Sashe 12
Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zan jure komai in har zan rayu da ke a inuwa aya, wallahi, wallahi, wallahi ba zan ta a butulcewa ba, ba zan ta a ha a ki da wata mace ba idan kika dawo gare ni ba zan ta a miki kishiya ba ke ka ai za ki rayu ki yi yadda kike so da ni, ni naki ne zuciyata taki ce SALIMAH" Ya kai karshen maganar rauninsa yana bayyana a cikin nuryarsa. Wani uban tsaki ta doka, wanda ya sa hawayen da suke makale a kwarmin idansa gangarowa, wannan tsakin ya tabbatar da maganganunsa tamar busar sarewa ya yi wato sun shiga ta kunnenta na hagu sun bi ta kunnen dama ko alamar tasiri kalamansa basu yi ba. FAROUQ wani tausayin abokin nasa ya kara kama shi, ko shi da yake namiji maganganun ABBAS sun shige shi amma ita SALIMAH da ake yi wa kalaman sannan ita ce mace kuma an san mata da tausayi kuma zuciyarsu tana da rauni a kalla ko da bata amince za ta koma ba ta masa wata kalma mai taushi. "SALIMAH" Ya furta a daidai lokacin da ya durkusa gwiwoyinsa a kasa yana durkushe a gabanta, bai yi la'akari da farin yadin jikinsa ba shi damuwarsa ma duk so da yake mata bata gaskata shi ba ya ma gabanta kwata-kwata. "Ya kike so a yi, mai kike so in yi ko kina so in ayo miki fatar jikina ki yarda, ko akwai wani angare na jikina ko koda ta kike so zan iya bari a cire guda aya ko da kare kika ce a dasawa zan yarda ko da hakan zai zama siyar mutuwata ai a dalilin so ne son ma naki SALIMAH... "Kai ya isa haka ABBAS mai ya sa kake kalami a inda ba za a tausaya maka ba? Wannan da kake gani ko ranka za ka cira ka bata ba za ta yarda ba kai alamunta sun nuna ko mutuwa za ka yi ba za ta tausaya maka ba, na lura mugun tsanar da ta yi maka ba iya kai take wa ba talaucin da kake ciki ne bata so da a ce kana da imbin dukiya ba sai ka ka roke ta ba, dukiya ce kawai a ranta duniya ce kawai a gabanta ka daina ata gishirinka a dahuwar kaho, ka zo mu tafi ka roki Allah ya cire maka son ta ka samu mai kaunarka ka yi sabuwar rayuwa ka manta da ita... ."Ita nake kauna FAROUQ" . Wani haushin su ne da ya turnuke SALIMAH ya sa ta kasa magana sun mayar da abu tamkar a wasan kwaikwayo ko littafin hausa, sai wani kalaman soyayya yake tamkar wani romeo, ita fa ko kalmar so bata damu sosai a furta mata ba ta fi damuwa ta ji dumus wato masu gidan rana, ku i da ake kira kare kukan ka, ku i aljannar duniya mai ku i ya huta sai yake shagalinsa. . FAROUQ kuwa jin furucin da abokin nasa ya yi sai ya juya musu baya, don ya gaji da ganin abubuwan takaicin da ABBAS yake a kan so ana wulakanta shi. SALIMAH kuwa ganinsa durkushe a gabanta sai wata tsanarsa take tsarga mata zuciya musamman in ta tuno da maganar Umma cewa zuwansa wajenta barazana ne ga zuwan manyan Alhazan zawarawan ta, zuwansa zai zama shamaki ga cikar burinta hakan ya sa ta ji gwara ta masa hukunci. "Dan Allah SALIMAH... Maganar ABBAS ta makale ne a daidai lokacin da SALIMAH ta aga bokitin ruwan tsarin nan ta sheka masa tun daga saman hular kansa, har bayansa jigilif ya jike, FAROUQ da sauri ga juyo jin zubar ruwa sannan jin wurin ya umame da wari, ya san kafin SALIMAH ta fito kamshi wurin yake amma tun da ta zo yake jin wani wari tunaninsa ko kwata ake kwashewa a wani wajen amma yanzu kuma sai ya ji warina dab da su hakan ya sa ya gane cewa ruwan wannan ne dama yake warin wanda ko ka an bai kawo a ransa cewa ruwa ne ma a bokintin hannunta ba. "Wannan ka an kenan daga abubuwan da za ka fuskanta matukar ka ci gaba da zuwa kofar gidanmu, ba za ka hana ni rawar gaban hantsi ba, nan gaba zan iya watsa maka tafashashshan ruwan zafi ka ga idan fatar jikinka ta silsilge ka hakura da zuwa in kuma baka daddara ba akwai wasu abubuwan da na tanadar maka har sai ka janye kafarka ta fukara'u a kofar gidan nan" Lokacin da ta wasa masa ruwan sai ya ji wani sanyi ne da ruwan tamkar ruwan randa ko na firji, ga wani wari da ruwan yake har fuskarsa ruwan ya wanke, jikinsa jigilif babu inda ruwan bai ta a ba a take wani kaikayi ya fara masa sallama a fatarsa. Duk wannan batutuwan da take masa ba ya ma fahimta, tsaye ya mike yana kallon kwayar idanunta bai ga salama ko tausayi ko rangwame daga idanunta ba. La ensa na kasa ya cije da hakoransa an kai ga ar da bakinsa ya kasa furta komai da a ce wani ne ya masa haka ba SALIMAH ba da sai ya gwammace ki a da karatu. "Ke wace irin wawiya ce, mai ya sa kika auki an adam ba a bakin komai ba, kike wulakanta an adam, bayan ubangijinmu ma ya fa a a littafinsa mai tsarki cewa ( Wakakadi karramana bani adama,,, hakika mun karrama an adam)" FAROUQ ya fa a a kufule yana jin tamkar ya hau ta da duka. "Yanzu zan nuna maka wawiya ce ni" Ta ce tana juyawa wajen kwatar gidansu inda aka yi wa makwararan wanke-wanke hanya ruwan yake taruwa a kwatar simintin da aka yi bokitin ta saka ta kwalfo ruwan ta nufo su a wanna lokacin su duka za ta watsawa don shi ma abokin hakan ya zama izna gare shi nan gaba ba zai sake yarda ya rako shi ba. Tana agawa za ta fara shekawa ABBAS FAROUQ ya yi saurin aga hannu zai wanka mata mari, cikin sauri ABBAS ya saka hannu ya rike masa hannun nasa, ba wai don abin da ta yi bata cancanci mari ba sai dai ba ya so a ta a lafiyarta gani yake da a mare ta gwara shi a mare shi zai fi jin saukin abin a ransa. ."Da ka bar shi ya mararwa kansa bala'i wallahi sai na saka an kulleka har igiya ta yi saura, ba kai ka ai abin zai shafa ba har danginka, kuma in kara gani wani ya zo wajen na" Ta ce tana nuna FAROUQ da yatsa tare da shekar da ruwan kwatar a waje ta yi jifa da bokitin ta juya abin ta tana dab da shigewa gidan ABBAS ya ce "SALIMAH" Tsayawa ta yi ba tare da ta juyo ba. "Idan har hakan zai sa ki farinciki na yarda na amince ba zan sake zuwa ba na za i na rayu da kuncin rashinki ke ki yi farin ciki" ."Hahahaha wa ya fa a maka barno gabas take, ai in ka ji mutum yana cewa ba zai iya ba bai kama shi bane ka ji uwar bari" Ta ce a zuciyarta wani da i yana baibayeta ganin ta yi galaba a kansa ashe akwai barazanar da za ta masa ya kyale ta. A fili kuma sai ta ce "Naka ya rage ABBAS za ka iya cigaba da zuwa ni kuma ba zan gaji da maka hukunci ba, kuma gobe za mu zo mu kwashe kayanmu daga wannan gidan kaima ka huta da biyan ku in haya" Tana gama fa a ta juya. "Za ki yi da na sani wata rana, za ki dawo ga ABBAS a lokacin da ya miki nisan da sai dai ki hango keyarsa daga nesa, yadda kika wulakanta shi na tabbatar Allah ba zai barki haka ba, yadda kika raina matsayi da samunsa na tabbatar akwai lokaci yana zuwa ki rubuta ki ajiye za ki ce dama FAROUQ ya fa a mini indai auren mai ku i ne, auren jari, auren da ba don Allah ba ga wurin nan wasu masu ku in suna da kirki da duk kyawawan abubuwa tun da ba duka aka taru aka zama aya ba amma ke saboda abin da kika yi wa ABBAS sai Allah ya jarabce ki! " FAROUQ ya ce cikin aga murya dama da ta juya ba tafiya ta yi ba sai da ta gama ji tsaf. Dogon tsaki ta ja ta ce. ."Bakin ka ya sari kashi, kuma mugun fatanka ya koma maka, babu abin da zan gani, sai dai ya kare a kan ka" Bata jira cewarsu ba ta shige gida. Har ta ace wa ganin ABBAS amma bai auke idanunsa daga wurin ba tamkar dai zai ganta haka ya kurawa wajen ido. A hankali FAROUQ ya yi taku aya biyu ya dafa kafa arsa ya ce ."Abokina" Ya ce cikin tausayawa ABBAS in. Ya san ba laifinsa bane so abu ne da yake cikin zuciya idanu ba ya ganinsa bare hannu ya ta a shi. ABBAS kawai juyowa ya yi ya rungume FAROUQ duk da jikinsa a jike kuma yana warin ruwan tsarin da ta watsa masa amma bai ji tsantsani ba, yana jin irin yadda kirjinsa yake bugu da sauri da sauri. ."Ka yi hakuri ka ji, idan so cuta ne hakuri magani ne" Kai kawai ABBAS ya gya a masa saboda ya ma rasa bakin magana ba ya gane komai kuma ba ya fahimtar komai. Da lallashi FAROUQ ya saka suka hau machine in suka tafi. Da sallama suka shiga gidan Mama inda ta shiga kallon yadda ABBAS in yake a jike. "SALIMAH ce ko?" Mama ta jefa musu tambayar don ta san ita ce ka ai za ta aikata wannan aikin. Shi dai ABBAS bai ce komai ba, FAROUQ ne ya bata amsa amma bai fa a mata yadda suka yi ba ya dai ce mata ta ce ba a ta koma ba gobe za su zo su auki kaya. "Allah kawo su lafiya, ya sa haka ne ya fi alkairi' Mama ta ce tana jin ciwon wulakanta mata a da SALIMAH take. ABBAS akinsa ya shiga ya kwanta rubda ciki, jinsa yake tamkar ba shi da lafiya, ga jikinsa ma ya au zafi