← Book details Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 53

Sashe 33

Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Turaki ya girgiza kai..yace..
Sonta nakeyi samira ba zaki taba ganewa ba..
yarinyar nan tun tana yar karamar ta take aikin bauta a rayuwarta,bata san wani jin dadin yarinta ba da kowane yaro yake samu..
bata da wani yanci ko zabi a rayuwarta,haka ta taso a cikin RUMFAR BAYI  babu wani digon farin ciki a rayuwarta..
Dan haka idan auren tane kawai zai sa na fitar da ita daga wannan rayuwar da take ciki toh zan iya sabawa da duk yan uwana dan nayi hakan..

Samira tayi murmushi lallai Allah yayiwa turaki zuciya me kyau..
  Tace,TAUSAYINTA kawai kakeyi turaki..

Dan haka a shawara ta indai har kana son kagan ta acikin farin ciki toh lallai ne ka YAN'TAR da ita kawai daga bauta amma kada kayi kuskuren danne mata hakki kace zaka aure ta...
Tana gama fadar haka ta mike ta fice...
Turaki ya shiga nazarin mgnr samira..

*********
    Jalal na kwance a kan gadonsa zazzabi ne sosai ya lullube sa...
  Khadija ce ta shigo dakin..
Ganin halin da yake ciki ba karamin tsorata tayi ba..
Da sauri ta fita tayi sashen gimbiya kilishi dan ta sanar da ita..

Hankali a tashe gimbiya kilishi ta shigo sashen nasa..
     Tausayi sosai ya bata,dan tasan ko da yana karamin sa baya son ko kadan mahaifinsa yayi masa fada akan gaskiyarsa...lallai dole ta koyawa surayya hankali,dan duk sbd ita ne haka ya faru..
Me magani aka kira ya shiga duba sa..
Khadija na gefe tana masa sannu..

*******
Mutanen ku kuwa su umayma...

Wani kauye sukaje can kusa da SANDAMU a nan suka samu wani malamin tsabbu..
   Surayya ta fayyace masa komai..
Dariya yayi ya buga kasa yace..
Ni ban ga wani aure a tsakanin wannan baiwar da kanin mijin naki ba...

Sai dai kuwa naga wani haske a tattare da yarinyar..
Surayya taja tsaki..ya wuce na yan'cin da take shirin samu gobe..

Malamin yace yanzu me kike so ayi miki?
   Surayya tace,so nakeyi kawai gobe idan an gama yan'tar da ita tayi gaba... tabar masarautar mu,dan bana son ta kara waiwayar kasar daura .....
  Umayma ta jinjina kai lallai surayya ta cika shu'umar mace..

Malam ya buga kasa ya kallesu..
Kamar anyi an gama ne ranki ya dade..
Surayya tayi murmushin murna sannan ta basa kyauta me tarin yawa suka fice...

**************
Washe gari...
  Sosai ne juwairiya taji sauki se de kafafunta da kyal take iya tafiya..

Fadawa ne suka shigo har cikin rumfar bayi sukace ana neman ta a can fa'da..
Hansai da laure ne suka shiryata tsab dan lbr har ya gama bazuwa,kan ZA'A YAN'TAR DA JUWAIRIYA...
Murna sosai bayi suka shiga yi,lallai Allah yana son juwairiya da alkairi daga ruwa rumfar hukunta bayi sai barin BAUTA daga daya...

A fada kam,jalal ne a kan (throne ) dinsa ga sauran royal family duk an hallara kowa ya samu waje ya zauna..
Surayya ma kanta dadi takeji dan tasan abunda ta kulla har wani kagara take ayi ayi a yantar da juwairiyar ta bace daga rayuwar su..

"Juwairiya kuwa na saka kafa acikin Fa'dar idanuwanta suka kai kan jalal dake hakimce fuskarsa babu yabo babu fallasa..dan sosai yake jin dadin yantar da ita da za'ayi..
Ahankali ya dago da kwayar idonsa ya sauke su akan ta yana aika mata da wasu sakwannin masu wuyar fassarawa.

Gaba dayansu zuciyoyin su sun dan karaya balle ma shi jalal din da yake ganin kamar(plan)dinsa bazai yi masa wani amfani ba.......

Toh readers menene PLAN din JALAL?

Not edited

Team RUMFAR BAYI

*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 31
Wattpad @afreey101

*****************

"A gaban dun'bin jama'a waziri ya Yan'tar da baiwa juwairiya kamar yarda al'adar masarautar tasu take..

   "Wani irin lumfashi me nauyi ta sauke....
farin ciki sosai ya ziyarci zuciyarta bata taba jin irin wannan yanayin ba a duk rayuwarta..
Jalal kansa sai da yaji wani irin sanyi acikin zuciyarsa,yau kam zai zama tahiri babba a wajensu,daga inda yake yana kallon yarda juwairiya ke ta sakin murmushi hakan ba karamin dadi yayi masa ba..

    Hansai da sauran bayi ne suka shiga congratulating din juwairiya cike da murna su,suna ji dama ace sune aka yantar,dan a wajensu idan aka yantar da baiwa kamar an sake haihuwar ta zata fara sabowar rayuwa me cike da yanci da farin ciki.

    Addu'a akayi taro ya watse...

"Jalal na fitowa daga fa'da ya koma sashen sa ya saka jakadiya ta turo masa juwairiya can bayan sashensa su hadu yana da mgn mahimmiya da yake yayi mata..
Jakadiya ta jinjinar dakai tana tuna lkcn da suka sanar mata taimakon da turaki yayi mata da kuma furucin da yayi na sonta,ko yanayin fuskarta se da jakadiya ta fahimci juwairiya bata son turaki,jalal ne a zuciyarta..

     "Zainaba ba karamin murna tayi ba ta makakkale juwairiya a jikinta,tana jin dadin yarda zata iya hada jikinta da ita a yanzu..
samira ce ta karaso wajensu tare da khaleed dan uwanta, dukkanin su mamakin kamanni ta sukeyi da Ammi har lkcn.
samira tace,na taya ki murna sosai..
Juwairiya ta murmusa cike da farin ciki tace nagode kwarai..
Khaleed ya kura mata ido yana tunanin zancen su da sarki jalal yau da asuba Allah yasa yarinyar ta amince..
Wani bawa ne yazo wajen yayi kiran samira,tayi musu sallama ta kama gabanta..

   "A daki samira ta tarar da turaki a zaune..
Ta karasa wajensa tace..
Gani ance min kana kirana..
Ya dago ya kalleta..kafin yace..
Nayi tunani akan maganar ki ta jiya..
Surayya tace, kuma me ka yanke hukunci akai..zaka tilasta mata auranka ne,ko kuwa ?

Turaki yace bazan taba yiwa juwairiya dole ba..dan haka bashi ne niyya ta ba..

Samira ta saki murmushi tace,naji dadin yarda ka zauna kayi tunani me kyau haka ,
yantar da ita da kayi ma ya isa ka taimaka mata sosai..
sai dai fa ni wlh wannan juwairiyar tana min kama da AMMI sosai..

Turaki ya gyara zama..
Me kike nufi?wacece kuma Ammi?
Samira tadan muskuta..
Ammi amaryar mai martaba ce wato kakana..
Turaki ya girgiza kai,babu alakar da zata hada Juwairiya da ita gsky dan kuwa iyayen juwairiya a cikin masarautar nan suka haife ta kuma naji lbrn yan asalin kasar daura ne..
Samira ta jinjina kai hakane nima nayi wannan tunanin...

*******
"Jakadiya ce ta samu juwairiya ta sanar mata da sakon jalal..
Kallon jakadiya tayi a dan tsorace..dan bata zaci tasan me ke tsakanin ta da yarima ba..

Jakadiya tajawo ta zuwa gefe tace..
Kada ki damu juwairiya ina bayanku keda AMALE..yanzu kije yana kiran ki..

Juwairiya na daga kafarta taji wani irin faduwar gaba,muryoyi ta shiga ji a kunnen ta kamar ana kwala mata kira..
Waige waige ta shiga yi..
Fuskokin su laure,hansai,rabi,zabba'u, zainaba kawai take kallo dake wajen tana jin wani irin abu yana tokare mata wuya..

  Gaba daya jikinta ya hau rawa..
Jakadiya tace,kije mana kinsan ba'a barin Amale jira..
juwairiya ta gyada kai,tana tafiya ne kawai amma gaba daya zuciyarta a dakule take..ji takeyi gaba daya gangar jikinta bata kaunar zama acikin masarautar..

"Jalal kuwa na zaune akan wani dan dakali yana ta faman zuba ido..
Duk ya rame sbd tunanin da saka a gaba yanayi duk lkcn da yake shi daya..

Yanzu dai addu'ar shi daya ce Allah yasa ta amince da (plan)dinsa...

    Hango ta yayi ta taho amma hankalinta kamar baya jikinta...
Da sauri ya mike ya karasa wajenta..
    Tana ganinsa ta lumshe ido tana dafe kirjinta,wani dan sanyi sanyi a cikin ranta ganin fuskarsa...

   Jalal ya kamo hannunta..
Ya jikin ki?ina fatan kin samu lafiya..
Juwairiya ta kura masa ido kawai ta kasa furta komai..

Jalal yace,ki yafe min ....
nasan duk nine silar shigan ki cikin wannan halin..
Juwairiya gaba daya ji takeyi lumfashin da take sha'ga yana dauke wa..
    Jalal gani yayi ta fada jikinsa babu shiri..
A rikice yace..
Me ya faru?
Baki ji dadin yantar dake da a akayi bane?na dauka ai yau ranar farin cikin ki ne..

Juwairiya ta girgiza masa kai..
Idanuwanta na fitar da kwalla ta dago daga jikinsa tana kallon kwayar idonsa tace..

'Ka taimaka min ranka shi dade..

  Jalal cikin murya me sanyi yace..
Bakya son auren turaki ne?
juwairiya ta kallesa da mamaki kafin ta girgiza kai..

Jalal ya ce toh taimakon me kike so nayi miki?
(A zuciyarsa kuwa yana addu'a yake Allah yasa idan ya bukaci ta gudu daga masarautarsu tabi khaleed kasar zazzau ta yarda...yarda zai samu ya yi shirinsa sosai,dan bazai taba bari ta zauna a nan ba turaki ya aure masa ita,dolene ya samar ma kansa mafita)

Ji yai tace..
   Ka taimakeni yarima,ina ji a cikin zuciyarta ko sakwon daya nayi a cikin wannan masarautar toh zan iya rasa rayuwata...

   Waro ido jalal yayi cikin al'azabi..me hakan yake nufi?me ya same ta dare daya?daga samun yancin ta?
Yanayin ta kawai yake kallo,shes not normal..akwai wani abu a kasa dan har kwayar idonta juyawa takeyi tana birkicewa..

Ya sa hannu ya share mata hawayen dake fuskarta..dan tausaya mata sosai,dole akwai abunda akayi mata,dolensa ya kare ta daga sharrikan GIDAN SARAUTA..

  kwantar da murya yayi yace..
Naji ki kwantar da hankalinki nima nayi wannan tunanin..(yayi using opportunity din)

Zan hadaki da khaleed dan uwan matar turakine ku tafi can kasar zazzau sai ki zauna a wajen kafin na gama shirin da nake na waiwaye ki..

Juwairiya ta damke hannunsa cikin nata..
Kayi min al'kawarin zaka neme ni koman dadewa..ni kuma nayi maka alkawarin jiranka har lkcn da zaka zo min da amsa ta..
Jalal ya janyo ta jikinsa yana cikin wani irin tausayinta a cikin zuciyarsa..
Na miki alkawari JUWAIRIYAR..na miki alkawarin nemo ki a duk inda kike,zan zo miki da sakon zuciyarta..

Taja lumfashi kafin tace nagode sosai ...duk suka sauke ajiyar zuciya..

*******
"Kamar yarda suka tsara da shi da khaleed..
zai saka shamaki ya fitar da ita ta kofar baya sai su hade a can da tawagar du khaleed su wuce zazzau da ita...

"Juwairiya ta shiga rumfar bayi da gudu ta shige dakinsu tana rusar kuka..
Hansai na ciki tare da laure suna ta faman murna basu san meke faruwa ba..
Chapter 33 · 0% Book details