← Book details Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 53

Sashe 22

Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juwairiya tace ni?
Jakadiya tace kwarai ke juwairiya .
Ta gyada kai kafin tace,toh inna..
"Sannan ta nufi hanyar dakin..
jakadiya kuwa tabi ta da kallo tana mamakin yarda jalal yasan har sunan juwairiya kuma ya bukaci data tura masa ita gyaran dakinsa,Allah dai yasa ba abunda take zargi bane..

*************
Tana shiga dakin ta ware ido ganin irin girmansa ga furnitures masu shegen kyau da tsada,dakin ya tsaru iya tsaruwa..

     Motsin dataji ne a cikin toilet ya tabbatar mata da cewa yarima yana ciki..

  gyara daurin zanin ta tayi sannan ta sa'bi tsintsiyar dake hannunta ta shiga gyaran dakin cikin kwarewa..

Ba karamin mamakin dadewar yarima acikin toilet tayi ba,sai kace wani mace?
    Tana goge goge ne taji fitowar shi daga cikin ban dakin..

   Kamshin sabulun wankansa ne ya daki hancinta..
Ta juyo dan gaisar dashi..
Sai ganin sa tayi daga shi se wani dan towel ya daura a kugunsa..
  Tayi kasa da kai da saurinta..
Tace barka da safiya mai martaba..
Ya kura mata ido..
Sannan ya shiga tafiya wajen da kayansa suke yana fadin..

"Na lura baki dauki mgn ta da mahimmanci ba ko?
juwairiya tace,kayi hkr ranka shi dade..
Yayi shiru ya shiga shirinsa..
juwairiya ta juya dan ficewa ta basa waje..
Jitai yace...
"Ki zauna ki jirani"
Batayi gardama ba Ta samu waje ta zauna kasa..
Da gefen ido take kallon yarda yake shiryawar sa cikin nutsuwa da kasaita,ya shafa turare sun kai shidda (tadan matse baki,shiyasa yake kamshi abunsa)..

   Sai daya gama shirinsa tsaf sannan ya dawo ya zauna a gefen gado yace..
  Ina son anjima da daddare ki same ni a can wajen da muka hadu jiya..

Juwairiya ta gyada kai..

  Jakadiya ce ta rangwada sallama..
Juwairiya jiki na rawa ta mike ta koma bakin kofa ta tsaya.

Jakadiya ta shigo tadan kalleta tace, idan kin gama kije umayma na neman ki a waje..
Juwairiya ta gyada kai ta fita..
Jakadiya ta karasa wajen jalal tana fadin..

     AMALE bango madafar bayi,dama yanzu ne gimbiya kilishi ta aiko da sako a fada maka..
Jalal ya jinjina kai irin inajin ki..

Jakadiya tace,idan ranka shi dade bai manta ba a al'adar masarautar nan duk cikon sati biyu na sabon sarki matansa ne da kansu zasu fito suyi masa girki..
Dan haka ne yau sarauniya surayya zata shiga madafa da kanta ta girka maka abinci na gani na fada.
gimbiya kilishi tace a sanar dakai kada kaci komai har lkcn da za'a gabatar maka da abincin..
Jalal ya gyada kai yace,naji jakadiya, magajin ya iso ne?
Jakadiya tace,ya iso ranka shi dade yana can a falo yana jiran fitowarka..

************
"Juwairiya na fitowa daga cikin dakin yarima ta tarar da magaji zaune a falon..

  Ta duka har kasa ta gaishe dashi..
Magaji a sake ya amsa mata,harta mike zata fita yace..
Bakiji ba..
Ta dawo tace na'am..
Ya kurawa fuskarta ido..
Kafin yace,Ina tunanin kamar na san fuskar nan taki shekaru da suka wuce..

  Juwairiya se a lkcn itama ta dago tana kallonsa sosai..
  Kallon juna sukayi kafin a tare suka nuna junansu suna fadin..
MANGORO ko??????...

Murmushi sukayi wa juna..
Magaji yace,haba ko da ince ni na san nasan wannan fuskar ashe ke din ce..
Juwairiya tace,ai kuwa dai ni ce kaga ko ranar ban samu damar yi maka godiya ba..

Magaji yayi dariya ah ah ai ya wuce shekaru dayawa,kinsan kuwa tunda ga ranar ban sake ganinki acikin masarautar nan ba ,har nemanki nayi.
Juwairiya tace,Allah sarki ai lkcn ne na fara aiki a sashen zainaba shi ya sa.

Yana shirin mgn sai ga jakadiya tare da yarima sun fito..
  Jalal idonsa akan juwairiya,ganin murmushi akan fuskar ta yasa shi kallon magaji...
Shima din yaga murmushi akan leben sa...

  Daure fuska yayi yace..
Magaji muje ko?
Magaji yace mai martaba sai yanzu aka samu fitowar?
Yarima yayi banza da shi..dan yasan halin magaji da zolaya..

Jakadiya ta kalli juwairiya, ke baki je neman da ake mikin bane?
Juwairiya tayi saurin guduwa tabar wajen..
Jalal yayi gaba shima..
Magaji yayi saurin binsa a baya yana fadin..
Takawarka lafiya darzaza amalen sarakuna....

************
"Har suka shiga fada jalal bai kalli inda magaji yake ba..
Magaji kuwa zancen nata cinsa a rai..
Kasa hakuri yayi Yace,wai ka san kuwa mai martaba yarinyar nan itace dai wacce na taba gani shekarun baya..
Se lkcn jalal ya kallo shi..
Wace yarinyar?
Magaji ya washe baki..
Wannan me konannar fuskar mana da mukaje da ita chadi..
Nayi mamaki sosai ma da ta gane ni itama wlh..
Yarima ya tabe baki..yaci gaba da aikin gabansa.

***************
"Zainaba ta kalli zabba'u,tashi muje sashen khadija..
Zabba'u tace toh ranki ya dade..
"Sun shiga sashen suka tarar da goggon khadija tazo..

Zainaba ta gaishe ta sannan ta dawo falo ta zauna tana jiran khadija ta sallame goggon nata..

"Goggo ta kalli khadija,ina fata kin gane bayanin da nayi miki ko?
Khadija ta murmusa na fahimci duk bayanin ki goggo,kada ki damu zan samu wacce na yarda da ita ta shiga cikin bayin da zasu tayata girkin sai tayi yarda kika fada din..
Goggo tace yauwa nizan koma..
"Sun fito falo zainaba ta kalli khadija dake ta washe baki..
Yadai ko goggo tazo miki da wani albishir din ne?

muje zuwa👇
TEAM RUMFAR BAYI

[9/18, 3:22 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction )
Na Afrah bhai
Page 23
Wattpad @afreey101

_"@ Ayshat maghili,Admin TEAM RUMFAR BAYI group thanks for the effort love😚"_

*****************

"Khadija ta saki murmushi, ai abunda ma yafi albishir tazo min dashi..
  Zainaba ta gyara zamanta,Allah ko?sannu yar lelen goggonta..
Khadija ta kwashe da dariya..
Kafin tace,wai ina Mustapha ne?kinsan dai da an gama mgnr bikin su ya turaki da hamza kanki za'a dawo ko?

   Zainaba ta lumfasa,nima damuwata kenan wlh,kuma gashi kinsan halin abba da shegen son auren hadin nan daya burgeni ko kadan..
Khadija ta dan zungureta,ni ai auren hadin ba karamin taimaka min yayi ba,ke kinsan in ba dan shi ba ai bazan taba samun ya jalal dina ba..

Zainaba tace ke kenan,ni kin ganni nan ma kadaici duk ya ishe ni a cikin yan kwanankin nan, tun dauke min juwairiya da mijin ki yayi..
   Khadija ta tabe baki..
Kema dai zainaba da rigima kike, kawai ki bari sai lkcn auren ki yayi sai ki zabe ta a matsayin kyautar ki daga wajen mai martaba..
Zainaba ta sa dariya,wlh kin kawo shawara kawata..
Suka saka dariya a tare..

***************
"Umayma da kanta takai juwairiya har wajen surayya. .
Surayya ta kalle ta cike da kyamata tace..
Ki shirya zamu shiga madafa dake yanzu..
Juwairiya tadanyi mamaki amma ta share tace toh ranki ya dade ..

"Tunda suka shiga madafar suka soma aiki ba kama hannu yaro..
Surayya kam na hakimce akan kujera tana basu orders cike da isa..

  Har sun kusa kammala aikin juwairiya dake gefe ta jinjina kai ganin irin delicacies din da aka shiryawa yarima..
tana mamakin yarda mutum daya zai iya cinye duk wadannan abincin..
Abinci har kusan kala goma sha biyar?ina zai kaisu?
Aiko duk tsokali daya yayi a duka se cikinsa ya koshi..
Tadan tabe baki,ko dayake duk bajinta ce ake son a yi masa..

  Juyowar da zatayi kawai ta hango wata baiwa na barbada wani gari acikin tukunyar miya..
   Da sauri ta karasa wajenta..
Baiwar tayi saurin kakkabe hannunta tana kallon juwairiya da kananun idanunta tace,lafiya?

Juwairiya tace,me kika zuba acikin tukunyar nan yanzun nan?
Baiwar ta watsa mata harara tace,zargi kikeyi?toh babu abunda na zuba sai gishiri..tana gama fadin haka tayi gaba da sauri..

Juwairiya taji gabanta ya fadi..
Meye ta zuba a abincin yarima?ta tambayi kanta..
Hankalinta ne yadan tashi dan ita kam bazata so a cuci yarima ba...
  Umayma ce tazo tayi kiranta akan surayya tace su fara kai abincin can babban falon jalal..

****************
Rabi ce ta shigo sashen khadija da gudun ta..
A daki ta tarar da khadija a zaune gefen gado..
Ta samu waje a kasa ta zauna tana lankwashe kafafunta tace..

Albishirinki ranki ya dade?
Khadija ta saki murmushi bani in sha..
Rabi tace yanzun nan muka gama da mgn da wannan baiwar da muka saka aiki acikin bayin gimbiya surayya..

Kuma Ta tabbatar da min cewa tayi yarda muka bukaci tayi...
Khadija ta kwashe da dariya cike da murna sosai..
Tace naji dadin albishir din nan sosai..
Dan Babu wacce zata samu yabawar jalal sai ni ni kadai kuma...
Su uwar gida manya,dole ne asha kunya da wulakanci ayau..

Ta kalli rabi,Allah yasa dai ta zuba dan'tsamin nan dayawa acikin abincin dan bana so ko kadan girkin wannan matar yakai cikin cikin ya jalal dina..
Rabi tace kada ki damu ranki ya dade na tabbata tayi komai kamar yarda muka tsara..

***************
"Su juwairiya sun gama jidar abincin zuwa sashen jalal..
An gana gyara falon tsab kamar za'ayi wata uwar liyafa..

  Kuyangi biyu akabari sai surayya data sha wata uwar kwalliya tana zaune gefe tana jiran fitowar yarima..
   Kallon su juwairiya tayi,tace duk zaku iya tafiya..

A sanyaye juwairiya ta fito tunani duk ya cika zuciyarta..
Ta kasa yarda gishiri ne wannan baiwar ta saka a cikin abincin yarima,kodai wanine ke son halakar da shi?toh amma waye zai so cutar da sarki?
Da wadan nan tunane tunane ta isa rumfar bayi..

********
Sai da jalal ya gama shirin sa tsab acikin kayansa masu tsada sannan ya fito falon..

Surayya ta mike cike da kissa tace..
Sannu da fitowa sarkina..
Yarima ya jinjina kai yana shirin zama ..
Surayya tace,na tabbata zaka yabawa kokarina..
Yarima ya kalli jerin abincinan dake gabansa..
Lallai kinsa aiki,duk wannan abincin ina zan kai su?

Surayya tace,haka zakace ma kenan ki?
Jalal ya murmusa bai ce komai ba..
Surayya ta banka wa kuyangin harara,ku zuba masa mana kuka tsaya kallon mu..

   jiki na rawa sukayi serving din yarima first dish,wanda ya kun'shi (farar shinkafa me kayan lambu da miyar tsokar shanu,sai dafaffen kwai a gefe),
Jalal ya dauki tsokali cike da yanga ya tsakuri abincin yakai bakinsa..

    yamutse fuska yayi yana Matse baki jin wani irin mugun tsami ya gauraye masa baki..
Da sauri Ya kalli surayya a fusace..
Miye wannan?harshena kike shirin cirewa..!ko kashe ni kike son yi?
Chapter 22 · 0% Book details