Sashe 2
Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
'Yarinya ce mai karanbani sosai bata ji,sai dai tasan iyakarta,dan kuwa kullum zaka ganta tana guje gujenta a cikin rumfar bayi wanda hakan yake saka bayin dake ciki annashuwa.
ummanta wato hansai tana kokarin bata tarbiyya irin tasu ta bayi marassa ga'lihu,haka kuma kamilu na mutakar son JUWAIRIYA dan dama ya dade yana neman haihuwa Allah bai basa ba.
(kamilu da hansai bayin Allah ne da kaddara ta fado musu aka siyar dasu a matsayin bayi ga masarautar ta daura)
"Tunda juwairiya ta ta'so bata taba ko da lekawa ne cikin masarautar ba dan kullum tana cikin rumfar bayi' gashi bata da abokin wasa dan duk bayin dake ciki da safiya tayi suke ficewa zuwa wajajen uwayen gidansu. .
Kamar kullum yau ma hansai ta gama shiryawarta dan tafiya wajen uwar dakinta wato GIMBIYA KILISHI,ta kalli juwairiya dake zaune ta kura mata idanuwanta masu haske,kamo hannun ta hansai tayi tace kici gaba da hakuri juwairiya kinji abbanki zai zo miki da halawa anjima,juwairiya ta saki dan murmushi sannan tace,umma muje na miki rakiya,hansai ta murmusa sannan ta kamo hannunta, suna kaiwa bakin kofa ta sake hannun juwairiya sannan ta shafa kanta kafin ta fice.
Hansai na tafiya juwairiya tayi saurin karasawa gaban babban kofar ta leka abunda bata taba yi ba kenan sbd gargadin da ummanta tayi mata..
Ware ido tayi ganin jama'a da yawa nata zurga zurgar su ga wani haske da har kashe mata ido yakeyi ga kuma iska me dadi dake kadawa..
Da sauri ta karasa cikin dakinsu ta dauko mayafin ummanta,ta boye shi a cikin doguwar rigar dake jikinta .
A hankali ta karasa madafa waton inda ake shirya wa sarki abincinsa, ta leka nan ta tarar da bayin dake dahuwa suna ta aikinsu,ta juya da sauri ta lulluba mayafin a kanta sannan da gudu ta saka kafa ta fice daga rumfar bayi..
**********
"Tafiya kawai takeyi tana kalle kalle sai washe baki takeyi dan bata taba ganin mutane masu yawa haka ba balle jinsin maza dan kuwa a rumfar bayi babu namiji a ciki.
"wani dan zomo ne ta hango fari dashi tas,ba karamin burgeta yayi ba,ta shiga binsa da gudu batayi aune ba taji tayi karo da mutum bum!
Da sauri taja da baya...
"Baki da hankali ne?ina kika bar idanuwanki da har zaki taremin hanya ta!!
Taji an fada da wata murya me cike da isa da iko..
Dagowa tayi da sauri dan son ganin waye wannan me muryar..yake magana kamar yana kirga lafuzan sa.
Caraf idanunsu suka sarke dana juna..
Wani dan saurayi ne da kalla zai kai shekara sha biyar..
Juwairiya ta kafe shi da ido dan tunda take bata taba ganin me kyau irin nasa ba,ahankali ta fara fahimtar irin kallon kyama da kaskancin da yakeyi mata..
hakan yasa ta shiga bin shigar shi da kallo..
Sanye yake da kayan alfarma kayane masu tsada ga zinari ta ko ina sai kyalli yake..
Ta kalli yaron dake kusa dashi at least shi ze kai 11 years,shima din cikin kayan alfarma yake..
Bakya jina?
Tayi saurin ja da baya kadan sannan tace,a tunani na mu biyune da laifin..
'tunda idan ni bani da ido ai kai kana dashi ba sai ka kauce min ba?
Cike da tsantsar mamaki suke kallonta..
Wacece ita da har zata ringa maida masa magana haka?
Juyawa yayi cike da fusata..cikin daga murya yace,wai ina sarkin Lumbu ne! Sallama kana ina!
wayace musu su ringa barin ya'yan bayi masara galihu suna shigowa nan!
Cikin sauri wani mutune yazo ya zube a gaban sa,Allah ya huci zuciyar YARIMA ayi min afuwa ayi min gafara!nayi laifi ka yafewa wannan bawan naka...
Wanda aka kira da Yarima ya yamutse fuska sannan ya kalli na gefensa,HAMZA me kake ganin zamuyi dasu?
Hamzan ya tabe baki,kawai mu kaita ga GIMBIYA tunda dai kowa ya sani BAYI basu da ikon shigowa cikin lumbun TAKAWA (wato sarki)..
RANKA SHI dade ayi musu afuwa..
Sukaji an fada daga bayan su..
'A tare duk suka juyo suna kallon shi..
Saurayi ne dan shekara 12 kyakkyawa ne sosai rike da hannun yar budurwa da bazata wuci sa'ar juwairiya ba..
Yarima ya daure fuska, saboda me zaka neman musu gafara TURAKI?
Turaki yai murmushi sbd a tare muke da ita kulangar ZAINABA ce..
Hamza da yarima suka ja tsaki sannan suka zo zasu wuce ta gefen juwairiya ta dago suka hada ido da yarima ya banka mata harara, ta bi shi da kallon mamaki har ya fice yana jin zafin halayen ta a garesa ....
"Da sauri juwairiya ta karasa wajensu turaki ta dukar da kai tace,na gode ranka shi dade..
Da kallo yabi fuskarta,daga ina kike?dan ban taba ganinki a cikin masarautar nan ba..
RUMFAR BAYI ta bashi amsa,ya jinjina kai,zainaba ta kalli yayanta,yaya turaki ina sonta!
Da sauri suka kalli zainaba cike da mamakin furucinta ..
Turaki yace,zainaba ke da kika ki amincewa da kowacce baiwa?zainaba tayi murmushi sannan ta juya da gudu tayi tafiyarta..
Turaki ya juya ga juwairiya data bi bayan zainaba da kallo..
Kiyi gaggawar komawa inda kika fito dan na lura ba ki gama fahimtar wasu dokokin masarautar nan ba,yana gama fadar haka yayi ficewarsa...
A sanyaye juwairiya ta koma cikin rumfar bayi gaba daya taji bata ma kwadayin sake fita dan kuwa duk mutanen da ke waje basu da mutumci ita kam zaman ta a Rumfar bayi yafi mata dadi inda kowa yake da same rights dinsa.......
Wannan kenan!
🏕 *RUMFAR BAYI* 🏕
Na Afrah bhai
Page 3
********************
"DAN SARKI JIKAN SARKI !!
"DAN SARKIN DA BASHI BA SARAUTA!!
"AAH LAFIYA TORON GIYA...
UWAR SORO"taci gaba da da yiwa yarima jalal kirari..wanda ke kokarin shigewa falon mahaifiyar sa..ko kallon inda take bayyi ba bata ..
"Sai Hannu kawai da ya da'ga mata fuskar nan a tamke..
"Gimbiya kilishi na zaune akan kilisarta tasha gayu cikin kayan alfarma zinari ne ba'a mgnr sa..
ga bayi nan sai yi mata hidima suke,hansai na gefe rike da tiren fruits kala'kala..
Kilishi na kallon dan nata ta fahimci cewa ransa a bace yake...
Hansai ta kalla tayi mata alama da su fice daga falon..
'Hansai ta mike sannan tayi wa bayin dake cikin falon mgn akan su fice..
"Kilishi ta kalle sa,yarima lafiya?
Yarima jalal ya dauke kansa gefe..
Tasan bazai yi mata mgn ba dan haka sai ta kalli hamza..
Hamza me ya samu yayan naka?
Hamza yaja tsaki,wai fa umma dan..........nan ya fada mata komai..
A fusace ta mike tana huci,wacce baiwa ce da har take da wannan ikon na maida wa yarima mgn!dole ne na hukunta ta dole ne tasan matsayin ta.!!!..
Yarima ya mike da sauri...
Kada ki damu umma na lura gidahuma ce dan bata gama sanin matsayinta ba..
Kilishi taja tsaki,dolene ta fuskanci hukuncin abunda tayi!..
Yarima ta riko hannun umman nasa,kada ki damu umma ya sakar mata murmushi..
Da kyal da so'din goshi yarima ya samu ya lallaba kilishi ta hakura..
**********
"Da gudu zainaba ta shiga makeken falon FULANI diyya dake tsare tsab cikin kwaliya ta gargajiya..
'Fulani diyya na zaune a kilisarta ga bayin ta nan duk sun zagaye ta sai hidima suke mata..
"Ganin zainaba ta shigo da gudu cike da murna yasa ta fadada murmushin ta..
Laure dake gefen fulani ta shiga fadin,yar sarki diyar FULANI wannan murna taki dole ta farantawa dukkanin wanda ya kalli wannan kyakkyawar fuskarki rai..
Zainaba tace Allah ko laure?
Laure tace kwarai kuwa ranki shi dade..
Fulani ta murmusa,me ya sakaki wannan farin cikin zainaba?
'Ta zauna tana lankwashe kafafunta,fulani na canja ra'ayina ina so a yau din nan nima a bani baiwata..
Fulani ta kalli laure cike da murna,laure tace Yanda kike so ai haka za'ayi gimbiyata..
Laure ta mike da sauri tayi waje..
Cikin minti goma sai gata da wasu yan matan bayi su biyar..
Ta kalli zainaba dake kishingedi tana cin tufa (apple )
Gasu nan ki zaba wacce ta mike gimbiyata..
Zainaba ta kwabe fuska sannan ta kalli fulani,umma duk bani son su..
Fulani ta kalli laure tayi mata nuni da ta koma ta canzo wasu..
Laure ta sake fita ta shigo da wasu yan matan har su shidda..
Still zainaba a shagwabe tace suma haka..
Laure cike da gajiya da wulakancin zainaba ta fice ta sake dauko wasu dan saida ma ta zabo su sannan ta zo dasu..
Zainaba ta girgiza kai tana turo baki..
Fulani ta sauke ajiyar zuciya dan ba yau bane zainaba ta fara wannan fitinar..
Toh wai zainaba wacce irin baiwa ce kike so ne haka?ina tunanin sai dai a kai ki can kasuwar bayi ki siyo da kanki..
Zainaba tayi saurin cewa ah ah RUMFAR BAYI zaku kaini umma..
Cike da mamaki bayin dake wajen suke kallonta dan kuwa babban kaskanci ne ace jinin sarauta ya shiga rumfar bayi..
Kina da hankali kuwa!
Fulani ta fada cike da daga murya..
Zainaba ta turo baki,umma ni wacce nake so tana can a RUMFAR BAYI..
Laure ta hadiye yawu kut amma sanin kuma juwairiya bata fita ko ina.. da wuyane a san da ita a cikin masarautar ma,sai ta sauke ajiyar zuciya tace,ranki shi dade wacece ita yanzun nan na kawo miki ita?
Zainaba ta langwabar da kai..
Sannan tace..
Wata yarinya ce kamar ni haka..
Laure taji kafafunta sunyi sanyi..
Fulani tace,me kike fada haka,kin taba jin a Rumfar bayi akwai yara ne?
Zainaba tace wlh umma da bakinta tace mana a Rumfar bayi take..kima tambayi yaya..
Fulani zatayi magana sukaji ana sanar da shigowar turaki..
Sai daya zauna ya gaisar da fulani sannan tace..
Wai turaki wane shirme ne zainaba ke fada,tace min akwai yarinya baiwa dake rumfar bayi kuma ita take so a matsayin baiwar ta ..
Laure ta cije baki...a ina zainaba ta gano juwairiya kuma?
Turaki ya kalli zainaba, ke dama da gaske kike?
Zainaba ta gyada kai ni ita nake so ta zama BAIWA ta ..
Ya kalli fulani eh mun hadu da wata yarinya dazu tace mana a Rumfar bayi take..
Fulani cike da tsananin mamaki ta kalli laure..
Wai haka?
Laure ta kakalo murmushi..
A...eh..eh....kam..anyi haka..akwai diyar hansai ina tunanin itace suka gani din...
Fulani ta ce cike da kasaita a kawo min ita nan!