← Book details Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 43

Sashe 5

Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nasihu masu bin sassan jiki da shiga zuciya, yana tufka ne mahaifiyarta tana warwara abin da zai fa a mata da ban wanda za ta fa a mata da ban, idan ya biya mata karatun ta nutsu sai mahaifiyarta ta goge hardar. Har ya bar duniya bayan auren da watanni uku a sannan ne ruwa ya karewa an kada domin kuwa sun bi duk hanyar da za su bi wulakanci kala-kala a kan ABBAS ya sake ta amma ya ki yau dai ga shi buri ya cika. Tafiya ta fara yi tana rike niki-niki da jakar kayanta, sai murmushi take, sai sannan kiran kawarta EESHART ya fa o mata da sauri ta kamo sunanta ta danna mata kira ringin aya biyu wayar ta yi ta auka. "Hlo kawata... "Albishirinki ce goro" Ta katse mata maganar tana dariya. "Goro fari tassss" Ta ce cikin zakuwa da son sanin dalilin shigar kawar tata cikin wannan farin ciki, saboda bata yi wani tunanin komai ba. "ABBAS ya ranga a mini saki EESHART yau ya warware wannan doguwar igiyar kaddarar da tsofaffin nan da shedu suka taru suka talaulaye ni da ita" Ta ce hakoranta talatin da biyu a waje. Alhaji ALI da suka shawo kwanar layin yana waya, da ita ya fara tozali ganin dariyarta sai ya saka shi cikin wani yanayi har ya shagala da kallonta har suka zo saitin ta yana kare mata kallo tabbas ya shaidata ita ce dai ta safen nan da ya gani lokacin da suka fita. "Eh, dariya, kyakkyawa" Ya ce a wayar saboda gaba aya ya ma sha'afa da abin da suke magana a kai. Daga aya angaren aka katse shi da mai yake nufi sai sannan ya dawo hayyacinsa don hatta direban sai da ya gane cewa Alhajin ya yi su utar baki, dariya ce ta so kwace masa amma gudun yi laifi sai ya danne, don ya lura da wacce yake kallo yana ganinsa ta madubi. "Ke SALIMAH bana son wasa wallahi ai ko za ki yi wasa da komai ban da wasa da sakin ABBAS don na san wannan an a nace in ba zai sake ki ba" "Wallahi kawata da gaske nake da bakinsa ya furta kin ganni har na ha o kayana na baro masa agwajan gidansa, kin ga shi ma ya huta da da biyan ku in haya" Wani ihu EESHART ta saka don ta rasa ma ina za ta ajiye wanna magana mai da ."Barka kawata na taya ki murna Allah mana tsari da auren masu dattin hula an malam shehu to ina dalilin auren talaka " ."Wallahi kuwa ai yanzu sai na za a na darje" "Hahaha wallahi kuwa kawata kina lokaci" Ta ce tare da a fashewa da dariya. "Bari in na je gida ma yi waya so nake in je in yi wa Umma albishir ita ma ta ani wannan farin ciki" Da to ta amsa mata tana mai kashe wayar sosai take ji da EESHART yadda take kaunarta tana bata shawarwarin yadda za ta ku uta daga auren ABBAS ta yi auren da za ta ji da i ta huta, sai dai bata san cewa ba turba mai kyau ba ce haka ba kuma hanya mai ullewa ba ce illa iyaka RU IYAR IGIYA ce. Alhaji ALI kashe wayar ma ya yi don ba ya so yake kwari i a waya, sai ya ga gwara ya bari idan ya zauna ya nutsu ya yi wayar. Raja'a ya yi da kallon SALIMAH da take waya har aka bu e get in bai sani ba sai da direban ya durfafi cikin gidan sannan ya dawo hayyacinsa. Ganinta yake tamkar ba bahaushiya ba sai ka ce wacce take aya daga cikin ukun nan, larabawa turawa ko indiyawa saboda yanayin farin fatarta kamar ba na africa ba. Napep ta hanga ta aga masa hannu tahowa ya yi sai da ya zo saitin ta ya ja birki. Jakar ta saka a cikin napep in, tana shirin shiga kamar an ce ta ago kanta ai kuwa ta hango ABBAS ya fito daga gidan tamkar zararre kafarsa ko takalmi babu uwa uba fuskarsa da hawaye, da sauri ta yi saurin shigewa napep "Malam ja da sauri mu tafi kar wancan ya karaso na ga ya yi kama da mahaukaci kar ya warce ni ya mini duka" Ta ce tana hango yadda ABBAS in ya rugo da gudu zai zo wajensu ganin da ya yi ta shige. So yake ya zo ya gwada sa'arsa ko za a dace duk da ya san da wuya wai gurguwa da auren nesa. Mai napep kuwa kallon tsoro ya jefi ABBAS in da shi duk da bai masa kama da mahaukaci ba ko ta yanayin shigarsa, sai dai dole ya bi umarninta tun da aikin ku i zai yi. A guje ya fisgi napep in suka tafi. Cak! ABBAS ya tsaya bai san ma ya aga hannaye biyu ya ora a kansa ba tamkar wanda aka yi wa mutuwa. SALIMAH wata ajiyar zuciya ta sauke ganin bai cim musu ba domin ita a halin da ake ciki yanzu ko hanya ba ta son ha awa da ABBAS in don an yi mai gaba aya haihuwa har hanji. A kofar gidansu aka ajiye ta, gidan kasa ne aka shafe shi da jar kasa, cewa ta yi ya jira ta ta auki jakar ta shige cikin gida. Umma da take zaune a kan kujera tana goga anyar ku ewa ganin shigowar SALIMAH da sallama tana rike da jaka riki-riki bata san lokacin da ta cillar da magogin ku ewar ba, tare da ku ewa guda aya da take rike a hannunta tana gogawa tsaye ta mike tana kallon fuskar SALIMAH mai cike da alamar farin ciki hakan ne ma ya sa ko sallama ta kasa amsawa. "Allah ubangiji ya sa ba ya ji bane" Ta fa a tana kallonta don ta tsani yaji ma ta fi son ta ji kalmar saki duk da ta san mawuyaci ne a yi sakin amma dai ganin yanayin SALIMAH ya sa ta ji tana son jin karin bayani. Cilli SALIMAH ta yi da jakar hannunta, ta karasa da gudu ta kankame Umma cike da farin ciki. ."Umma ABBAS ya sake ni" Ta ce tana kara kankame mahaifiyar tata da karfi. "Ke SALIMAH kin san dai bana wasa da ke" Ta ce lokacin da ta ciro SALIMAH daga jikinta tana kallonta ido cikin ido. "Wallahi Umma ya sake ni saki aya" Ta ce tana ta murna da nuna farin ciki.. "Ayyyyyiririr yiriiiiii" Umma ta rike hanci tare da kwarara gu "SALIMAH anya yana cikin hankalinsa kuwa ya sake ki, ko dai wani abu kika bashi ya sha ya bugu kika tambaye shi sakin?" Umma ta ce tana jinjina yadda aka yi hakan ya afku. "Rass yake babu wani buguwa dawowarsa kenan ma daga... ."Assalamu alaikum" Wani yaro ya shigo da sallam. Amsa masa Umma ta yi tana masa kallon rashin sani. "Wai in ji mai adaidaita sahu a bash i ku insa" Ya ce yana ja ya tsaya. "Lah ka ga na manta ma da shi, Umma kawo ari hu u a bashi" Cewar SALIMAH. "To zo ka kar a" Ta ce tana mika masa ya kar a ta fita. "Oh wai ku in adaidaita ma sai kin zo gida baki da ku i, yau dai Allah ya yanke miki wannan wahala, mai za a yi da wahala na san yanzu manyan mutane masu fa a a ji sai kin za a kin darje" Umma ta ce tana dafa kafa ar SALIMAH. "Wallahi kuwa Umma na san layi za suke yi da motoci a kofar gidan nan kowa yana burin ya mallake ni" Ta ce tana rungume Umma tana jin wani da i domin ta rasa gurbin da za ta ajiye farin cikin da take ciki. Saboda har ta fara hango ta a kayataccen gida na alfarma tana cin duniyarta da tsinke. "Ai babu wanda zai yi tozali da wannan kyakkyawar halittar taki, ya yarda ki su uce masa, shi ya sa nake jin takaici da mahaifinki ya aura miki fukara'u bayan na san na haifi babban jari farar mace alkyabbar mata" Umma ta ce, dariya suka saki a tare. *ABBAS* Tamkar mahaukaci sabon kamu haka ya juyo ya dawo gidan, yana shigowa ya ji wani kunci a ransa kamar zararre haka yake jin sa sai ya ji ba zai iya jure zama a cikin gidan ba, ganin SALIMAH bata nan kuma ya san cewa ba wai unguwa ta je ba gidansu ta tafi a matsayin ya sake ta. Bedroom in ya shiga da niyyar ya sauya kayan jikinsa amma da ya shiga sai ma ya rasa mai zai yi a cikin akin, fitowa ya yi ya shiga falon ya akko mukulli ya kama hanyar waje sai a sannan ya tuna babu takalmi a kafarsa, dawowa ya yi ya saka takalman ya fita ya rufe gidan. Tafiya ya fara yi amma sai yake ji tamkar kafafunsa ba za su yi jumurin aukan gangar jikinsa ba, saboda yadda kafafun nasa suka yi sanyi ba ma kafafun ba hatta jikin nasa ma sanyi karai ya yi kawai dai yana saka kafafun ne ba tare da sanin ina ma yake jefa su ba, ga wata juwa da take faman aukansa. Machine ya tsayar ya fa a masa inda zai kai shi a daidai kofar gidan da ya masa nuni ya ajiye shi ya bashi ku insa. Da sallama ya shiga gidan Mama da fitowarta kenan daga ban aki tana rike da buta ta ga ABBAS ya shigo da sallama amsa masa ta cikin sanyin murya, ganinsa ba yadda yake, idanunsa jajur kai gaba aya a matsayinta na uwa mahaifiya a gare shi tana ganinsa ta san yana cikin matukar damuwa tana ganinsa ta san gaba aya ba ya cikin hayyacinsa. Butar hannunta ta ajiye tana nutar falo ya bi bayanta zaunawa ta yi a kujera yana shigowa akin wani kukan ya taho masa irin kukan da mai yinsa yake yi idan ya ga mai rarrashin sa. Da sauri ya karasa gabanta ya durkusa gwiyoyinsa a kasa tare da kifa kansa a kan cinyarta ya fashe da kuka. 09013181851 [1/5, 8:57 PM] Sadiya Abdulrazak: *RU IYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH *GARGAGA Ban yarda kuma ban amince a juya
Chapter 5 · 0% Book details