← Book details Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 43

Sashe 34

Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

NA MAMAN AFRAH *First Class Writers Asso* Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGA Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 13 *ABBAS* Tun da HAWWA ta bashi ha urin nan ya kasa mantawa da abin da ta masa, domin wannan abin da ta yi ya nuna ta san kima da muhimmancin an adam wanda ba kowa ne ya san hakan ba bare har ya bada ha urin laifin da ba shi ne ya yi ba, galibin mutane ko da a ce su suka maka laifi to baka isa su ce ka yi ha uri ba. Wasu suna ganin hakan ci baya ne yayin da wasu suke ganin wanda za su ba ha urin bai isa su furta masa kalmar ha urin ba kuma ba komai ne yake saka hakan ba illa girman kai. HAWWA ya furta hakan a fili yana son sanin dalilin da ya sa bata zama mai girman kai da agawa ba irin na wasu an matan zamanin da aka fi samu yawanci idan suna daidai shekarunta ake samun su da gigiwa rawar kai da kuma raini amma kuma sam ita yanayinta ya nuna ba haka bane. "ABBAS yarinyar nan ta baka ha uri ne kasancewar Yayanta ne ya maka laifin ba don wani abu ba" Wani sashe na zuciyarsa ya kissima masa hakan. Iska ya fesar daga bakinsa yana mai son mantarwa da duk batun ta dama kawai ta burge shi ne sannan ha urin da ta bashi ya wanke masa kaso mafi yawa daga cikin acin ran da Yaya Usman in ya saka shi ba tare da wani waran laifi ba bayan yana ganin za su yi sa'anni da Yaya Usman in tun da a alla shi ma ba zai wuce shekaru 30 ba. Juyi ya yi tare da mi a hannu ya janyo katin aurin auren SALIMAH wanda suka kai masa ita da EESHART fito da shi ya yi yana are masa kallo musamman wurin sunanta da na angon nata da kuma date aurin auren ma'ana ranar da aka aura. Shiru ya yi yana ta tunanin shikenan SALIMAH ta yi aure ta bar shi ta auri za in ranta mai ku i kamar yadda take da buri shi ta bar shi saboda talauci da halin babu. Motsi ya ji da sauri ya tura katin asan latifarsa ya kwanta lif. Mama da sallama ta shigo akin yana daga kwancen ya amsa mata wuri ta samu ta zauna ta ce "ABBAS" "Na'am Mama" Ya ce yana tashi zaune amma ya kasa ha a ido da ita saboda ba ya so ta gane halin da yake ciki ya san kuwa kallo aya za ta masa ta gane. "Mai yake damunka kwana biyun nan? Kai da ka daina saka kan ka ciki damuwa amma yanzu kake so ka mayar da kan ka ruwa? " Ta jefa masa tambayar tana tsare shi da ido. "Mam... "SALIMAH ce ko?" Ta katse masa hanzarin kiran sunanta da ya fara. Idanunsa ya ago ya sauke a kan fuskarta yana jinjina yadda aka yi ta gane damuwarsa bayan ya san ya sanar da ita cewa shi yanzu ko tuna SALIMAH ba ya yi amma kuma shi kansa bai san ya aka yi daga ranar da ta dam a masa katin aurin auren sai kawai ya ji ya fiya tunaninta tabbas so ba arya bane kuma ba ya fita ya bar zuciya sai dai ya lafa. "Na ce SALIMAH ce ?" Kansa ya sunkuyar don ba zai iya mata arya cewa ba ita ba ce. "To kuwa ka sani haramun kake aikatawa ABBAS tun da yanzu ta zama mallakin wani dole ka yi ya i da zuciyarka na ganin ka auracewa tunaninta " 'Mama ya aka yi kika sani?" "Ai na ga katin aurin auren tun ranar da ka shigo da shi a hannunka na lura kana cikin damuwa shi ne da ka tafi masallaci na bu e na gani, kuma na san babu mai yin wannan anyan aikin sai SALIMAH wato ta akko afa ta kai maka katin ka kar a ka ga yanzu burinta ya cika ta mayar da kai tuwa wato cikin damuwa" agowa ya yi yana kallon Mama a gefe aya yana raya cewa kenan SALIMAH da biyu ta bashi katin aurin aurenta shi duk a tunaninsa don kawai ya gani ne amma in haka ne ba aramar iyayya take masa ba. Hannu ya kai asan katifa ya zaro katin ya yayyaga shi tare da masa gutsin-gutsin. " Da ya fiye maka dai tana can ta bu e babin sabuwar rayuwa ta barka da dakon so ita kuma cikin walwala da jin da i da kuma daula, ya kama ta kaima ka fitar da matar aure ka yi aurenka hakan zai sa damuwar da kake da ita ta ragu ko da ba duka ni na rasa ma ya aka yi ka koma ruwa" Shiru ya yi . "Da kai nake magana fa ABBAS" "Mama ni ina zan samu wata matar aure ni ai na gama aure a duniya!" "Baka isa ba ABBAS" Mama ta yi maganar a zafafe cikin hargowa. Shi kansa sai da ya tsorata da yadda ta masa maganar har ya rasa abin cewa. "Saboda wata wacce bata damu da kai ba babu yadda za a yi ka i yin aure' "To Mama ki yafe mini Allah huci zuciyarki, ni kawai ina ganin na gama so a rayuwata ba zan ara soyayya ba matan ma tsoronsu nake" "Sai ka yi aure ABBAS ai a duniya ba a ta a zama aya kuma duk lalacewar zamani ba a rasa na kirki tuni idan ka saka tunaninta a kwandon shara za ka samu wacce kake so take sonka kai har ma ku zo ku yi rayuwa ka ji tamkar baka ta a sanin wata SALIMAH ba" Jin ta kawai yake amma ya san da wuya kuma zai yi wahala hakan ya kasance. "Tun da kana ganin kai ka gama za in mace a duniya, to ni zan zama maka matar kuma ba zan maka za en tumun dare ba, don aure kam babu fashi sannan ba gudu ba ja da baya!" Tana gama zuwa nan a maganarta ta tashi fuuuu ta bar akin don tana ganin in har bata zage dantse ba to tunani zai yi tafiyar ruwa da hankali da tunanin ABBAS!. "Da kallo ya bi ta tamkar wani sakarai, ji yake gaba aya Mama ta hargitsa masa tunani da lissafi, shi da a son samunsa ne ba zai ara yin aure ba gwara ya ringa azumi saboda ya yi wa mata ku in goro tun daga kan SALIMAH ya san dai an ce zuciyar mace( SADIYA ABDULRAZA ) Tana da tausayi da rauni amma dai ban da ta SALIMAH. Da a ce SALIMAH tana da tausayi da bata guke shi saboda talauci ba amma ya fawwalawa Allah komai kuma ya sa a ransa zai kar i za in mahaifiyarsa da hannu bibiyu wata ila ya dace wata ila ya samu mai share masa hawaye wata ila ba maye gurbi ba har ma sai ta fi SALIMAH matsayi a wajensa sai dai shin wace ce wannan? Wace mai baiwa da sa'ar ce za ta tsinci dami a kale?!. *SALIMAH* Hannunta har rawa yake wajen ri on wayar da ta kara a kunne, zuciyarta tana azalzalarta a kan tambayoyin da suke unshe a birnin zuciyarta wanda take tunanin ta inda za ta fara jero masa su, don ba za ta iya jira har sai ya dawo gida ba ko ma a ina yake dole ta fallasa masa asirin zuciyarta na acin ran da ta unsa kuma ta yi dakonsa tsawon kwanaki uku ragas. A ufule ta yi niyyar zayyano masa laifinsa don ta ji ko zai yi arfin halin kare kansa? Domin ta yi al awarin sai dai a yi duk wacce za a yi amma ba za ta saurara ko ta lallashin zuciyarta ta bi abin a sannu ba. Sai dai me? Kalaman da Alhaji Tahir ya feso mata su ne suka sa ta guntse nata da ta guntso za ta amayar masa. "Ki zo angarena yanzun nan bana son ata lokaci, minti biyar kacal na baki!." Yana gama fa ar hakan it ya kashe wayar ba tare da ya jira cewar ta ba, dama ya yi maganar ne bisa bada umarni ba wai neman shawara ba. Da kallo ta bi wayar bakinta a sake tamkar yawu zai zubo mamaki al'ajabi game da mutuwar zaune su ne suka taru suka saka asusuwan da suke ilahirin jikin SALIMAH yin mutuwar kasko. Zuciyarta tana harzu ata a kan cewa ya raina mata wayo game da rainin hankali gaba aya ma ya raina mata ajawali ita in SALIMAH da maza suke buri da fatan su mallaka don su same ta yake neman bu a mata asa a idanu? Ita SALIMAH da yake kaffa-kaffa da acin ranta yake rawar afafu a neman aurenta ita zai wa haka, ita SALIMAH da take bada umarni a gidan ABBAS kuma ABBAS ya bi ba tare da musu ko gajiyawa ba kuma ko da ita ce ta yi laifi sai dai a bi abin da take so amma yau ita aka yi wa laifi kuma ake bata umarni cikin halin ko in kula wato an dake ta an hanata kuka. Bayan umarnin da aka bata na zuwa angaren wai har da iyakance mata lokaci, a matsayinta na sabuwar amaryar da bata tare da ango ba bare ta yi tunanin har an ci moriyar ganga ne za a yada korenta. Wani unci ne da takaici ya cika mata zuciya wai ita ce ma za ta je part insa tana ganin wannan raini zai ja mata a wajen abokan zamanta wanda tsawon kwanaki ukun nan babu wacce ta yi tozali da ita. "Kawai ki je a yi wacce za a yi tun da dai haka ya za
Chapter 34 · 0% Book details