Sashe 6
Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 4 *ABBAS* Dakatawa Mama ta yi bata hana shi kukan ba, duk da sautin kukan nasa yana ta a mata zuciya, ta san cewa ba karamin abu bane zai sa ABBAS in kuka haka ba kamar wani mace, kasancewarsa mai hakuri da juriya ha e da kawar da kai sai dai ta san kukan nasa ba ya rasa nasaba da SALIMAH domin ta san ita ka ai ce matsalarsa, ita ka ai ce damuwarsa, ya auki son wacce ba ta son shi ya saka a ransa ko ka an SALIMAH ba ta tausayinsa bare ta ji tausayin halin da yake ciki na soyayyarta burinsa kullum ya faranta mata, amma bata gani ta raina duk kokarinsa a kanta shi kuma kullum fa i tashin sa SALIMAH ce duk da Mama ta san yana matukar kokarin ganin ya kyautata wa Mamar matsayinta na mahaifiya a gare shi sai dai ganin irin jarabawar da ya ha u da ita na matar da ya aura sai take yafe wasu abubuwan tun da bata rasa komai ba kanin mahaifin ABBAS in bai rage ta da komai ba tun bayan mutuwar mahaifin ABBAS yake awainiya da su har yau bai daina ba kuma bai gajiya ba. Sai da ta ji kukan nashi ya tsagaita, ta tabbatar ko ma mene ne yanzu zuciyarsa ta yi sanyi, saboda duk idanun da suka zubar da hawaye to mai idanun yana samun salama a zuciyarsa. Jin yana ajiyar zuciyar sai ta saka hannunta wanda tun da ya kifa kansa a cinyarta ta ora hannun a bayansa, fara buga masa bayan ta shiga yi a hankali sai da ta tabbatar ya samu nutsuwa daga imuwar da ta gan shi a ciki sannan ta saka hannun ta duka biyu ta ago shi. Sosai ta ji rauni a zuciyarta ganin yadda idanunsa suka yi wani irin ja hatta fuskarsa da saman hancinsa duk sun yi ja saboda kukan da ya yi, kasancewarsa mai farar fata. Ba ma wannan ne ya aga mata hankali ba sai ganin ya yi wani irin zuru-zuru idanun duk sun fa a, kuma ko jiya ya je gidan nata domin rana bata ta a fitowa ta fa a bai je ya ga Mama ba yana kaunar mahaifiyarsa ita ma tana kaunarsa kasancewar sa aya tilo a wajenta. "ABBAS mene ne?" Ta tambaye shi cikin sanyi da tausasa murya. Idanunsa ya runtse wasu hawayen suka zubo sosai ta ji hakan ya ta a ta, ta rasa SALIMAH wace irin mace ce da bata tausayin mijinta kullum yana cikin damuwa sai dai ta auki hakan a matsayin jarabawar da Allah ya jarabci ABBAS in da ita tana masa fatan Allah ya bashi ikon cin jarabawar. Idanunsa take kallo wanda ya rufe su hawayen suna surnanowa. "Na sha fa a maka kake rike sirrinka, su iyali da kake gani sirri ne, da i ko wuya ba a son a ke jin kansu sai in abin ne ya yi yawa sai a fa a domin sulhu da kawo maslaha" Ta ce cikin murya mai kama tana masa nasiha, duk da ta san ABBAS yana da dauriya da zurfin ciki sai dai wani lokacin kasancewar ta na mahaifiya gare shi ba sai ya furta cewa yana cikin damuwa ba kallo aya take masa ta fahimci halin da yake ciki, duk da cewar halin da gidan ABBAS in yake ciki abu ne bayyananne wanda kowa ma ya sani sai dai wanda bai ta a taka kafarsa a gidan ABBAS in ba. "Ka cigaba da hakuri wata rana sai labari, wata rana masu bada labarin ma babu kowa, shi zaman duniya an hakuri ne duk abin da aka yi hakuri da shi zai wuce wata rana kamar ba a yi ba" "Mama" Ya ce bakinsa yana rawa don har ya fara jin sanyi alamar zazza i zai rufe shi, ga shi yana so ya fa a mata cewa ya saki SALIMAH amma kuma bakin nasa ya masa nauyi. "Na'am ABBAS" "Na, na, na" Ya ce yana ta faman maimaitawa tamkar wani mai in'inna. "Mai ka yi ABBAS? Ni mahaifiyarka ce da baka da kamata a fa in duniya ina so ka sani da a ce SALIMAH ce take maka wannan kaunar da kake mata, ai dai ka san kana matukar kaunarta, kaunar da kai kan ka baka san iyakarta ba to da ita ce take maka kauna ko da ta fi wacce kake mata to ina so ka sani da bata kai ni kaunarka ba" Idanunsa da suke rufe ya bu e har sai da gaban Mama ya fa i ganin irin mugun jan da suka yi. ."Tabbas da bata kai ni kaunarka ba, ai a duniya babu wanda ya kai uwa kaunar anta, na maka misali da kaunar da kake mata ne don ka gane, uwa-uwa ce kaunar uwa da ban take, shi ya sa ma aka ce a yi wa uwa biyayya sai da aka nanata sau uku sannan aka ce a bi uba amma sau aya aka ambaci uba. Saboda kaunar uwa da ban take anta tun yana cikinta bata gan shi ba take kaunarsa, jin sa take har cikin ranta, yadda take shan wahala rainon cikin da haihuwar da kuma shayarwa rainon yaro har ya girma shi ya sa ubangaji ma aukakin sarki ya ambata a littafinsa mai tsarki, cewa wahala ce a kan wahala. Shi ya sa uwa kaunar anta bata ta a gushewa a zuciyarta sai dai ta ki wani hali nasa in yana aikatawa sannan kuma kullum a yaro yake a wurinta bata ganin girmansa" "Haka ne Mama" ABBAS ya ce cikin sanyin murya yana jaddada cewa in har duk wannan kaunar da yake yi wa SALIMAH yana jin zai iya sadaukar da komai ita ta samu zai iya sadaukar da numfashin sa ita ta rayu, amma kuma Mama ta ce ko dai kaunar ta fi haka to kaunar uwa ta wuce nan wannan ya sa ya ji jikinsa ya yi sanyi. ."Fa a mini mene ne ka yi?" "Na saki SALIMAH" Ya ce wani kuka yana taho masa sai da ya dantse bakinsa ne kuka mai sauti bai fito ba sai hawaye kawai. Wani irin bugawa da karfi zuciyar Mama ta yi. Sosai ta ji tashin hankali tun da ta san tabbas zai shiga matukar damuwa da rashin SALIMAH abu ne mawuyaci SALIMAH ta kar i bikonsa ba ta ma jin hakan zai iyu musamman da yake daga mahaifiyar SALIMAH har SALIMAH burinsu bai wuce kar ar takardar sakin ba, dama mahaifinta ne zai iya yin komai to shi kuma mai yanke kauna ta auke shi wato mutuwa. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!!!" Ta shiga maimaitawa har sau uku, shi dai yana ambata mata ya yi sakin sai ya yi saurin maida kansa ya kifa a cinyarta, ita ma ganin zai kifa kan nasa sai ta sake shi daga rikon da ta masa tun lokacin da ta ago shi. Shiru ta yi na an lokaci gaba aya tausayinsa ya mamaye mata zuciya, da a ce tana da ikon cire masa son SALIMAH daga zuciyarsa da tuni ta cire masa ya huta. "ABBAS garin yaya haka ta faru? Baka san cewa saki shi ne halataccen abun da ubangaji ba ya so ba? Baka san cewa a duk lokacin da aka yi saki sai al'arshin ubangiji ya girgiza ba? Mai ya sa ka yi wannan anyan aikin bayan ka san kai ne za ka cutu ba ita ba, ita dama wannan damar take nema kuma ita ce cikar burinsu ita da mahaifiyarta. Sau nawa suna tako gidan nan su mini iban albarka da cin mutunci a kan sai na saka ka sake ta, amma saboda son da na san kana mata nake shanyewa in jure, mai ya sa ka yi haka babu shawarata?" "Mama, ni ma ban san na furta ba zuciya ce ta auke ni da acin rai, haushi da takaici sai da na furta kalmar sakin sannan na gane wautar da na yi" "To ai dama shi shai an har abada burinsa kenan burinsa ya shiga tsakanin ma'aurata burinsa ba ya cika sai ya ga ya raba aure, kai shi fa duk wani abu mai kyau gaba yake da shi" . "Haka Allah, ya kaddara dama can rubutacciyar kaddara ce, a rubuce yake cewa a wannan rana igiyar aurenku za ta datse, a wannan rana zamanta a gidanka zai yanke sai dai wani rabon kuma in akwai shi za ta dawo" Mama ta ce bayan ya gama fa a mata yadda abin ya faru. "Ba za ta ta a dawowa ba Mama ni na sani" Ya ce har lokacin kansa kife a cinyarta. "Ka kwantar da hankalinka ka yi addu'a ni ma in taya ka Allah za a abin da ya fi alkairi" Ta ce tana ago fuskarsa ta share masa hayawayen, tare da masa fa a sosai a kan sanyawa mace hannu sosai ta nuna masa illar yin hakan ta umarce shi da duk runtsi duk wuya kar ya kara dukan mace, sannan ta masa nasiha mai ratsa jiki a kan yadda da kaddara kyakkyawa da kuma mummuna. Har sai da aka kira magriba tana ta masa nasihar sai da ta ga ya samu nutsuwa, ta saka masa albarka da fatan wanyewa lafiya, sannan ta ce ya je ya tafi masallaci ita ma ta yi alwala ta yi tata sallar. Sai da ya yi sallar ishsha'i ya dawo gidan, nan ta zuba masa abinci amma ya ki ci duk da akwai yunwa a tare da shi amma shi ba ya jin yunwar zafin rashin SALIMAH ya danne komai. A tsakiya Mama ta saka abincin ta auka a cokali ta nufi bakinsa tare da ce masa ya yi Bismillah, Bismillar ya yi ta shiga bashi a baki, sai ya samu kansa da kin mata musu haka take bashi abincin a baki ita ma tana ci har suka cinye ta