Sashe 41
Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ce. "FARUQU idan ban ora maka nauyi ba don Allah mi a Hauwa'u makaranta mai adaidaita sahunta bai zo ba(SHIN KIN KARANTA LITTAFINA AN ADAIDAITA SAHU? IDAN BAKI KARANTA BA AN BARKI A BAYA DOMIN NA ATA LOKACI SOSAI WAJEN AYATA LABARIN IYA ANSAI DA JABIRU SUN TAKA MUHIMMIYAR RAWA A LABARIN DA NAIRA 500 KACAL ZA KI SHA KARATU). Kafin FAROUQ ya ba Baffa amsa ABBAS ya yi karaf ya ce. "Babu wani ora nauyi Baffa ai sai a mi a ta bari na kar i mukullin sai na mi a ta" Shi kansa ABBAS bai san maganar ta fito ba ji ya yi tamkar an fusge ta. Sosai Baffa ya ji da in cewa zai kai ta, ita ma sai fuskarta ta washe jin za a kai ta ba tare da ta makara ba. FAROUQ sosai ya yi arfin halin danne dariyarsa don ya gane kishi ne ya sar e ABBAS shi ya sa ya ce shi zai kai ta da alama ba ya son ta hau bayan machine in kowa. "Bani mukullin" Ya fa a cikin majewa don ya ga FAROUQ in yana satar kallon Baffa da HAWWA yana masa wani murmushin na gano ka. Shi kuma abin da ya sa ya maje ya san har kullum dai zancen gizo ba ya wuce na i wato FAROUQ yana zarginsa da kamuwa soyayyar HAWWA wanda har yanzu yake aryatawa. Tada machine in ya yi ta hau suka fara tafiya Baffa yana aga mata hannu tare da fatan dawowa lafiya ita ma hannun ta aga masa daga nan suka tafi FAROUQ kuma ya shiga bincikar wayar ABBAS zai auki lambar kafin ya dawo masa da machine in ya wuce gida. Tu i ne yake yi mai cike da nutsuwa, amshin turarensa da nata yana dakar masa hanci, yadda suke tare a machine in sai yake rawa a zuciyarsa ina ma su cigaba da kasancewa a haka, da in da yake ji a ransa sai ya ji tamkar bai ta a riskar kansa a cikin irin hakan ba. "Mai ya sa bakya sa ni abi idan za ki je school?" ABBAS ya tsinci kansa da tambayar da shi kansa bai san ya yi ba. abi kuma Yaya?" "Au ashe ba islamiya ba ce " Ya ce cikin wayancewa yana tuhumar kansa dalilin da ya sa ya yi tambayar ma. A dai dai titin da za su tsallaka wanda zai sada su da school in su HAWWA suka hango Yaya Usman ya taho, ganin HAWWA a bayan machine ABBAS yana ja ransa in ya yi dubu ya aci shi a haka nan ma ya tsani ABBAS amma shi ne don gigiwa ya akko masa abar aunarsa a machine, wacce yake fata da burin mallaka a matsayin mata kuma uwar a. A fusace ya taho har yana neman karawa wani mai napep, shi kuma ABBAS sai a lokacin ya gan shi haka ma HAWWA. "ABBAS kai ABBAS" Ya shiga wala masa kira tun kan ya araso. an dakatawa ABBAS ya yi tare da gangarawa gefen titi ya tsaya, shi ma Yaya Usman in gangarawa ya yi inda suke ya sauka daga nasa machine in ya tunkari ABBAS rai a mugun ace sosai a fusace yake ta yadda ABBAS yake mamakin dalilin tsayar da su da kuma dalilin acin ransa. HAWWA jikinta ne ya auki mazari don ta san yadda yake a fusacen nan dakyar ne in ba rashin mutunci zai yi wa ABBAS ba sosai ta ji damuwa ta sar e ta lokaci guda don bata son abin da za a atawa ABBAS rai kamar yadda ta lura shi ma yanzu ba ya son a ata mata... *SALIMAH* Yana kai wa inda nan ne ta san ya kai arshen magan kai kawai ta aga masa ta tashi da an gudu tana tashe bakinta jin kuka mai arfi ya wace mata, ofar ta bu e ta fice takalmanta ma a hannu ta ri o su, shi kuwa Alhaji kafa a ya aga alamar can ta matse mata, sauran matan sallama suka masa suka kama gabansu. Baram ta banka ofar da za ta sada ta da falon nata jifa ta yi da takalman a falon tana kallon tangameman falon da ya gaji da ha uwa da tsaruwa amma wai ake mata batun zai zama mallakin wata a gobe, bayan an uwa da abokan arzi i nan suka kawo ta awaye duk sun san nata ne amma saboda cin fuska za a ce wai ta bar wa wata bayan ta san yana da halin da ko gida ari zai iya siyawa amarya amma saboda kwamacala zai ce a part aya za su zauna shin wane irin miji ta aura? Fiiii ta hau sama ta je ta shiga arewa ko ina kallo tana kuka wiwi tabbas akwai tashin hankali a kalamansa da dokokinsa amma duk abu ne wanda a duhu yake ba wani zai gani ba sai dai in ita ta fa a wannan batun za aki kuwa dole duk wanda ya zo sai ya gane tun da dole za a ga amarya ba ma wannan ba wa za ya fa awa za a mata kishiya? Bayan ta yi wa mutane kurin cewa daga ita Alhaji Tahir ya rufe ofa ita ce ta gaban mota ita ce ta shiga taro amma kwatsam a ce a kwana uku rak wannan matsayin ya zagwanye? asan ta sake sakkowa kamar wata mahaukaciya sabon kamu duk ta zauce ta firgice ita gaba aya ta ru e da rabon part in nan da aka ce da yake duniyar ce a gabata ita dokokinsa za ta iya fatali da su amma batun part in nan tamkar cewa ya yi ta raba ranta biyu ne ta bada rabi, part in da ko Ummarta bata zo ta gani ba amma za a raba a ba wata bayan su sauran matan gidan kowacce gashin kanta za ta ci. "Ko dai hannu aka saka mini? Ko dai shiga tsakanina aka yi da shi' Wani sashe na zuciyarta ya jefa mata tambaya. "Waye zai shiga tsakaninku kawai butulci ne irin ma maza shi dama namiji ai butulu ne a wani aulin ba an goyon baya ba" Wani angaren na zuciyarta ya sake sa a mata hakan. Baki ta dam e tana jin ruwan hawayenta yana biyowa ta bakinta yana sauka ha arta wai ita SALIMAH ce yau namiji ya saka ta zubar da hawaye a cikin kwanakin cin amarcin ta amarcin da bai ciwu bama, ba ma wannan ba yau ne kwanan nata na uku zai cika amma mai zai yi da daren nata na yau wanda ya rage waya aya tal? Ko dai ita ce ba ya son kasancewa tare da ita ta rasa kalar tunanin da za ta yi hakan ya sa take zaune tamkar mutuntumi ko gunki ta da e a wajen ita kanta bata san iya awannin da ta kwashe a wajen ba a atshe ta lalla a ta koma bedroom in da yake asa inda aka ajiye ta jiya ta zame ta kwanta ba wai don ta rintsa ba sai don duniya ta rasa mai za ta yi ta ji da i a ranta. Ta yanke hukuncin ta za asa saboda idan ta za i sama duk wanda ya zo zai gane an raba part in ta biyu tun da dole za su ga amaryar a nan kuma dole a jefa mata ayar tambaya. Tamkar ta i-ta i haka take kwance garau har aka faran assalatu dakyar ta lalla a ta tashi tana jin wani zafi a jikinta kamar zazza i, alwala ta yi ta yi sallah sallar da ita kanta tana karatun sallah amma bata san mai take karantawa ba saboda tunani ya cunkushe mata walwa maimakon ta mayar da hankali ga sallaar ta yi addu'ar neman mafita amma haka ta sallame ta tashi ta koma makwancinta. Wayarta ta akko iphone 16 in tana arewa wayar kallo tana tuna android inta ta gidan ABBAS wacce bashi ya ci ya saya mata don ya faranta ranta shi kuma yake ri e keypad amma bata gode masa ba a raine ta kar a ga shi yanzu tana fa wayar da ake yayi sai dai kash! Cukurku un al'amuran da suka taru suka yi wa rayuwarta awanya sun disashe duk wani walwalarta. Sunan Umma ta kamo tana son kiranta ta sanar mata matsalolin da suka kunno kai a sabon gidan auren da suka ci buri amma tana tsoron ran Ummar ya aci saboda tana aunar Ummarta a duniya ota ka ai ta rage mata tate suka kasawa su tsare amma kuma dole ne ta fa a mata tun da ita ce mahaifiyarta kuma an magana sun ce abin da babba ya hango yaro ba zai hango ba ganin arfe shi sai kuwa ta doka mata kira. Umma da bayan ta idar da sallah ta zubo ruwan zafi a plask ta ha a kakkauran shayi da ya ji madara da milo tana zaune tana ha awa da biredi tana lumshe ido ga aran jannareton da wani matashi yake zuwa ana tada mata gida sabo ga plasma tangamemiya abun sai wanda ya gani, kiran da ya shigo wayarta ne ya sa ta tashi ta akko ganin SALIMAH sai murmushi ya su uce mata. "Yarinya mai goshin arzi i auren mai ku i da da i duk rayuwarmu ta sauya, bare yanzu in kika bararraje ai duniya sabuwa mu gaba ta kaimu gobarar titi" Shi ne furucin Umma bayan SALIMAH ta danne kukan da ya taho mata ta yi sallama, shiru ta yi tana tuna wannan zancen bai tabbata ba. "Umma mun kama RU IYAR IGIYA" Ta ce tana fashewa da kuka. "SALIMAH RU IYAR IGIYAR uban me wai?" Ta tambaya tana dangwarar da kofin shayi ya tuntsure, don a tunaninta SALIMAH ta jaza musu salalan tsiya ne wato ta saka ya sake ta. "Umma aure za a aura masa yau" "Aure dai da na sani SALIMAH shi Alhaji Tahir in ne zai miki kiahiya bayan na cikin gidan da kika tarar?" Kwashe komai ta yi ta fa a mata amma banda dokokinsa da maganar haihuwa. "Sakaran banza to ta Allah ba tashi ba da ya i saninki a mace kansa ya yi wa ai ya yi wa arzi i dundu kuma zai dawo ya same ki