← Book details Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 53

Sashe 7

Rumfar Bayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ta tsaya tsak..
Cikin kasaita ya karasa gaban ta yana yatsine fuska..
Juwairiya ta zube kasa tana sunne kanta dan tasan babu abunda ya tsana kamar ganin fuskarta..

Dama...dama..uhm..na...
Yarima ya daka mata tsawa..
Ki bude baki kiyi min mgn!
Bana hane ki da nuna wannan fuskar taki a inda kika san ina nan ba?

Juwairiya tace,afuwa zanka shi dade uwar dakina zainaba ce ta umurceni da samo mata wannan furen ta nuna masa furen dake hannunta..
   Yarima ya tabe baki,ki ba'ce min daga gani...
yana gama fadar haka ya juya yai tafiyar shi..
Juwairiya tabi bayansa da harara sannan ta mike ta kakkabe jikinta tayi gaba.......

***********************
Pls share
Comments
And
Vote
[9/18, 3:13 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
NA Afrah bhai
Page 8
Wattpad @Afreey101

*************************

'Tana shiga sashen zainaba ta tarar da ita a tsaye sai safa da marwa takeyi.
Juwairiya ta mi'ka mata furen dake hannunta, ta amsa tana sakin murmushi me kayatarwa,gaskiya furen nan yayi min kyau sosai,se de akwai wata matsalar kuma juwairiya.. ta karashe mgnr kamar zatayi kuka..

     Juwairiya tace,matsalar me kuma ranki ya dade ba dai har sun tafi din ba?

'Zainaba ta girgiza kai,dazun ne fulani ta aiko min da sakon cewa kada na fita ko ina  zata aiko min da wata mai magani ta dubani akan yawan ciwon cikin nan da nake fama  dashi ,kin kuma san halin fulani, har fa wani bawa ta ajiye a kofata wai dan kada na gudu sbd bana son magani..yanzu ya za'ayi na fita kenan?

         'Juwairiya tadanyi tunani kadan sannan tace inda ranki ya dade ba zata damu ba ina da shawara..
Zainaba tace da gaske?
Juwairiya ta gyada kai ..
Zainaba tace fadi muji..
Juwairiya tace ko naje na sanar dashi bazaki iya fitowa se shi din yazo nan..

Zainaba ta ware ido...
Ah ah bana so yazo nan juwairiya..ta karashe mgnr a shagwabe tana kallon juwairiyar..
Can kuma tace,yauwa! Tasa hannu taja juwairiya zuwa dakinta...

'Cire.....ta fada kai tsaye..
Ciki da mamaki juwairiya ke kallonta..me zan cire ranki shi dade ?
Zainaba ta nuna kayan dake jikin juwairiya..cire kayanki ki bani..
A tsorace juwairiya tace,kiyi hakuri ranki ya dade amma.....

Zainaba tayi dariya,ba ina nufin ki tu'be min ba dan naga jikin ki ba..
Ah ah ina so ne muyi canjen kayane kawai kin ga babu wanda zai san ni ce na fita bake ba ko?

    Juwairiya ta gyada kai,wato wayo zakiyi wa fulani ko?amma idan aka kama mu fa?ni gsky tsoro nakeji..
Zainaba ta murmusa kada ki damu bazan jima ba zan dawo,kedai kawai cire kayan ki bani..

Juwairiya a sanyaye ta cire kayanta,zainaba ma ta cire nata ta bata..
Juwairiya tabi kayan da kallo,ina zata iya saka wadan nan kayan?
Ta girgiza kanta,ranki shi dade bani da matsayin da san saka wadan nan kayan..
Zainaba ta harare ta,amsa!
Kuma umurni nake baki daki saka su yanzun nan!
Juwairiya ta amsa a tsorace..
Tana kallon zainaba bata nuna wani kyama ba ta saka nata kayan tana dariya tace,lallai ke kam wannan kayan naki ashe walawa kike yi sosai..(ta fada tana jujjuyawa cikin katoton rigar juwairiya )

Juwairiya dai da kallo kawai take bin ta,a sanyeye ta saka kayan itama atamfa ce riga da zani sai wata alkyabba ja da ruwan madara,ita kanta tayi mamakin yarda kayan suka amshe ta....
Zainaba tabi ta da kallo,lallai juwairiya Allah yayi mata baiwa dayawa,se de kawai yanayin data tsinci rayuwarta ne...
     Zainaba tace,toh ni na tafi,ta dauki furen ta tana sake fadin,babu wanda zai gane ni ce,ta saki murmushi tayi gaba..

juwairiya ta zauna a takure tana tunanin idan wani ya shigo fa yanzu tasan tabbas kashin seya bushe..
    Motsin dataji ne a waje ana sanar da shigowar turaki yasa ta saurin komawa shinfidar zainaba ta kwanta hade da juya bayanta ta rufe rabin fuskarta..

   A tsanake ya shigo falon cike da takonsa yana mamakin rashin ganin juwairiya da bayyi ba..
    Yan matan fulani naji mun kusa hutawa da jinyar ciki ko?dazu fulani ke sanar min an kawo me magani daga cikin katsina..

     Juwairiya tayi wiki wiki da ido,bata so ko kwakwaran motsi tayi turaki ya gano ita ce..
Turaki ya zauna yana mamakin shirun da zainaba tayi masa..
To wai ko barci take ne ?
Yana wannan tunanin ya mike har ya kai bakin kofa yace, ko ina kawarta ta tayi yau oho..

   Juwairiya najin fitar sa ta sauke ajiyar zuciya sannan ta mike zaune,se a lkcn ta nuna da inda take zaune(wato akan kilisar zainaba ),ta mike da sauri tana sake kallon shigarta,tabbas bata taba saka kaya irin wannan ba,ta dan murmusa zataso ummanta dasu jakadiya su ganta a cikin irin wannan shigar..
Wani tunani ne yazo mata..
Da sauri naga ta shige dakin zainaba ta dauko mirror tana kallon kanta..

    Ita kanta wani lkcn idan taga fuskar ta a haka tsoro take bata..
Hannu tasa a hankali ta fara goge tabon har kyakkyawar fuskarta ta bayyana..

    Ta kurawa fuskarta ido..
Motsi taji daga falon..
Da sauri ta mike jiki na ba'ri ta fito zuwa falon tana leke...
Sai ji tayi bawan dake waje yana daukar izinin zainaba  dan zagawa bayan gida..
  TOh!
Kawai ta fada a da'ke sannan tace,wai ina zainaba ta tsaya ne?(tayi mgnr kamar ta fashe da kuka)
Gani nayi Tadan jawo hular alkyabbar ta rufe rabin fuskarta tana fadin,dole ne naje na dawo da ita tun kafin asirin mu ya tonu,ba tare da wani tunani ba tayi waje da saurinta..

**************
'Surayya na tashi daga barci taga wayam babu yarima a dakin.
tsaki taja cike da takaici,wai yau itace gimbiya surayya ake wulakantawa har haka,wulakancin ma wai daga namiji..

Ta juyar da kwayar idonta tana tuna irin  samarin dake tururuwa a wajen neman aurenta,amma gashi sbd wata tsohuwar abokantaka dake tsakanin mahaifinta da mahaifin yarima jalal an kawo ta nan se wulakanta ta akeyi..

      Ta kalli shinfidar gadonsu cike da takaici,ta tabbata duk bayin da zasu shigo da kuma yan uwanta da zasu zo mata bankwana toh gulma ce zata kawo su dan  ganin  yarda daren farkon ta da yarima ya kasance...

Abu daya data tsana a rayuwarta shine a ga kamar bata isa ba (she hates pple downgrading ha),bata son ko kadan a raina ta,sbd ta mallaki komai a rayuwarta, tana da kyau,gata diyar sarki,yanzu kuma matar yarima me jiran kujerar mulki...

Wani tunani ne yazo mata..
Ai da sauri Ta mike da ta tube duka kayan dake jikinta tas..
Sannan tasa hannu ta hargitsa shinfidar gadon,ta dauko yar karamar wuka dake cikin tiren fruits ta hawo kan gadon tasa wukar a finger dinta tana runtse ido ta tsakawa kanta wukar kadan'sannan ta samu jinin ta dake ta di'qa ta shiga shafawa a wani bangaren gadon....

       Yamutsa gashin kanta tayi dayasha gyara sannan ta ja bargo ta rufe kanta tana kuka kasa kasa..(yarima yayi kadan ya jawo mata raini,dolene ta nuna masa wacece SURAYYA)

   'Bayi ne tare da yakumbon ta suka shigo dakin da jakadiya a bayansu..
   Ganin halin da take ciki yasa duk suka saki murmushin murya suna gyada kai cike da gamsuwa..

Yakumbo ta karasa wajenta tana dago da ita zuwa jikinta..
Sannu surayya,sannu UWAR GIDAN YARIMA JALALLUDEEN...
ai duk mace idan tayi aure dolene ta fuskanci wannan  daren farin cikin,amma daurewa zakiyi kinji?
Surayya dake sunne kai ta gyada kai,yakumbo ta ciro zanin shinfidar  ta mikawa jakadiya dake ta gyada kai cike da farin ciki,lallai yarima an  girma...

     Jakadiya na amsar zanin da saurinta ta karasa sashen gimbiya  kilishi dan aiwatar da umurninta..

    Uwar soro na ganin jakadiya ta karaso sai washe baki takeyi..
yasa tayi sauri wajen fadin isowarta cikin kirarinta masu tsada...

    'Gimbiya kilishi na a kishin'gi'de jakadiya ta shigo tana bayyana mata zanin dake hannunta..
Wani irin murmushi ta saki..

Jakadiya tace, gimbiya uwar gidan mai martaba, ina miki albishir da a daren jiya yarima ya zama cikakken namiji....
   Kilishi ta gyada kai cike da gamsuwa tace,wannan albishir naki jakadiya ba karamin farin ciki ya saka ni ba,dan haka ina so ki samu shamaki a baki azurfa goma a matsayin Tu'kwicin ki.......
   Gu'da jakadiya ta saki hansai dake zaune kusa da kilishi na tayata sai murna sukeyi..ni kuwa afrah nace 'Oh"

***********

"Mustapha ya dade tsaye a babban zaure yana jiran zuwan zainaba..
Shiru har sai da abokinsa yazo ya sake sanar dashi  cewa shi kadai ake jira su tafi rana keyi...

  Ya cire rai kwarai da zuwanta har ya juya zai fito ya hango wata ta tunkaro wajen..se de shigarta kawai ya nuna masa ba ita bace ba..
     Yana fitowa tana karasowa wajen..
Ta yaye lullubin dake kanta tana sauke lumfashi sosai sbd tsabar gudun data sha..

Mustapha cike da mamaki yana bin ta da kallo,wai dama kice haka?
Zainaba ta gyada masa kai sannan ta fito da furen data boye cikin riga ta mika masa..

   Wani irin farin cikine ya lullube sa..
Yasa hannu ya amsa sannan yace..
Nagode kwarai da kika amshi tayin soyayyata,ina miki alkawari akan bazakiyi dana sani ba gimbiyata..

"Zainaba ta rufe fuskarta cike da kunya tana murmushi..
Mustapha yace,duk da baki damu da sanin sunana ba bari ni nayi karanbanin fada miki..

Zainaba ta bude fuskarta tana kallonsa kafin tace,kawai ka riga ni fada ne amma nima yanzu nake shirin tambayarka..

Mustapha ya gyara tsayuwarsa, kice ma har tunanin mu iri daya ne kenan ko?
Zainaba ta murmusa kawai..
Yace,toh sunana Mustapha dan gidan WAMBAN kano..ina fata matsayina yakai da yin soyyaya da diyar sarkin daura...
   Zainaba tace,kwarai kuwa..
Yace toh nagode....
A nan suka hau yar firar su sama sama...

*********
'A wajen juwairiya kuwa sauri kawai take bugawa,har tazo hanyar da zata kaita inda su zainaban suke amma sai ganin jama'a tayi sunyi yawa a wajen sosai..

Ta cije yatsan ta,yanzu ta ina zata bi kenan?
Hanya da'yace kawai zata iya kaita kuma sai ta bi ta sashen samarin gidan,wato sashen su turaki kenan..
Kafada ta daga lkcn data karasa sashen taga babu kowa a wajen,ta saki lumfashi tace, ina tunanin duk suna fa'da ne...

   Tafiya take cikin sauri kanta a kasa..
Batayi au'ne ne kawai taji taci karo da mutum..
  A tsorace ta dago da kanta.....
Chapter 7 · 0% Book details