← Book details Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 53

Sashe 40

Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    Da saurin sa ya juya.......
Dai dai lkcn da gimbiya amina ke  dauke hular alkyabbar dake rufe da fuskar juwairiya.......

  caraf..ya hango fuskar da bayyi tsanmanin ganin ba ko kada..
Ji yayi gaba daya jinin dake jikinsa ya tsaya cak,kwakwal'warsa ta bar aiki a take...
Ware ido yayi yana nuna ta daga can cikin dubban mutanen da yake ciki..
Itace......ya furta...
Mamaki ne ya rufe sa sosai..
Me takeyi a nan?
Meye haka ke faruwa?
Me ya kawota kasar kano daga kasar zazzau?

Samun kansa yayi da bin ta ido kamar wanda yaga wata fatalwa..
Sai wani haske take tana kashe ido kamar wata taurariya...

Ji yayi mutanen dake wajen nata yaba kyawun ta suna susuta tsarin ta..

  Lkcn da zai farga sai gani yayi bata a wajen..

  A rikice ya kalli dogaran dake wajen yace..ina zuwa kada ku biyo ni..
Da saurinsa yabi hanyar da yake tunanin nan ne ta bi...

"Neman ta ya shiga yi kamar wani mahaukaci..
sai can ya hango shigen irin alkyabbar daya hango ta da ita dazun..tafe take tare  da wasu bayi mata a bayanta sai daya dake rike da hannun ta..

   Karawa tafiyar sa sauri yayi..
Yasha gaba su da saurin sa yana ssuke ajiyar sa...
  Hanne dake rike da hannun juwairiya da fuskarta ke rufe har wannan lkcn..

Ta kalli jalal zata balbale shi...
ji tayi mgnr ta tsaya mata a makoshinta sbd irin kyaun da kwarjinin da jalal yayi mata a ido..
Gaba daya bayin suka saki baki  suna kallonshi kamar wani angle..

Jalal da zuciyarsa ke ta bugawa da sauri da sauri..
Ya saka hannu ya dauke hular alkyabbar daga kan juwairiya...

   Juwairiya ta dago da saurinta jin kamshin da ba zata taba iya mantawa dashi ba...
  Mutuwar tsaye ne sukayi su dukan na wani dan lkc.... suna karewa juna kallo cike da tsantsar mamakin ganin junan su a wannan lkcn..

    Jalal ya kamo hannunta da karfi ya shiga janta...
Hanne ta yunkura tana sake rike hannun juwairiya gam..
Juwairiya ta girgiza mata kai..kafin tace..
Hanne ina zuwa..
Hanne ta sake ta...
jalal yaci gaba da janta har suka karasa bayan wani gini da babu kowa a wajen.

"Ya sakar mata hannun yana kare mata kallo daga saman ta har zuwa kasan ta..

Ba karamin kyau tayi masa ba kamar ba ita ba,duk ta canza..
juwairiya kanta kallon shi takeyi..
Jalal kyakkyawan namiji ne ajin farko...
irin (guy)din nan ne da kowacce mace take mafarkin samu a matsayin mijinta..

Jitai yace...
Kece haka?
Ko mafarki nakeyi?
Juwairiya bata ce masa komi ba.. sai karasawa da tayi zuwa gabansa ta sa hannu ta muntsine shi a hannunsa...
Tace..
Ni ce...kana mamaki ko?
Ya gyada mata kai..
Tace toh zan fada maka komai ranka shi dade yanzun nan..
Zauna...
Ta nuna masa wani dan dakali..
Jalal ya zauna itama haka..
   "Juwairiya taja lumfashi kafin ta shiga bashi dukkan lbrn ta..

  Ba karamin tausayawa mahaifiyar ta yayi ba.. shi bai san meyasa mata suka fiye zalunci haka ba sbd son duniya..Allah dai ya kara tsarewa..

Ya sauke ajiyar zyciya..
Abun al'ajabi wai juwairiya jinin sarauta ce itama..
Ya saki wani irin murmushin murna lallai komai yazo masa da sauki..
Yanzu ne lkcn da zai bayyanar mata da irin son da yakeyi mata..

     Ya kalleta cikin ido yace..
Na tayaki murnar saduwa da dangin ki..
Juwairiya tayi murmushi tana sadda kai kasa tace nagode ranka shi dade..
  Jalal ya murmusa yana fadin...

Inaso na kebance dake anjima..
sbd na lura gidan naku yau a cike yake..
Juwairiya tace hakane,sai dai anjiman zaka iya samuna a sashena..
Jalal ya girgiza kai...
A sirri nake so mu hadu...
Juwairiya ta kura masa ido,tana jin sonsa na ratsa ta..
Tace..
Toh shikenan zan aiko hanne ta sanar dakai a inda zamu hadu..

    Ta mike tana kakkabe kayan jikinta..kafin tace..
Toh Sai anjiman kenan ko?
Jalal yayi saurin mikewa shima..

Jitai yace..
Wato dan yanzun kinsan umurnina bazai yi tasiri akan ki ba shiyasa kike neman guduwa ba tare da neman izini na ba ko?

  Juwairiya tayi murmushi tace
haba dai kai fa sarki ne ni kuwa diyar sarkin ce kaga har yanzu umurnin ka dole yayi tasiri a kaina..
Jalal yaja lumfashi...sannan ya samu kansa da furta abunda ke cikin zuciyarsa..

"Nayi kewarki rashin ki a sashena....

Juwairiya tayi mutuwar tsaye...
Dan kalaman shi sunyi wa zuciyarta shigar mamaki..

Yadai da kallon kina mamaki ne?
juwairiya ta gyada kai cike da kunyarsa..
Yayi dariya yana daga kafadar sa..
Ina jiran sakon ki anjima...
yayi gaba cike da tsantsar farin ciki acikin zuciyarsa..

"Taro ya tashi lafiya?baki duk sun wuce masaukinsu...
     Jalal da magaji tare da sauran bayin da sukazo daga kasar daura  duk suna sashen bakin inda aka sauke su..

    Magaji sai mamakin jalal yakeyi..
Ganin yarda ya wani saki rai sai faman fitar da murmushi yakeyi tun dazun.
    Magajin ya dawo kusa dashi yana fadin..
Ni kuwa AMALE dazu kaga diyar sarkin kanon nan?
Ni sai nake gani kamar nasan fuskarta a wani wajen amma na kasa tunawa...

Jalal yayi saurin kallonsa..
Magaji yace,ko da yake ma me yasa zan tamabayeka kai da kayi tafiyar ka..
Jalal ya mike yana fadin..
Bari na shiga na watsa ruwa...
Magaji ya girgiza kai wani abun sai AMALE..

"Juwairiya ta dauko wasu kaya ta saka bayan ta fito daga wanka..
Sai data gama shirinta tsab sannan ta kira hanne...
Tace..
Hanne aiken ki zanyi dan Allah..
Hanne tace toh ranki ya dade inaji..
Juwairiya tayi dan jim kafin tace..
Kije sashen da aka sauki bakin mai martaba inaso ki sanar da sarki jalal ya same ni a bayan sashena yanzu..

Hanne ta kura mata ido..
Juwairiya tayi saurin cewa..
Gaisawa kawai zamuyi dashi..
kuma ki fada masa sakon a cikin sirri kinji?
Hanne tayi dariya na gane ranki ya dade kada ki damu..

Hanne na fita juwairiya ta fada kan gadonta tana murmushin murna..
Yau dai zata kasance da jalal dinta..
Allah yasa ya sanar da ita amsar da ta dade tana son ji daga bakinsa...

"Lkcn da hanne ta shigo sashen bakin wani bawa ta tarar ta fada masa tana son ganin sarki jalal..

Bawan yayi sallama a cikin falo a lkcn jalal da magaji na zaune suna fira..
Bawan yace wata baiwa ce tazo yanzun wai tana son ganin ka ranka shi dade..

Jalal ya mike da saurinsa..
Ya kalli magaji..yace
Ina zuwa..
Magaji yabi sa da kallon tuhuma..
Jalal ya fice da saurin sa...yana ji wani irin farin ciki na ratsa sa..

"A tsaye ya tarar da ita ta juya bayanta..
Jalal ya saki murmushi sannan ya karasa wajenta da sallama..
Ta juyo suka hada ido dashi..

A tare suka sakarwa junan su murmushi..
Jalal ya bita da kallo up n down..
Tana sanye ne da doguwa riga kalar ja da baki sai mayafinta kalar fari da digon baki..sai kamshi take bazawa..

   Jalal yace..
Kin canza..
Ta kalli jikinta da sauri..
Amma kinfi kyau a haka..
Ta lumshe ido ta bude kafin tace nagode..
Jalal ya gyara tsayuwarsa yace..
kamar yarda nayi miki alkawari zan fada miki amsar tambayar ki duk lkcn da muka sake haduwa..

Ya shafa sajen fuskarsa yana fadin..
Tun a baya ban gama fahimtar abunda yasa nake kyautatamin miki ba,sai bayan wani lkc da zuciyata ta shaku dake...
Juwairiya ta kura masa ido..
Jalal ya kalleta cikin ido yace..
Juwairiya....
Yarda ya furta sunan sai da tsikar jikinta ya tashi..

*INA SONKI.........*

Wani irin yanayi taji wanda bazata iya fassara shi ba...
Zuciyarta nata harbawa..dum!dum!dum!

Jalal ya dawo daf da ita ya tsaya..
Kece mace ta farko da zuciyata ta fara kamuwa da sonta..
Bansan dalilin da yasa nake sonki ba..
Amma tunda idanuwana suka ga wannan kyakkyawar fuskar ta ki a wancan lkcn na kasa sukuni...
Na rasa meke damuna..
Bani da tunani sai naki..
Ina mutukar jin dadin kasancewa dake....
Juwairiya.....
Ina kuma fata kema zuciyar ki ta kamu da son JALAL ko?

Wani irin kunya ne ya lullube ta..
Tayi saurin juyawa zata gudu..
Ya cafko ta da karfi yana rungume me a jikinsa...

A cikin kunnenta taji yace..
Ko bakya son MIJI me mata biyu ne?

juwairiya taji wani iri har cikin zuciyarta a take kuma ta tuna da irin wulakancin da surayya tayi mata..
Sai Ta samu kanta da turo masa baki ta kwace jikinta daga rikon sa..

Jalal yabi ta da kallo..
Ta kalleshi..tace
Kasan dai yanzu ba da bane ba ko?dan ina yancina..!
Jalal dai kallonta yake..cikin mamakin canzawarta farat daya(but he like ha courage)..

Taci gaba..
Toh kada ka kara tuna min da wadan nan matan naka..
Jalal ya rike kugu..yana fadin..
Eyyyeeeeh duk kishin ne haka?

Juwairiya  tadan harare shi..
Ba wani kishi so nake kawai ka bari dan bana so..
Jalal yace,toh ina dai jiran amsata zuwa gobe kafin na tafi..

  Juwairiya tace wace amsar?
Jalal ya rike baki,lallai yarinyar nan  haka kika koma?
Juwairiya tayi murmushi  tace eh din..
Jalal yasa hannu ya fisgo ta zuwa jikinsa..
Kallon cikin idonta yayi..yace..
Ina ganin SONA da kishina a cikin wadan nan kwayar idanuwan naki...
Dan haka ina jiran amsata sbd bana son wani yayi min shigar sauri kin gane?ya kashe mata ido daya..

Juwairiya ta samu kanta da gyada masa kai..
Yace yauwa ko ke fa..
Muje na maida ke sashen naki..

"Hannayensu sarke dana juna har suka iso kofar sashen nata..
Ya sakar mata hannun sannan ya matso zuwa gabanta..

Ji tayi kawai ya kai wa goshin ta sumba (peck)
Ta runtse idonta ta budesu ahankali  tana jin wani irin abu ya na tsirga mata..
Chapter 40 · 0% Book details