sa'a suna fitowa sashen hajiya wata baiwa ta tare su da sakon Ammi akan suje tana neman su..

"Lkcn da suka shiga bangaren ammin,khaleed suka tarar a falon tare da haruna suna cin abincin rana..

   Juwairiya ta gaishe su duk suka amsa a sake...
Ammi ce ta fito daga cikin dakin ta tace,wai ku yanzu ace kun fita tun safe baku san ku dawo kuci abinci ba ko?

juwairiya tace,kiyi hkr ammi..
Ammi ta kamo hannunta ai baki da wani laifi ke kam yaran can dai dama haka suka gada...
Muje ciki na nadanar miki abincin ki..
Yan biyu suka saki baki suna kallon ammin farat daya ta daina kuya dasu sai juwairiya..

Khaleed da haruna ne suka hau musu dariya..

"Washe gari mai martaba yace juwairiya ta shirya zasuje can kasar kano dan ta gana da mahaifinta..
   ai kuwa ammi da kanta ta shirya juwairiya tsab,khaleed da haruna ne zasuyi musu rakiya zuwa can din..

*Masarautar kanon dabo...*

"Da yamma suka shigo masarautar..
sarki abu-turab na can fada waziri yaje ya sanar masa da zuwan su..

Yayi mamaki mutuka dan a ganin sa mai martaba yayi tsofan da zai ringa damun kansa da zuwa kawo musu ziyara..ko lafiya?

"Sashen Gimbiya amina suka yarda zango...
Amina tunda taga juwairiya taji gabanta ya fadi..
Ta kalli ammi cike da tsananin mamaki ta nuna juwairiya..

Ammi tayi dariya tace,kwarai diyarki ce amina..
Amina kuka ne ya zo mata,taje ta rungume juwairiya cike da kaunar diyar yar uwarta ta..

Juwairiya tayi kasake tana jin wani iri wai itace yau matar sarki kamar amina take runguma haka,kuma wai yayar mahaifiyar tace...

Khaleed ne ya leko dakin yace,ku fito zuwa falo ga sarki abu-turab ya shigo..
Juwairiya taji gabanta ya fadi..
Hannun amina taji acikin nata..
Tayi saurin kallonta..amina ta sakar mata da murmushi kafin tace muje kiga babanki..

"Juwairiya na saka kafa acikin falon ta hango shi a zaune yasha kaya na alfarma sosai ga rawaninsa mai kyau da tsada kyakkyawa ne sosai ga hutu ya zauna masa sosai...(wannan shine mahaifina?)

Ji tayi zuciyarta tayi rauni sosai..
Amina tace..
Takawa ga yar taka...
Abu-turab ya dago da sauri..
Idanuwansa sauka akan fuskar juwairiya...
Mikewa yayi da sauri yana jin zuciyarsa na bugawa a take kuma ya tuna da zarah'un sa..
Hawaye ne suka taro a cikin idonsa..
Amina tajawo juwairiya zuwa gabansa..
Abu-turab ya rungume ta cike da so da kaunar diyar tasa..
Kuka sosai juwairiya takeyi,wai yau itace a jikin sarkin kano kuma wai mahaifinta ne...
Abu-turab ya dago da ita yana kare mata kallo yace..
Ya sunanki?
Tace sunan juwairiya..
Ya kalli su ammi yana nuna juwairiya, amina ta kama hannunsa,diyar kace ,itace Zarah'u ta haifa maka..
Abu-turab ya zube a kasa..
Ammi taje ta dafa kafadarsa...
Sannan suka fayyace masa komai..
Ba karamin tauyawa juwairiya yayi ba,wai jinin sa ce tayi BAUTA...lallai dolene yayi kokari ya bata duk farin cikin dake duniyar nan...

A sanyaye Yace ki yafe ni juwairiya ki yafe wa wannan uban naki...
Juwairiya ta girgirza masa kai tana zubar da hawaye...

"Abu-turab da amina ne suka shiga rokon ammi da mai martaba akan su bar musu juwairiya ta dan zauna a wajensu..
Da kyal suka samu ammi ta amince ta bar musu ita...

Muje zuwa TEAM RUMFAR BAYI...
👇
SABOWAR RAYUWAR JUWAIRIYA ko ince sarauniya JUWAIRIYA

Sorry for late update

Taku AFRAH BHAI....

   *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 35
Wattpad @afreey101

*sabowar rayuwa*

*******************

"Sarki abu-turab ne da kanshi ya tara dukkan bayin dake cikin masarautar sa..
  Gimbiya amina ya saka ta zabarwa juwairiya sababbin bayin da zasuyi mata hidima daga wannan ranar ta yau..

Cike da kwarewa amina ta shiga zabar mata su..
Abu-turab ya jinjina kai yana yabawa zabin matar tasa dan kuwa duk yan matane ta zabo kusam sa'annin juwairiya din..yasan diyarsa zataji dadin zama dasu..

     Ya kalli wani dogari yace dashi,ka dauki bayi kuje can sabon sashen dake kusa dana amina a gyarawa juwairiya shi ta zauna a ciki..
   Amina ta karaso wajen mijinta tana mai farin cikin ganin sa a cikin wannan yanayin..
Abu-turab ya kamo hannunta suka shige cikin sashen sa..
Ya kalleta yace..
Na gode sosai da taya ni farin cikin da kikeyi inaso ki tayani rikon juwairiya..
Amina ta girgiza kai..
Ka manta diyar zarah'u kamar a matsayin diyata take nima?
Gashi kafi kowa sanin yarda yake kwadayin samun diya mace nima ko?

  Abu-turab yayi dariya..hakane gimbiyata..gashi kuma kin samu..
Sannan Idan su yarimaADO da Abdullahi sun dawo gobe inaso ki hada su yar uwar su..

Amina tace,ai wannan ya zama dole..mai martaba
Abu-turab yace,yauwa inaso kuma ki saka jakadiya ta zauna ta koyar da juwairiya Al'adu da halayen zama a gidan sarauta,tunda dai kin ga a inda tayi rayuwar ta a baya..

Amina ta jinjinar dakai,hakane kada ka damu inshaAllah zakayi mamakin juwairiya,abu-turab yace nagode sosai gimbiyata...

"Amina na fita daga sashen abu-turab ta kira jakadiya da hanne (sabowar baiwar juwairiya)ta basu umarni akan su fara koyar da juwairiya da'bi'u da halayen jinin sarauta..
Jakadiya tace,kada ki damu ranki ya dade kamar anyi an gama ne wannan..

Juwairiya na zaune a cikin dakin amina,hanne ta shigo cike da girgimawa tace..
Sannu da hutawa uwar dakina..
Juwairiya taji abun wani banbara kwai..
Hanne ta sake fadin..
Ki fito gimbiya amina nason mgn dake..
Juwairiya ta mike ta filo falon..
Amina ta kalleta cike da kulawa..tace
   Juwairiya zo nan kiji..ta nuna mata kusa da kilisar da take zaune..
Juwairiya tayi yarda tace..wato ta zauna a kusa da ita..
Amina tace,inaso yanzu ki bi su jakadiya zuwa sabon sashen ki dan su koyar dake da'bi'u da al'adun mu na gidan sarauta kinji?
Juwairiya tayi murmushi ta gyada kai..
Amina tace yauwa diyata tashi kuje..

"Ba karamin haduwa sashen na juwairiya yayi ba,dan a ganin tama yafi sashen zainaba nesa ba kusa ba..
Komai yaji zam zam..

  Jakadiya da hanne ne suka shiga koyar da ita duk abunda suka san zai amfane rayuwarta a cikin masarautar dama waje... a matsayinta ta sarauniya juwairiyya kuma diyar sarki abu-turab..
   Tunda ga yarda ake zaman kilisa..
Yarda ake tafiya..
Yarda ake cin abinci..
Yarda yake amsa gaisuwar bayi..
Yarda yake bada umarni..
Yarda ake jan aji..
Yarda ake kasaita..
Da dai sauran su.........
Juwairiya ta cika da mamaki,wato komai zakayi a gidan sarauta sai an koyardake kenan?

Sai ta tuna da halayen YARIMA kau sarki jalal..
A take ta saki murmushi mai kayatarwa..
Hanne ce tace da ita..
Kinfi kyau idan kina murmushi haka uwar dakina..
Juwairiya ta kalleta,itama fa a baya tayi irin wannan rayuwar..
A sanyeye tace da ita Nagode hanne..

"Acikin kwana biyu kacal sai da jakadiya ta tabbatar da juwairiya duk ta koyi abunda suka koyar da ita..

Tabbas kuma an samu canji nesa ba kusa ba,dan kuwa ita kanta juwairiya har mamakin kanta takeyi..
Komai nata ya canza a cikin dan kankanin lkc...
Gashi sarki abu-turab na mutukar kula da ita duk da baya samun zuwa wajenta sosai amma yana aiko mata da sakwanni sosai..hakama gimbiya amina duk suna nuna mata soyayya..
Chapter 38 · 0% Book details