← Book details Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 53

Sashe 15

Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   Zaune yake ya lumshe idonsa..
Ta samu waje ta takure sannan tace..
Ranka shi dade gani nazo..
Har cikin ransa yaji sautin muryar ta..
A hankali ya bude ido ya sauke su akanta..

  Juwairiya tayi saurin dukar da kai..
Yarima yace,zauna yana nuna mata waje a nan kusa dashi kadan..
Juwairiya ta kalleshi taga yarda ya tsare gida dole yasa taje ta zauna wajen a takure..

Yarima bai bata lkc ba ya kwalawa bawansa kira..
Se gashi ya shigo cikin saurinsa..
Yarima ya fada masa dayaje ya sanar da du'bu a can rumfar bayi a kawo masa abincinsa yanzu..
Bawan ya amsa da toh kafin nan ya fice..

Juwairiya dai ta rasa me zatace masa,yace  mata tazo sashen sa amma ya ajiye ta a nan yayi shiru,ga ciwon dake kafar ta yana dan damunta kadan kadan...

A wajen Yarimakuwa  ya rasa meke damunsa,me yasa yake son ganin wannan yarinyar a kullum ne kusa dashi?me yasa ta dame sa har haka?

    Yadan kallo ta, tsoronsa ma takeyi daga gani,yaja lumfashi me dumi,kafi karfin baiwa kamarta yarima...ya fadawa kansa..

      Haka yayi ta tunani a zuciyarsa har bayi suka shigo da abincin jere a cikin tiren silver.
sai faman kallon juwairiya sukeyi cike da mamakin ganinta a sashen.
balle kuma a inda take zaune dan kuwa basu da hurumin zamaa  wajen,balle kuma wai tare da yarima cab...!

    Suna gama shirya abincin suka fice bakin su kunshe da gulma iri iri..

    Juwairiya ta lura da hakan dan kuwa tasan a Rumfar bayi gulma kala kala ake kawo musu..
Ta tabbata sai lbrn zuwanta sashen yarima  ya kai wa ummanta..

   Ta kalli yarima shi kam ko a jikinsa ma..
Mikewa tayi da sauri tace,uhm ranka shi dade bari na zuba maka abincin..
Jiki na rawa ta kai hannun ta dan daukar plate dake ajiye gabansa..
   Sai jin saukar lausassan hannun yarima tayi akan nata..
  Tsikar jikinta ce ta tashi..
Gabanta na faduwa ta kalleshi ido a bude...

Yarima ya motsa bakinsa,duk da shima baisan dalilinsa na taba jikinta ba kawai dai bayajin yin mgn ne kuma yana so ya tsayar da ita daga daukar plate din.
Ki barshi...ya fada yana dauke hannunsa daga nata..
Juwairiya tace toh!
Zan iya tafiya?
Yarima ya girgiza kai ,zauna kici...ya nuna abincin dake gabansu.
juwairiya ta waro ido ta dafa kirji Ni?
Yarima yace me kika dauke ni?Giwa?baki ga naci abinci bane dazun?

Juwairiya tayi wiki wiki da ido,nima zanci anjima...ta fadi kamar zatayi kuka..
Yarima ya daure fuska,umurni ne nake baki ba zabi ba...

A sanyaye ta zauna..
Yarima ya basar abunsa...
Juwairiya ta kalli delicacies din dake gabanta, miyau ta hadiye dan rabonta da abinci tunda safe da suka karya..
  Ta kalli gefen yarima taga ya dauke kai gefe..

Abincin ta diba ta hau ci da saurinta dan ta samu ta tafi da wuri..
   Yarima yayi murmushin gefen baki.
Tana kammalawa ta mike,nagode zanka shi dade Allah ya baka kujerar mulkin daura..

  Ya saki murmushin da bai san lkcn daya subuce masa ba..
Juwairiya mutuwar tsaye tayi...dan bata tunanin ta taba ganinsa yana murmushi haka,kyau da kwarjini yayi mata har bata san ta kafe shi da ido ba..

Yarima ya kalli kafarta...
Na lura kin samu masu baki magani dayawa ko? ba sai na baki wani ba...
  Juwairiya ta dauke idonta tana kallon kafar,murmushi ta saki tunawa da kyallen daya bata dazu..sai ta kwanto shi daga zaninta ta mika masa..

Ga wannan Allah ya baka yawan rai,nagode kwarai da gaske...
  Yarima yabi kyallen da kallo..
Sannan ya mike yazo kusa da ita ya tsaya..
     Bana amsar abunda na bada a matsayin kyauta..
Juwairiya ta dago da sauri,kyauta ya bata?ita juwairiya har ta kai yarima ya bata kyauta?
      Yarima ya lura da mamakin furucin sa takeyi,yace zaki iya tafiya..
Juwairiya ta juya da sauri tayi waje...

*************
"Tana shiga tafe tana tunane tunane,har ta kawo wajen ajiyar dawakai,hango mahaifinta tayi yana bawa dabbobin abinci...
Ai da sauri da gudunta ta karasa wajensa...

Lah baba! Ta fadi da karfi..
Ya juyo cike da farin cikin ganin ta,juwairiya kece haka?
juwairiya ta saki dariya baba yaushe ka dawo?shine umma bata sanar min da dawowarka yau ba?ta karashe mgnr cike da shagwaba..

  Baba ya kamo hannunta,jiya da daddare na samu dawowa,juwairiya tace nayi kewarka baba sosai,ka tafi ka barmu...
Baba yayi murmushi kiyi hakuri juwairiya kinsan fa cewa sarki da kansa ya bani umurnin tsayawa a can kasar kanon ta dabon,sannan shima mai martaba na can yaki barina na dawo kasata akan lkc, yanzu ma haka sati daya kacal zanyi na koma..

Juwairiya ta jinjina kai,su kenan basu da yan'ci sai yarda akayi dasu,gsky BAUTA batayi ba...
Zama tayi a wajen babanta suka sha fira har yamman dare sannan ta koma rumfar bayi...

"Tana shiga laure tazo ta fisgo ta cikin karfi,da mamaki take ta kallon yarda take ta janta  har suka shige daki... hansai na a zaune ta buga uban tagumi...

   Miye haka goggo laure?juwairiya ta tambayeta...
Laure ta kai mata dankwashi akai,ubanki ne !wato ke juwairiya duk yarda muke jan kunnenki ba zaki san matsayin ki ba ko?
  Juwairiya tace,na sani mana...me akace nayi kuma?tayi mgnr a sanyaye..dan tasan ruwa baya tsami banza..

Hansai tace,me ya kaiki sashen yarima?
Baki san waye shi bane? Acikin wannan watan fa zai zama sarkin daura !!!yafi karfin yarinya irin ki!bakya tausayin rayuwar ki ko!???

Juwairiya ta kalli hansai da mamaki,tace sarki?
Laure tace,kwarai kuwa,mai martaba zayyi murabus ya basa mulki kwanan nan!...

Hansai ta kamo hannunta, juwairiya a kullum ina fada miki,ke Baiwa ce!ki kare mutumcin kanki...

Juwairiya tayi murmushin yake,na fada miki umma ki yarda dani,kawai fa sako naje amsa a wajensa,kuma shi ya umurceni dana je wlh..
Laure tace,ki kula dai kinsan haukan kishin matarsa atooh..
Juwairiya ta gyada kai zan kula goggo...

**************
"Gimbiya kilishi ta kalli fulani diyya suna zaune a fadar mai martaba.
ina ganin tunda lkc ya matso kusa ya kamata mu fara shirye shirye a kan lkc..

Fulani tayi murmushi, hakane zan saka turaki ya hadu da hamza se suyi duk abunda ya dace..
Mai martaba ya murmusa, sai dai nima akwai alkawarin da nake so na cikashi a wannan babbar ranar..
Kilishi tace,muna jinka..
Mai martaba yace,akan auren yarima ne da diyar waziri nasan kun san da wannan mgnr amma ina ganin kamar lkc yayi dana cika alkawarin dana dauka shekaru dayawa da suka wuce,tunda dai anyi auren sa na farko ..
Kilishi tadan tabe baki,hakane tunda ya zama dole mu cika wannan alkawarin..
Fulani tayi murna sosai tace,lallai yarima ya cika dan gata,mai martaba yace,ai da mun gama dashi zamu zo kan sauran suma,sbd dai akwai diyar galadima da nake so a hada da shi hamza,shi kuma turaki nayi masa mgnr jikar sarkin zazzau...

Kilishi murmushin yake tayi dan ita kam tana wa hamza tanadin diyar sarkin katsina,mai zanyi da wata diyar galadima lallai kam....

"har an gama mgnr su kenan suma?fulani ta tambaya cikin tsantsar farin ciki ..
Mai martaba yace kwarai kuwa lkc kawai nake jira..
Fulani tace toh Allah ya kaimu lfy..

**************
Surayya ce ta karaso cikin lambun cike da fara'ar ta,yanzun nan ta samu labarin na'din yarima da za'ayi a karshen satin nan...

   Hango sa tayi a tsaye yana karewa wasu tsuntsaye kallo...
  Ta karasa da saurinta ta rungume sa ta baya tana murna sosai..

  Yarima yana jin kamshin ta ya gane itace..
Surayya tace,ina taya ka murna sosai sarkina...
Yarima yadan murmusa,kodai kina taya kanki murnar zama gimbiyar daura?...

Surayya ta dawo gabansa,duka biyun daidai ne...
yarima ya gyada kai..
Surayya ta kamo hannunsa,sai yaushe zaka bani damar shiga zuciyarka?
Yarima ya kura mata ido,surayya ta karkace kai,naji lbrn aurenka da diyar waziri,hawaye suka taro a cikin idanuwanta....

Yarima yace, na zata duk wannan bazai dame ki ba...
Surayya tace,inji wa?ai duk mulkin mace bazaso ayi mata kishiya ba..
Yarima ya jinjina kai....

************
Juwairiya tare da zainaba suna tafe sai lbrn wasikar da Mustapha ya aiko mata take bata...
Suna kawowa kofar lambu zainaba tace,mu dan shiga naji kukan tsuntsayena,ta janyo hannun juwairiya suka shige ciki....

  "Turus sukayi ganin yarima da surayya rungume da juna...
"Juwairiya taji gabanta yayi wani irin muguwar faduwa har se da ta saka hannu ta dafe shi..
  Zainaba kuwa sakin baki tayi..ganin basu ma ji shigowar su ba yasa tace, sannunku masoya...!

  Da sauri duk suka juyo suna kallonsu..
Yarima idanuwansa akan juwairiya dake tsaye ta dauke kanta gefe,haka nan takeji zuciyarta wani iri,meye nata aciki dan kawai miji da mata na more rayuwar su..tasan dai ita harta mutu bazata samu wannan ba..

   Zainaba tace,lallai yaya ashe haka kake kaima?
Yarima ya banka mata harara,sannan yace me ya kawo ki nan?

Zainaba ta kamo juwairiya dake tsaye kamar an shuka ta,laah toh kuyi hakuri idan dan mu ne yanzu ma zamuyi tafiyar mu..

Surayya sai wani murmushi takeyi,tazo zata kamo hannun yarima,ya kauce yana sake kallon su juwairiya dake shirin barin wajen..
   Zainaba!

Ya kira sunan kamar me koyon mgn,zainaba cike da mamaki ta juyo dan kuwa ta dade bataji yayan nata ya kira ta da sunanta ba..

  Ta dawo gabansa tace na'am yaya..
Yace inaso ne kiyi min wata alfarma,

zainaba tace ina jinka yaya...

Ki bani waccan....!

Ya nuna saitin da juwairiya take a tsaye..
    Ba zainaba ba har surayya da juwairiya se da gabansu ya fadi..

Sai a lkcn ne surayya ta shiga scanning din juwairiya tana jin wani irin tsanarta ta dasu a zuciyarta, wacce baiwa ce har ta isa ta saka yarima ya bukace ta...

Ruwan harara ta shiga zubawa juwairiya, ita kuwa baiwar Allah ma bata san tana yi ba..

    Zainaba da mamaki tace,wa kake nufi yaya,dan a iya sanina baka ma son ko ganin fuskar juwairiya...
Yarima ya kasa amsa mata dan kuwa sai a lkcn ne ya fara jin haushin kansa,me yasa ya bari mgnr ta fito daga bakin sa...

Gani sukayi kawai ya wuce abunsa kamar bashi bane yayi zancen..

Surayya ma tazo wucewa zuciyarta kamar ta fashe..ta tsaya daidai saitin juwairiya sannan taja dogon tsaki tayi gaba..
Zainaba tace oh iko sai Allah...

************************
WATTPADIANS
Chapter 15 · 0% Book details