Sashe 9
Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wannan karon za e ba nasa bane bare ya miki za en tumun dare ya za a miki ahlil fukara'u" "To Umma bari na akko mayafi, ai ni na matsu na gama iddar nan ko na fara wankar ku en zawarawa in sake kayan sawa na kece raini" "Ko ni uwaki ai sai kin sake mini sabon zubi saboda in zawarawan naki za su shigo mu gaisa kar su ganni a tsumma" Cewar Umma tana dariya. "Ai dole ki aura manyan lasa-lasai. "Kai yaro in ji wa ko ba fa i sunansa ba" Umma ta ce tana murmushi don kunnuwanta so suke kawai su ji an ce Alhaji wane ne, amma sai dai kash an samu akasin lissafi don cewa ya yi. "Wai in ji ABBAS..." Ku biyo ni don jin ya za ta kaya... 09013181851 [1/5, 8:57 PM] Sadiya Abdulrazak: https://chat.whatsapp.com/Duq93sLLgjCKV0uuildAH1 IYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH *GARGAGA Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 3 *SALIMAH* Sai da ta yi sallar ishsha'i sannan batun EESHART ya fa o mata, ta yi mamaki matuka na ganin bata kira ta ba wayar ta akko ta duba bata ga miss call ba. Shiru ta yi tana ta mamaki a ranta duk tunaninta EESHART in za ta yi ta kiranta suna labarta abin da ya faru tun da dai bata gama bata labari ba ta ce ta bari za su yi waya idan ta je gida. Kawar da tunanin ta yi, ta bu e data ta hau whatsapp, sakonnin da suke ta rige-rigen shigowa ne ta jira suka gama shigowa, dubawa ta yi ko za ta ga EESHART ta mata magana amma ta ga tun maganar da suka yi lokacin tana gidan ABBAS amma ko igon magana bata mata ba, bayan ta saba ko yaushe suna tare a online idan ta mata magana ta ga bata nan ta kira ta idan bata da data ta saka mata amma dai yau ta rasa dalilin hakan sai dai ta mata uzuri a kan ko wani babban dalili ne ya mantar da ita farin cikin da take, cikar burinta wato sakin da ABBAS ya mata a yau Ganin tana online sai ta kara shan ruwan mamaki amma bata dogara da mamakin da ta shayar da ita ba ta je ta mata magana. Hi ta ce mata amma shiru-shiru sama da minti goma bata ma bu e sakon ba bare ta mata replay. Kara mata magana ta yi cewa kawata ya na jiki shiru, sama da minti biyar bata bu e ba abin ya yi wa SALIMAH ciwo amma dai sai ta dake har lokacin tana jiran ta fara ji daga gare ta duk da tana ganin nata online, bayan ta saba tana hawowa wani lokacin idan ita EESHART ta bar mata sako sai ta kara cewa ina ganin ki online fa matar manya. Basarwa ta yi ta fara scrolling ganin sakonnin group in kawayen su da suka bu e message yana ta shigowa, sai ta shiga group in nan ta ga sun baja kolin hira har da EESHART in yawanci hira ce ake ta zaman takewar auratayya kowacce tana bada labarin mijinta da kulawar da yake bata da yake duk yawanci matan aure ne sai anmata kalilan. Taggin in EESHART ta yi ta ce na ajiye miki sako a pc kawata na ga baki duba ba har yanzu. Ok kawai ta ce suka cigaba da hirarsu. Jim ka an ta duba amma ta ga EESHART bata duba ba har dai ta fara tunanin ko wani laifi ta mata amma iya tunaninta bata gano komai ba. Ta kasa duba sakon kowa kawai sai dawuwuri take abin da EESHART ta mata ya tsaye mata a rai. Sunan kawarta ta kamo BASEERA wacce har ta manta rabon da su yi magana saboda ita BASEERA tana fa a mata gaskiya tana nuna mata ta yi hakuri ta zauna a akinta tun da ABBAS yana son ta kuma yana kyautata mata, shi arziki na Allah ne in da rabo wata rana sai ta ga ya yi arzikin. Wannan ne ya sa kullum suke fa a da ita saboda tana ganin ita ma bakin cikin ta fito ta auri mai ku i take mata tun da ita ma BASEERA talakan take aure sai dai shi mijinta ya fi ABBAS rufin asiri. Sallama ta mata amma sai ta ga ba ta oline datar ta kashe ta sauka ma daga whatsapp "Ki zubo tuwo ki ci SALIMAH, azu na ce mu ci azu kika ce sai an jima idan ya huce ba za ki ji da insa ba" Umma ta ce tana tattare kwanuka. Da to ta amsa mata tana zuwa ta zubo ka an amma tana sakawa a baki sai ta ji anon dai sai a hankali ba kamar miyarta ba ta saka ishashshan magi duk tsiya kuma dole ABBAS in ya kawo. "Umma ki bani magi na kara lami na ji miyar" "Haba SALIMAH to ya kike so ki ji ni da na gama ci yanzu ban ji wani lami ba, amma ga gishiri nan ki kara saboda maggi dai kin san tsada yake ni kuwa da ba wanda zai kawo mini gare ni ba komai ni nake siya da sana'ar da nake yi" "Ai kin kusa hutawa don har mai girki zan aukar miki idan na auri attajiri" Dariya ta yi ta bata maggin guda aya ta saka sannan ta ji dama-dama. Sai da ta gama bayan sun kwanta Umma a saman gado ita tana katifa a kasa, wayar ta akko ta sake hawa whatsapp amma har lokacin babu sakon EESHART. Sai dai BASEERA ta amsa mata sallama har tana tambayarta lafiyarta. "BASEERA yau dai ABBAS ya yanke igiyar aurenmu na huta da alakakai" "Subahanallah! Yanzu sai da kika yi yadda kika yi kika kashe aurenki, darajarki da kimarki akin mijinki, wannan rayuwar da ake ciki a irin dagulallan zamanin mai cike da ru u samun miji managarci ma wahala yake, maimakon ki rufawa kan ki asiri ki rabu da tunanin ru in duniya mijin ki yana son ki yana kyautata miki sai abin da kike so yake yi ki juya shi kamar waina a tanda, mai mace take nema da ya wuce abin da kika samu? Wasu fa malamai da bokaye suke bi don su samu wa annan abubuwan amma ke ba boka ba malam Allah ya mallaka miki, amma shi ne kika yi watsi da ni'imar Allah, kina bin gurguwar shawarar zuciyarki da ta kawaye suna ora ki a keken era, ke baki san RU IYAR IGIYA kike kamawa ba... "Dakata! BASEERA wai ce miki na yi na gama aure a duniya ne? ". "Baki ce mini ba amma dai ai auren mai ku i ne da kike kwa ayin yi ya sa kika raina naki mijin, shin wai ke baki san cewa ku i ba su ne rayuwa ba, ku i ba su ne farin ciki ba, to wallahi mafi yawan wanda suke cikin daula wasu basu da kwanciyar hankali, ga komai sun samu gida mai kyau mota su hau wacce suke so ku in su yi facaka, ga sutura sai wacce suke so ga an aiki nan bila adadin suna musu hidima su ci mai kyau su kwanta mai kyau, amma da za ki duba rayuwar gidan cike take da tarin matsaloli da kalubale, wata da za a bata za i in dai za ta auri talakan da za ta samu kwanciyar hankali to ta gwammace ta bar daular da take ciki. Wata mijin ma ba shi da lokacin ta wata ta yi hannun riga da farin ciki abubuwa dai barkatai ga su nan ke idan ana cin aure ba a tona cikinsa, amma ke ki raina taki ni'imar kike hangen na sama da ke? Idan mutum yana son ya gane ni'imar da Allah ya masa to kar ya dubi na sama da shi ya dubi na kasa da shi, shi inda mutum yake buri da kwa ayin samu ai hangen dala ba shiga birni bane, akwai abubuwa barkatai da baki ba zai iya fa insu ba" Gaba aya ran SALIMAH ya gama aci kwata-kwata wannan dogon lissafin da BASEERA take mata shi ne ya sa take raba hanya da ita, shi ne dalilin da ya sa ko magana bata san fa a mata ita kullum nasiha tamkar malamin da ya hau minbarin wa,azi sai ka ce ita ce mikiya mai hangen nesa. "Fakyakul kairan auli yasmut" Shi ne abin da SALIMAH ta tura mata bayan ta gama jin dogon voice Haushi ma ya sa ta kashe datar ta sauka, tun da har lokacin ita EESHART bata mata replay ba, dama a rashin uwa ne ake uwar aki, da a ce EESHART ta mata magana sun cigaba da tattaunawa da babu abin da zai sa ta ta o ustaziyar wannan wato BASEERA dama EESHART in ce tasu ta zo aya don ko wasu daga cikin kawayenta haushin ta suke ji a kan yadda ta auri kyakkyawan miji managarci mai cikar haiba da kamala yake son ta da nuna kulawarsa a gare ta wannan ya sa wasu duk suka janye jiki daga gare ta don kowacce so take dama a ce ita ce ta samu wannan damar. Suna ganin sun auri an dukununu ga baki ga bakar zuciya amma ita ta samu fari mai farar aniya da kyakkyawar zuciya. *WASHE GARI* Tun da asuba da Umma ta idar da sallah ta hura wuta ta ora katuwar tukunyar ruwan koko. Ita kuma SALIMAH tana idar da sallah ta koma ta kwanta. "Ke SALIMAH tashi kike iza wutar kokon nan idan ya tafasa ki dama, zan tafi in kai marka en kosan nan" Umma ta ce tana a mata duka a kafa. if ta yi tana jin wani acin rai in akwai abin da ta tsana a duniya bai wuce a ce an hana ta bacci ba, da a gidanta ne