← Book details Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 43

Sashe 13

Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

jin sa yake tamkar a wata duniya ta da ban. "ABBAS baka jin yadda kake warin ruwan nan?" "Ba na jin warin abu aya na sani ina jin kamshi" "Kamshi fa ka ce?" FAROUQ ya tambaya da mamaki. "Ai tun da SALIMAH ce ta watsa mini ba zan ji warinsa ba, kuma zuciyata bata ganin laifinta sannan kuma har abada ba zan daina sonta ba" Ya ce har lokacin yana nan kwance rubda ciki. "To majnun na Laila ai sai ka tashi ka je ka yi wanka ka cire jikakken kayan nan, ni na tafi sai da safe" Bai jira cewarsa ba ya fita daga akin ya wa Mama sallama ya tafi. Mamar ce ta shiga akin take masa nasiha dakyar ta shawo kansa ya yi wankan ga zazza i mai zafi ya rufe shi magani ta bashi ta rufe shi sai numfarfashi yake. Washe gari da yamma Mama tana waje makwarara ta rike ABBAS in da yake ta kelaya amai, da yake da zazza in ya kwana ga ciwon kai mai tsanani hakan ya sa da safe ta kira FAROUQ suka je asibiti magunguna allurori da drip aka rubuto masa, wani abokin su FAROUQ ya kira ya zo gida ya saka masa drip in bayan ya masa allurorin. Bayan an cire ne kuma ya ce zai yi amai Mama ta fito da shi da yake yanzu su ka ai ne a gidan FAROUQ ya tafi. Bayan ya gama aman ne ya zauna a kan wani an dakali da yake tsakar gidan, Mama sai kallonsa take da tausayawa, suna cikin wannan halin ne suka tsinkayi muryar ana sallama. "SALIMAH ce Mama" ABBAS ya ce yana tashi tsaye yana fa a jin muryar SALIMAH tana aya daga cikin masu sallamar duk da bai ganta ba amma ba zai kasa gane muryarta ba amon muryarta yana aya daga cikin sautuka masu muhimmanci a rayuwarsa. Mama hannu ya kai ta rike shi ganin yana karkarwa kuma duk ya ru e ga jikinsa ba karfi, sallamar ta amsa tana jin wani aci a ranta jin ya ce SALIMAH ce. Cikin gidan suka shigo, su biyu ne, ita da wata kawarta ar unguwarsu wacce kusan shekara uku da mutuwar aurenta, ita ma bata yi auren ba har yanzu. Suna wani gani-gani suka shigo gidan su duka suna taunar cingam tana kas-kas cike da rashin kamun kai mayafin nan sakale a kafa unsu ko arzikin yafawa bai samu ba. "Mamar ABBAS ya kike?" SALIMAH ta ce cike da shekiyanci. Shi kuwa garau ya mata da idanu yana kallonta har ba ya son ya kiftawa ya zama tamkar wani zararre, gani yake tamkar yau ne rana ta karshe da zai sake ganinta a rayuwarsa tun da ya yarda ba zai sake zuwa gidansu ba ita kuma ba za ta dawo ba. "Ina lafiya" Mama ta bata amsa cike da gatsali kamar yadda ta yi don Mama ji take ta tsani yarinyar nan yanzu ma bata so ta shigo mata gida ba za ta fama wa ABBAS mikin ciwon sonta da ta tabbatar ko jinyar nan da ya kwanta ita ce sila. "Mukullin akurkin kajin can za a bamu za mu kwashe kayanmu" Kawar tata mai suna RUKY ta fa a tana yi wa Mama kallon up and down. Ko kala Mama bata ce ba ta ja ABBAS yana togewa amma a haka ta nufi akinsa da shi, sai waiwayenta yake, Mama tana zaunar da shi ya yunkura zai tashi wata harara ta zabga masa da ta sa ya koma ya kwanta a katifar dama ba karfin jikinsa yake ji ba. Mukullin ta auka ya fita daga kofar akin ta tsaya ta jefa musu ta koma akin ABBAS yana jin lokacin da suka fice idanunsa a rufe yana jin yadda bugun zuciyarsa yake bugawa sosai. Da motar aukan kaya suka je da maza uku suka kwashe kayan tas don sauran kayan ABBAS ma a nan aka watsar masa su suna bi ta kai suna wucewa, hatta ledar tsakar akin sai da suka na e kayan nasa a dandamalin kasa suka ajiye, da suka gama suka rufe musu gidan. Motar kayan tana biye da napep in da su SALIMAH suke ciki, a kofar gidan Mama suka tsaya, ita da RUKY dai suka shiga da sallama suna wani yatsina. Mama da ta fito daga akin ABBAS jin sallamarsu bayan ta amsa sallamar kafin ta yi magana SALIMAH ta cillo mukullin suka juya suka fice daga gidan. Sosai Mama ta jinjina rashin tarbiya da rashin girmama na gaba tabbas in ba kaddara ba ma babu abin da zai sa ABBAS ya auri SALIMAH don ko hanya basu ha a ba ya bata rata a komai na daga nagartar tarbiya. ABBAS da yake cikin bargon da Mama ta rufe shi yana jin karan dirin tsayuwar motar da shigowar su cikin gidan da kuma fitarsu, sannan ya ji lokacin da motar da napep in suka tashi idanunsa kawai ya runtse yana jin wani zafi a ruhinsa. SALIMAH basu yi masauki ba sai a an kafintoci, in da ABBAS yake aiki saboda rashin mutunci wai a can za ta siyar da kayan haka suka je aka sauke kaya aka yi ciniki aka biya su, gida suka karasa ta sauke tarkace da sauran kayan kicin inta ta sallami masu motar da napep in bayan an shigar mata da kayan gida. Dubu biyar ta ba RUKY a cikin ku in sauran kuma ta ba Umma ta ajiye bayan ta auki dubu ashirin don har kujerun ta siyar. "Yo ajiyar mai za a yi ke da idan kika fara samun ku in sai mun rasa yadda za mu yi da su, ai kawai mu yi cefanen kayan da i mi fara wankin ciki tun yanzu, ki auki wani abun ki yi inkunan kafin na kece raini ya zo wato na zawarawa" Cewar Umma. 09013181851 KU MATSO DOMIN JIN DADDA AN LABARI . ZAN CIKAWA KOWANE MUTUM AYA DUBU GOMA 1OK Shin kin ta a jin labarin 52U? Yadda mutane suke register da cin moriyarsa, da dala 21 ake yi $21 kimanin 35k. Duk wacce za ta yi register a team ina zan cika mata dubu goma 1OK ta kawo 25k sannan duk wata zan ke bata 15k tsawon wata 3 idan acc inta ya cika wata shida zai bu e sai ta cigaba da kwashe ku enta. Mutum 2O nake nema kar ku bari damar nan ta wuce ku ki mini magana a PC 09013181851 [1/5, 8:57 PM] Sadiya Abdulrazak: *RU IYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH *GARGAGA Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 6
Chapter 13 · 0% Book details