Sashe 42
Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Babanta juwairiya yayi murmushi yana kare mata kallo dama zuciyarsa sai data bashi juwairiyar suce ake mgn..
Allah mai iko ashe asalinta na nan kasar kano inda yake rayuwa..
Yayi murna kwarai da ganinta a haka..
Juwairiya a take tayi sashen gimbiya amina dashi ta gabatar mata dashi..
Sannan ta saka sarki abu-turab ya yantar dashi..
Zo kuga murna wajen bawan Allah nan..
Washe gari da sassafe kuma ya shirya sai kasar daura wajen yan uwan sa..
*************
"Karshen wata yazo sarki abu-turab da gimbiya amina suna ta shirye shiryen taron zabar mijin juwairiya da za'ayi.
ita kuwa tunda aka sanar da ita sai taji wani iri dan kuwa ita ta riga ta san wanda take so ...
"Ranar gabatar da taron gimbiya amina da jamila sune gaba wajen shirya juwairiya..
Kai kace wata amarya ce dan ba karamin kyau tayi ba,ga kaya masu tsada da sarkar gwal data sha..
"Kilishi ta shigewa jalal gaba a wajen abbansa har ya amince da mgnr..
Ranar tafiya kuwa da kansa yace wa jakadiya ta shirya da ita za'a tafi,sannan ya dauki hamza dan a lkcn magaji yayi tafiya tare da waziri baya gari...
Lkcn da suka isa kasar kano,masarautar har ta fara cika da yaran sarakuna daga kasashe daban daban..
Jalal kuwa kallonsu kawai yakeyi dan kuwa yasan yayi musu zarra... ya siye zuciyar wacce suka zo neman soyayyar ta..
Abu-turab da kansa ya saka aka shigo da juwairiya cikin Fadar..bayi na biye da ita a baya ..
Wajen zama na musamman aka ware mata,jakadiya da su gimbiya amina na gefenta suma..
Lkcn da aka fara kiran sunayen (princes)din juwairiya addu'a kawai takeyi Allah yasa sarki jalal ya zo yau shima..
Duk wanda ya shigo idan jakadiya ta tambayeta se tace ah ah bai mata ba..
Gimbiya amina tadan rankwafo wajenta tace..
Juwairiya ki kwantar da hankalinki ki zabi wanda kika ji ya kwanta miki.
Ta gyada kai tana fidda ran zuwan jalal...
"Kamshinsa kawai taji ya daki hancinta..
Ta kurawa kofar shigowa ido..
Ai kuwa sai ga hamza a gaba jalal na bayansa jakadiya na biye dasu a baya..
Wani irin lumfashi ta saki da karfi..
Jalal kuwa kura mata ido yayi ji yake kamar yaje ya dauke ta daga inda take zaune..
Ganin yarda duk mazan dake wajen sai wani faman kallonta suke..
Shamaki na gabatar da sarki jalal jakadiya ta tambayi juwairiya (opinion ) dinta akan sa..
juwairiya ta saki murmushi sannan ta gyada kanta cike da tsananin kunya..
Ai a take fada ta hau kida aka hau busa algaita..matan bayi na ta ku'da wajen duk ya karade da kide kide..
Sarki abu-turab ya mike cike da kasaita da murna sosai..ya sanarwa jama'arsa shi Sarki abu-turab ya bawa sarkin daura JALALLUDEEN auran diyarsa sarauniya JUWAIRIYA ...
Ihu da shewa aka hau yi..
Gimbiya amina ta rungume juwairiya tana murna sosai..
Jalal baki yaki rufuwa zuciyarshi yaji wasai,sai gaisawa ake dashi ana shi murna..
"Da Yamma mai martaba Abu-turab ya saka aka gyara can sashen da karamin falonsa yake dansu juwairiya su kebence su fahimci junansu(date)
Gimbiya jamila taja juwairiya zuwa sashen ta..
Ta shiga bata shawarwari akan yarda ake fitar da lafazi me dadi da kuma yarda mace zata kama kanta a gaban (suitor)dinta..
Ta shiryata cikin kayan alfarma kafin hanne tazo suka fice..
"Juwairiya na kawowa gaban kofar falon jakadiya tayi saurin tarar ta..
Murna sosai sukayi da ganin junan su,juwairiyata rungume jakadiya tana tambayar ta ko ya su ummanta suke..
Jakadiya tace,kowa na nan kalau,ai babanki ma ya dawo..
Juwairiya tayi murmushi tace,nayi kewar su dayawa..
Jakadiya tace,ai kin kusa komawa garesu,yanzu ki shiga ciki yallabai yana jiran ki..
"Lkcn data shiga falon jalal na zaune a saman kujera cushion...
Ya dago ya zuba mata ido har ta samu waje itama ta zauna a kujera me fuskantarsa..
Irin fadin farin cikin dake mamaye a cikin zukatansu bata lkc ne..
Jalal yayi gyaran murya..
Ta dago ta kalleshi..
Jitai yace
Nagode....juwairiya
Tayi murmushi..
Kafin tace itama...
Nima haka...ranka ya dade
Jalal yayi murmushi..
Kafin ya sake fadin..
Kinyi kyau..
Ta dukar dakai se yayi tace...
Kaima haka...
Amma kin fi ni ai tunda kika siye zuciyar mazaje dayawa..
juwairiya ta murmusa..batace masa komai ba..
Shiru ne ya ratsa...
Se ji tayi yace...
Inaso a karshen watan nan ki tare ni a gidana..
juwairiya ta dan waro ido..
Da wuri haka..?
Jalal yadan langwabar da kai..
Nayi kokari ai..kinsan tun yaushe na fara mafarkin kasancewa dake ne?
juwairiya ta girgiza kai..
sai ka fada ranka ya dade..
Jalal ya daure fuska..
Bana son wannan "ranka shi dade"din fa..a tunani na mun wuce wurin..
Taja lumfashi..
Toh AMALE......
Ya saki murmushi ko ke fa..
Juwairiya tace,ina jinka toh..
Jalal yace tunda nayi gamo da gatar da fuskar ki nake mafarkin samun ki...
juwairiya dadi ya lallube ta..
Jalal ya mike cikin takun kasaita ya dawo kusa da ita zai zauna..
juwairiya tayi saurin matsawa tana kallo kofa..
Baka tsoron wani ya ganmu a haka?
Jalal ya zauna yana fadin..
Sai me?
juwairiya ta tabe baki..
Ya kamo hannunta ta bishi da kallo..
Zoben sa ne ya gani a babban dan yatsan ta.
Mamaki ya kamashi..yace..
Ina kika samo wannan zoben nawa?
Tayi dariya tace ka manta? wajen MAI KIFI..?
Jalal ya jinjinar dakai yana dariya..
sannan ya cire zoben ya fito da wani a cikin alhujinsa ya saka mata shi..ya sumbaci hannun nata..
Murmushi kawai takeyi..
Jalal ya kalleta..
Yanzu tunda kina da ikon sakawa shiyasa nazo miki dashi..
Tace..
Nagode Ranka..se kuma tayi shiru..tace auuu nagode AMALE ..
Jalal yace ni kuma fa me zaki bani?
juwairiya ta amshi zoben daya cire mata (nashi)
Ta maida masa a yatsansa..
Jalal ya kai hannunsa saitin bakin ta..
Dariya tayi dan ta gano me yake nufi..
Jalal ya langwabar dakai..
Kinsan abunda nake bukata a wajenki..
Juwairiya ta make kafada..
Kafin ta fakaice shi ta mike da sauri tabar falon tana masa dariya..
Murmushi ya sakar kafin ya mike shima yana fadin...
Zamu hadu ne yarinya...
*"Invitation"*
*Ana gayyatar duk fans din rumfar bayi zuwa daurin auren JALAL DA JUWAIRIYA gobe inshaAllahu...*😅😅
TEAM RUMFAR BAYI
*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 38
Wattpad @afreey101
*BIKIN MANYA*
**************************
""Lkcn da su sarki jalal suka sauka a kasar daura..
Labari gaba daya ya gama ya'duwa acikin masarautar...
Sarki jalal zai kara aure,kuma diyar sarkin kanon dabo ce amaryar tasa..
Labarin babu inda baije ba,da masu murna da kuma masu bakinci duk yakai garesu..
"""Umayma na samun wannan danyen lbrn ta garzaya sashen gimbiya surayya da saurinta ta sanar da ita abunda ke wakana..
Wayyo hauka ne kawai surayya batayi ba....Jalal zai karo aure?
Duk ta susuce ta birkice a lkc daya..
"Umayma ta kalla da itama din ke taya ta bakin ciki sosai tace, yau na shiga uku!umayma..
idan itama wannan ta shigo ta samu nata cikin ai na gama yawo...kinsan tuni gimbiya kilishi zata saka jalal sakeni!
Umayma tace...
ni a ganina ranki ya dade wannan malamin tsabbun gsky aikinsa baya wani Ci..
Toh ace tun kwanakin da muka zubawa gimbiya khadija wannan maganin a kofar sashenta amma shiru kake ji ba wani lbr?
Ciki ma sai girma yakeyi..
Surayya tace,gskyr kine umayma tunda ga aikin da yayi mana akan wannan baiwar har yanzu babu wani ci gaba a har wajen yariman ma..
Gashi yakumbo tayi tafiya..
Umayma tace,kada ki damu ranki ya dade mu koma can yanzu mu same shi ya fada mana dalilin da ya saka aikin da yake mana baya CI...duk dukiyar da muke bashi..
Ai kuwa shiryawa sukayi suka koma wajen malam na Sandamu..
Yana ganin su ya kwashe da dariya..
Umayma tace, hattara!
Malam yace,nasan ai zaku dawo ne..
Surayya tace,ban gane ba?wato da saninka kenan kake mana aiki baya Ci ?
Malam ya buga kasa yace,ai abunda yasa aikin ki baya ci sbd wannan asirin ne da kika yiwa wannan baiwar..
Surayya tace ban fahimce ka ba?
Malam yace,aljani daya ne kawai yake min aiki a yanzu bazan boye muku ba..
Toh na riga na tura shi da sunanki akan wannan baiwar,dan haka duk aikin da zan basa da sunanki bazai yi sa ba..
Surayya ta gyara zamanta,toh miye abunyi yanzu?dan ina damuwa sosai wlh..
Malam yace,sai mun warware wancan asirin kafin wani aikin Ya yiwu.
Umayma ta kalli surayya..
Surayya tace,toh me muke jira?ai tuni na manta da lbrn wannan baiwar malam,tunda ta bace tabar masarautar mu ai ni a yanzu na gama da shafin ta..
Malam yace toh angama..
A take ya warware asirin da sukayi wa juwairiya...
Ya sake kallon surayya..
Yanzu me kike so ayi miki?
Umayma ta dawo kusa da surayya tace..
Ranki ya dade me kike so ayi yanzu?
Surayya tace cike da tsantsar kishi,a hana auren sarki JALAL..
Umayma ta girgiza mata kai,ranki shi dade yanzu ke kenan haka zaki ta zama ba ciki bare goyo?
A tunanina haihuwar da kike nema tafi miki komai mahimmanci a wurinki yanzu?
Idan amaryar ta shigo basai mu san abunyi ba a lkcn..
yanzu kawai ya taimaka miki kema ki samu naki cikin ko ba haka ba?
Surayya ta jinjina kai cike da gamsuwa da shawarar umayma..
sannan ta kalli malam tace..
So nakeyi nima na samu ciki malam,ka taimaka min..dan ni kadai nake so na haifar wa sarki magajin sa..
Malam yace babu damuwa an gama ranki shi dade ..
Ya bata wani garin magani yace,kin ga wannan ki samu kiyi amfani dashi kamar sau biyu..zaki dawo kiyi min godiya..
Surayya da umayma murna ta kashe su..
Suka biya malam da dukiya me yawa suka tafi..