← Book details Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 53

Sashe 34

Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonsu tayi..
Kafin ta fada jikinsu ta saka wani kukan...
Hankali a tashe suka shiga tambayar ta ko lfy?
  Juwairiya ta dafe kirjinta..tace
Umma bazan iya ba..bazan iya ba umma,zuciyarta jinta nake kamar zata tsage ya zanyi umma?
A rikice laure tace..
Meke damunki haka juwairiya?
Juwairiya ta fashe da kuka..
Umma zan bar RUMFAR BAYI zan bar masarautar daura, idan ba haka ba ji nake umma kamar zuciyata zata iya fashewa.. ji nake na tsani duk wani lumfashi da zan shaka a wajen nan..

Hankalin su ba karamin tashi yayi ba..
Kuka suka sosai sukeyi dan a take suka fahimci sihiri ne a jikin juwairiya(kunsan mutanen da' da saurin canfin su)
GIDAN SARAUTA  kenan! sunsha ganin ire iren wadannan matsalolin..

Jakadiya ce ta shigo cikin saurinta..
Itama kukan ta saka ganin su a haka ba karamin karaya zuciyarta tayi ba.

"ta shiga kwaso kayan juwairiya dan jalal yayi mata bayanin komai,ita kam a ganinta kila wani haske ne yazo musu dan bayyana wa juwairiya ASALINTA ... (dan har kamarsu da Ammi sun fada mata shi da khaleed kuma bata koye wa jalal komai ba ta fada mishi yarda suka sami juwairiya ,jalal ya girgirza sosai amma yasha alwashin indai yana raye sai ya nemo wa juwairiya ASALINTA)

       Hansai ta kamo hannun jakadiya suka dan fita waje..
Jakadiya tace,kiyi hakuri hansa'u ni a ganina duk abun nan da ke faruwa alkhairi ne inshaAllahu a wajen juwairiya,kika sani ko wannan tafiyar tayi sanadiyyar saduwarta da yan uwanta na usuli?

Hansai na kuka shabe shabe tace,hakane jakadiya, amma ina zata nufa yanzu?wa take dashi?
Jakadiya tadan waiga ganin babu kowa a wajen sai ta fayyacewa hansai duk abunda ta sani a tsakanin jalal da juwairiya...

Hansai ta ware ido ta saki baki,ta kasa gasgata mgnr jakadiya, amma ko ba komai taji dadin taimakon da jalal zayyi wa juwairiya,gashi kuma Allah ya kawo wa juwairiya ranar da zatayi bankwana da BAUTA..

"Jakadiya,laure da hansai ne suka fito a asirce dan su fitar da juwairiya..

A kofar Rumfar bayi sukaci karo da shamaki yana jiransu..
Juwairiya ta juya tayiwa RUMFAR BAYI kallon bankwana,sannan ta kalli hansai tace..
Umma dan Allah ki bawa zainaba hakuri,kice mata nayi alkawarin aiko mata da wasika idan har na samu masauki me kyau..
Hansai tace,kada ki damu juwairiya zan isar mata da sakonki...

'Ta kofar baya suka fita,a inda suka tarar da motar khaleed tare da wasu maza kuda biyu..
Juwairiya na kuka shabe shabe tayi bankwana da iyayenta sannan tayi bankwana da MASARAUTAR DAURA....

********

"Gu'da kawai kake ji na tashi daga sashen gimbiya surayya,umayma ta kalleta cike da farin ciki..
Yanzun nan wani bawa yake sanar dani,yaga fitarsu juwairiya ta kofar baya kuma da alama ita akeyiwa rakiya...

Lallai aikin malamin nan kamar yankar wuka yake..
Surayya ta gyara zamanta..tana murmushin samun nasara...tace
Yanzu dai na kawar da wannan shegiwar yarinyar saura na mallake SARKI JALAL na haifa masa YARIMA me jiran kujerar mulki...
Duk suka kwashe da dariya..

************
"Tunda suka hau kan hanya juwairiya ke ta rusa kuka,sai dai ba karamin wasai takeji a cikin zuciyarta ba,ji take kamar an sauke mata wani katoton dutse daga kanta..

   Khaleed ne ya lumfasa ya kalleta..
Ki daina kukan nan haka mana..
Juwairiya ta gyada masa kai ta shiga goge kwallarta..tana jin kewar yan uwanta da kuma AMALEN ta..

Khaleed ya kalli me tuka su yace,idan mun kai malumfashi sai mu tsaya a ci abinci..
Juwairiya ta buga tagumi tana tunanin irin rayuwar da take ciki...
Ooh!
Yanzu kuma komai rayuwa ta ajiye mata?
...daga aikin BAUTA zuwa samun YANCINTA yanzu kuma tana hanyar yin HAJIRA......

**********
"Ba su iso kasar zazzau ba sai cikin dare sosai...
Khaleed na ganin haka ya wuce da ita can bangarensa ya bata wani daki yace ta kwana a ciki zuwa gobe da safe...

"Juwairiya tayi masa godiya sannan ta shige cikin dakin da kullin kayanta..
Dakine karami amma ya tsaru sosai dan tunda take ma a rayuwarta bata taba kwana a cikin irin sa ba..

"Ta ajiye kayanta a gefe sannan ta mike ta shige kofar da take tunanin ta ban daki ce..
Alwala ta farayi tana kaiwa wajen wanke fuska ta shafo tabon dake fuskarta, tsaki taja tace,Allah ya kawo min lkcn da zan wanke wannan tabon karyar daga fuskata har abada..
Ta saka ruwa sosai ta wanke shi tas,se taji wani irin wasai a fuskar ta ta,alwalar ta dauro ta fito..

Tana shirin ta'yar da sallah taji an kwankwasa kofar dakin..
Tsoro ne ya dirar mata..
Muryar khaleed taji yana cewa ta bude shine..
Ta karasa ta bude masa kofar...
Wani irin faduwar gaba ne ya ziyarci khaleed..
Cikin mamaki ya nuna fuskarta..
Me ya samu fuskarki ina tabon yake?

Tayi murmushi tace..lbr ne me tsawo..
Khaleed ya jinjina kai,lallai akwai wani boyayyen al'amari a tattare da yarinyar nan,yaji dadin da jalal yayi wannan tunanin,tabbas akwai (link)a tsananin su da Ammi..

"Takardar dake hannunsa ya mika mata,ga wannan babu yawa dan nasan dare yayi da kyal mu samu abinci daga cikin gidan..
Juwairiya ta bude takardar,balangu me zafi ga kuma yaji a gefe da albasa sai baza kamshi yake..

Miyau ta hadiye tace nagode sosai..
Khaleed yace,babu damuwa se da safe..
juwairiya tace Allah ya kaimu lfy...

"Tana shiga dakin,tayi sallolinta sannan ta jawo takardar balangun ta,ta lashi lebenta na kasa,lallai kuwa Allah me iko wai yau itace da cin balangu irin wannan..
"Sai da Taci ta koshi tasha ruwa ta kwanta...

******

Washe gari da safe..
Bayan tayi sallar asuba ta sake komawa barci dan gaba daya jikinta a gajiye take..

Kwankwasa kofar khaleed ne ya farkar da ita daga mafarkin jalal da takeyi..

Ta mike da sauri tana mamakin kanta..
Lallai su juwairiya har an samu wuri,ta fadi tana ma kanta dariya..
Bude masa kofar tayi..
Khaleed yace,ki shirya zan shiga dake can cikin gidan..

juwairiya ta gyada kai sannan ta koma ciki tayi wankan ta ta sake kaya..
Lkcn da khaleed zai dawo har ta kammala komai..
Dan haka tafiya kawai sukayi....

Team RUMFAR BAYI
*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 32
Wattpad @afreey101

_"Lovely fans of RUMFAR BAYI i appreciate your love for this story,your comments means alot to me,INA YINKU IRIN SOSAI DIN NAN"_
_#teamyarima #teamjuwairiya #teamJJ #teamJULAL #teamRumfarbayi_

*******************

"Tunda suka fito daga cikin bangaren na khaleed juwairiya ke ta kallon irin tsari da girman masarautar zazzau, tabbas tafi masarautar su nesa ba kusa ba..

  "Tafiya sukeyi juwairiya na faman kallon yarda bayi take zurga'zurgar su ,a zuciyarta tace,oh duk dai in da bawa yake dan wahala ne shi..

Gani tayi duk inda suka wuce sai an tsugunna an gaishe da khaleed cike da girmamawa,shi kuma a amsa musu a sake,ta lura ko kadan baya da wani girman kai..

   Wani bangare taga sun nufa,me girma da kyaun tsari,yasha sabon fanti..
   Suna shiga cikin wani makeken falon ta ware ido tana kallon irin kwalliyar da falon yasha,gasu fan'teka da kwalla duk an yi jere dasu gwanin ban sha'awa..

Khaleed ya kalleta yace,ki zauna mana ya nuna mata waje a kasan darduma..

Wata baiwa ce ta fito daga wata kofa ta zube a gaban khaleed tana kwasar gaisuwa cike da girmamawa..
Ya jinjinar dakai kafin nan yace,marka ina uwar dakin naki take ne?ita na shigo na gani..

Marka dake ta kallon juwairiya tace,ai tana ciki ranka shi dade bari na sanar da ita ka shigo..ta juya ta koma kofar da ta fito da saurin ta..
Juwairiya kam ba karamin tsarguwa tayi da irin kallon da marka ke mata ba..

"Suna nan a zaune shiru kusan minti goma..
Juwairiya taji wani irin kamshi ya daki hancinta..
Tayi saurin dago da kanta...
Sai caraf taci karo da fuskar AMMI..dake kokarin karasowa cikin falon cikin shiga ta alfarma..

   ita kuwa Ammin gaba daya hankalinta na wajen khaleed ne dan bata ma lura da juwairiyar dake zaune a gefe ta tsare ta da ido ba...

   cike da fara'a Ammi tace da khaleed...ah ah mutanen daura ne saukar yaushe?
Khaleed yayi murmushi yana gyara zamansa yace,jiya da daddare na dawo Ammi mun same ku lafiya?
Ammi tace lafiya kalau... ya kuma ka baro mana samirar?

Khaleed yace tana nan kalau ai da bakuwa ma nake tafe Ammi..ya nuna gefen da juwairiya take a daskare tana bin Ammi da kallo..

   Ammi ta juya inda taga khaleed na kallo sai cin karo tayi da fuskar data tsorata ta sosai..
     Kallon kallo suka shiga yiwa juna ita da juwairiya kamar idanuwansu zasu zazzago..
Khaleed dai gyara zaman sa ya sakeyi yana jira yaga yarda za'a karkare..

***********
*A masarautar daura kuwa*

"Jalal hankalinsa a kwance yake sosai dan yasan khaleed zai kula masa da juwairiyar sa..
tunda ya daukar masa alkawarin yin hakan.
Yaja lumfashi..
Allah yasa juwairiya ta gano asalinta...
shine kawai addu'ar sa a gareta dan kuwa yana so itama ta samu farin ciki a cikin zuciyarta..

A halin yanzu yana zaune ne a cikin wajen shakatawar sa...
Ba karamin kewar juwairiya yakeyi ba..

Surayya ce ta shigo da sallamarta...
ko kallon inda take bayyi ba..
Zama tayi a kusa dashi ta narkar murya tace..

Sarkina ka yafe min na san kana fushi dani,amma wlh bani da niyyar kai karar ka a wajen abba..
Jalal yaja tsaki yana mamakin halin surayya..
Ta sake kwantowa jikinsa..kaji sarkina kayi hkr..
Jalal a zuciyarsa yace..lallai wannan yarinyar yar rainin hankalin ce,dolene ya ho'ra ta da abunda yasan zai fi yi mata ciwo..

Murmushin mugunta yayi sannan ya kwalawa jakadiya kira..
Sai gata da sauri ta shigo wajen..tace gani ranka shi dade..
Jalal yace,inaso ki aika min sashen khadija a fada mata yau ina gayyatar ta kwana a sashena..

  Dam!zuciyar surayya ta buga..lallai ma wato a gabanta yake gayyatar matarsa kwana?babu wani dan kawaici?

Jakadiya tayi murmushi sannan tace, An gama Amale..ta fice...
Surayya taja tsaki,ta mike rai a bace tabar sa awajen..
Jalal yayi dariya yace kadan ma kika gani Surayya...

*************
"""Zabba'u ce ta sanar ma zainaba tafiyar juwairiya..
Kuka sosai tayi na kewar ta tana jin haushin rashin zuwanta suyi bankwana..
wasiko kin da Mustapha ke aiko mata ne ta dauka sannan taja zabba'u suka fice zuwa lambu..
Chapter 34 · 0% Book details