Sashe 17
Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiiish ya daura yatsan sa akan leben sa..sannan ya shiga takowa har ya kawo gabanta ya tsaya..
Kirjinta ne ya shiga bugawa....tayi saurin sauke idonta kasa..
Jalal da muryarsa mai dadin amo yace, me ya kawo ki sashen na?ko baki san hukuncin shigowarki nan din ba ne?
Juwairiya ido ya kawo kwalla,na..na..sani..amma...ka..kayi hakuri dan..darajar Allah...
Jalal ya murmusa yana jin wani irin nishadi na dibar sa..
Dago ki kalleni...ya bata order..
Juwairiya ta sake kasa dakai,mai martaba yin hakan a gareni kamar raini ne..
Jalal ya sake murmusawa,sannan ya kama hannunta...
a tsorace ta dago da kanta suka hada ido dashi,ji tayi gaba daya jikinta yayi lakwas...
Jalal ya janyo ta sannan naga ya bude wata secret door sun shige daga ciki...
Bude baki tayi ganin su a cikin kogin mai martaba...
Jalal ya kura mata ido ganin yarda ta saki baki tana kallon wajen..
Juwairiya ta juyo tana kallonsa..
Wani irin murmushi ta sakar masa da ita kanta bata san miye dalilin ta na yi masa shi ba..
Jalal yaji bugun kirjinsa ya linku,bai taba ganin ta tayi murmushi haka ba..
Juwairiya ta zare hannunta daga nasa tana sake juyawa tana kare wa wajen kallo..
"Jalal ya kura mata ido kamar ya samu TV..
Wani tunani ne yazo mata acikin zuciyarta ,sake juyawa tayi ta dawo kusa dashi ta dukar dakai..
Cikin sanyin murya tace..
"Ranka shi dade idan bazaka damu ba ina so nasan dalilinka na kyautatamin da kakeyi a cikin yan kwanankin nan,nasan bani da hurumin yi maka wannan tambayar ,amma zuciyata na mutukar son taji amsar ka..
Jalal ya lumshe ido ya bude..
Me zai iya fada mata,shi kansa bai gama sanin dalilin sa ba..
Tambayar dake cin zuciyarsa ce ta fado masa shima ,meya sa take boye fuskarta da wannan tabon...?
Juwairiya taji shirun yayi yawa..
Ta dago suka hada ido...
Gani tayi jalal yasa hannu ya fisgo ta da karfi..
A tsorace ta shiga bashi hakuri..amma inaaa bai tsaya ko ina da ita ba sai gaban kogin...
Jikin juwairiya ya hau rawa..kayi hakuri ranka shi dade na tuba!bazan kara ba..kayi min rai!
Jalal bai saurare ta ba.. kawai sai ji tayi yasa hannu a wuyanta ya tura kanta cikin ruwan..
Wani irin ihu ta saki tana jan lumfashi kamar zata mutu,me yasa jalal yake shirin kashe ta?me tayi masa?tunani iri iri ke yawo acikin zuciyarta,ta sadakar da sake yin wata rayuwar sai ji tayi ya dago da ita ya fito da kanta acikin ruwan..
Idanuwanta ne da sukayi ja ta kura masa ido cike da tsantsar tsoro da kuma mamakin abun da ya aikata mata a yanzu..
Jalal kansa kallon fuskarta yakeyi kafin nan ya juya ya koma kofar da suka fito...
bai dade ba ya sake dawowa gabanta dauke da mirror a hannunsa..
Duk abunda yakeyi kallonsa kawai takeyi,ta rasa me yake tunani haka,kashe ta yake sonyi???
Jitai yace...
"Kalla nan"
Madubin dake rike a hannunsa ta kalla...
Fuskarta ta gani tangaren babu ko di'gon tabo a jiki..
Ware ido tayi sannan ta kallesa da sauri..
Jalal ya gyara tsayuwarsa..
Zaki iya fada min dalilinki na boye fuskarki da wannan tabon na karya?
Gabanta ne ya shiga faduwa jikinta ya hau rawa,tun yaushe yarima yasan wannan sirrin nata?yau ta banu!
Jalal ya sake fadin..
Idan har zaki iya fadamin dalili toh nima zanyi kokari na samu amsar tambayar ki na kyautata miki da nakeyi...
"Juwairiya taji kuka yazo mata,me zata iya fada masa?taya zata iya fada masa ma sbd ta tsare mutumcin kanta ne yasa take boye fuskarta da tabon karya...
Zubewa tayi a kasa tana kuka sosai..
Jalal ya dan dafe kansa..
Kafin ya duka kasan kusa da ita yace..
Ba kuka na tambaye ki ba!
Juwairiya ta dago da jajayen idonta tace.
Ranka shi dade idan na fadi maka nayi hakan dan kawai na tsare mutumcin kaina ne zaka yarda dani?
Jalal cike da rashin fahimta yake kallonta..
Juwairiya ta shiga goge hawayen ta tana sake fadin..
A wajenku ku masu mulki da iko mu bayi ba komai bane ba,kun dauke mu tamkar kayan kazanta ko kayan da zaku iya sakawa ku yar ba tare da kun damu da feelings din mu ba..
bamu da wani galihu ko girma a idon ku..
ta nuna kanta tace,ni yarinya ce dana taso cikin tarbiyyar iyayena wadanda suke bayi a karkashin ikon ku,na taso ne acikin RUMFAR BAYI kuma tabbas naga yarda mata yan uwana suke fuskantar musgunawa da cin mutumci a wajen wadan da suka fisu karfi da mulki..
Taja lumfashi...
A lalata rayuwar su ko kuma a siye su a matsayin SA'DAKA ba'a damu da nasu ra'ayin ba.
mahaifiyata a kullum cikin tunanin yarda zata tsare min mutumcina takeyi,sbd haka ne sukayi min wannan tabon a fuskata dan ya taimaka wajen tsare ni daga maza masu lalata rayuwar bayi mata irina..
Jalal tunda ta fara mgn yake saurarenta har ta kai Aya bai tsayar da ita ba..
Kukan ta taci gaba dayi cike da takaicin yarda asirin da suka dade suna boyewa ya tonu..
kuma wai Sarki jalal da kansa ne ya gano su shikenan kokarin su ya zama a banza...
Ji tayi kawai an fisgo ta..
sai saukar kanta taji a fadadden kirjin jalal me fitar da wani irin kamshi me sanyi...
Gaba daya wutar ce ta dauke...
Meke damun yarima?
Jalal ya rasa me yasa ya kasa controlling kansa,juwairiya ta fara kiciniyar kwace kanta..
Jalal ya sake ta yana maida lumfashi, sannan ya mike tsaye ya juya ya fice daga wajen cikin saurinsa..
Juwairiya ta bi bayansa da kallo,ta kasa yarda da zuciyarta, tasan jalal yafi karfinta nesa ba kusa ba amma me yasa tajiki ajikinta kamar ya fara having feelings akan ta,ta girgiza kai da sauri...
kai inaaa tausayi kawai take basa..
Mikewa tayi da sauri tunawa da tayi dadewar da tayi a wajen,ta tabbata zainaba zata neme ta..
Da gudu ta fito falon tana yan leke leke ga mamakin ta babu kowa a wajen,ta sauke ajiyar zuciya sannan ta fito waje tana sake rufe rabin fuskarta ta da mayafin dake kanta...
"Juwairiya "
Taji an kira sunan ta a lkcn da take kokarin barin sashen ..
A dan tsorace ta juyo sai ganin umayma tayi tana mata wani irin kallo..
Murmushin dole tayi mata tace,umayma ashe kece?
Umayma tace uhm ni ce,juwairiya tace,bari na karasa toh tayi saurin barinta a wajen tayi gaba ..
Umayma ta jinjina kai,mai ya kawo juwairiya turakar sarki jalal?lallai akwai wani abu kasa...
dole ne tasa ido akan ta..
"Umayma na shiga ta samu jakadiya ta fada mata sakon surayya na son ganin jalal..
Jakadiya ta shiga ta sanar masa yace shi bazai ga kowa a yanzu ba,dan yana hutawa ne..
Jakadiya ta fito ta fadawa umayma, ba haka suka so,umayma jiki a sanyaye ta koma sashen surayya..
Murmushin mugunta surayya tayi,ta kalli umaymah tace, babu komai zanci gaba da jiransa,tunda dai mun samu wannan yarinyar tasha maganin hana daukar cikin ai bani da wata matsala dan yanzu ni kam..
Umayma ta murmusa kada ki damu ranki shi dade,na samu wata baiwa mai amana sosai a can madafar kuma na fada mata sakon ki,ta amince zata rinka saka maganin acikin abinci gimbiya khadija.
surayya ta jinjina kai cike da gamsuwa tace,aikin ki yana kyau umayma...
*************
"Khadija ta kalli rabi bayan fitar zainaba tace daga dakin,yadai kin ganta kuwa?
rabi ta fito da layar data kunshe acikin zaninta ta mika mata,khadija tayi saurin amsa tana fadin, ki kiyaye bakin ki!bana son jin sirrina yana yawo acikin wannan masarautar kin gane?
Rabi ta gyada kai,khadija tace yauwa muje na koma sashena...
********************
Bayan sati daya...
"A cikin yan kwanakin da suka wuce gaba daya jalal bai zauna ba,
kullum suna cikin fa'da aiki yayi masa yawa sosai,duk irin nemansa da matan sa keyi bai sa ya kula kowaccen su ba.
A yau ma dai sun samu dan hutu ne shine ya zo dan gaida mahaifiyar sa..
Gimbiya kilishi na hakimce akan kilisarsa..
Cike da kulawa tace, jalal kaga yarda ka koma kuwa? Ina tunanin lkc yayi da zaka canza bayin dake kula dakai kamar yarda al'adar masarautar take..
Jalal yace,ummana kenan,aikine fa kawai yakeyi min yawa,yadan langwabar da kansa ya sake fadin,kin san kuma ban saba da irin wannan aikin ba..
Kilishi ta girgiza kai ,gobe ka shirya dan dama mahaifinka yayi min mgnr da dadewa..
nace masa mu dan baka lkc ka kara hutawa,toh tunda dai na lura kai kullum acikin aikin kake sai nayi tunanin dole ne kawai na fitar da rana da kaina.
Jalal ya gyara zaman sa yana fadin,toh umma zan shirya idan har hakan kike so,kilishi tayi murmushi yauwa dan albarka ..
Hansai ce ta shigo falon tana fadin,Allah ya kara maka yawan rai yanzun nan baiwar gimbiya khadija tazo da sako a fada maka..
Jalal yadan tabe baki,kilishi tace kai wannan yarinya da jaraba take..
Hansai tace, tace a sanar maka tana son ganinka idan babu damuwa..
Jalal baice komai ba ya mike yana kallon kilishi,umma bari na tafi..
Kilishi taji gaban ta ya fadi,cike da bakin ciki tace,ban gane bari ka tafi ba duka duka yaushe kazo?
Kodan kaji kiran matar ka ne?
Jalal ya murmusa,haba umma ke kinsan danki ai..
Magaji ne na saka a kira min shi tun dazu kuma na tabbata yana jan yana jirana acikin Fa'da..
Kilishi tayi murmushi,toh yi maza kaje ai na dauka rawar jiki kakeyi wa wannan figaggiyar yarinyar.
Jalal na murmushi yayi ficewarsa..
"Khadija ta kalli rabi tace,kin tabbata sakona yakai gareshi?
Rabi tace,wlh a kan kunnena hansai ta fada masa..
Khadija taja tsaki,yanzu a kalla anyi kusan 5hr amma shiru babu yarima..
Ta kalli rabi,jeki ki dubo min sashen surayya ko yana can..
Rabi tace toh ranki ya dade..
"Rabi na isa sashen surayya ta shiga tambayar bayin dake waje ko mai martaba yana ciki?
Duk suka tabbatar mata da cewa baya nan kuma ya ma dade bai zo ba..
Ta dawo ta sanar wa khadija duk irin ruhoton data kwaso..
Dariyar farin ciki khadija ta saki dan a yanzu ne ahankalin ta zai samu kwanciya tunda dai ba ita kawai yarima yake sharewa ba...