← Book details Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 43

Sashe 8

Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

umamen tuwo suka ci amma kuma sai ya ki tafiya wajen aikin kafinta ya ce zai an huta zuwa kwana biyu. Ita ma Mama bata takura masa ba saboda ta san saboda damuwar da yake ciki ne kuma dama ciwo an lokaci guda ne sauki sai a hankali, bare kuma cuta ta so. Da yamma ya tafi gidan nasa auko kayan sawa saboda ko da ya yi wanka na jikinsa ya maimaita. Tun da mai machine in ya ajiye ji a kofar gidan sai gabansa yake fa uwa dakyar ya samu karfin gwiwar tunkarar kofar gidan ya bu e yana ta karanto addu'a a ransa domin yana dosar cikin gidan sai ya ji komai ya dawo masa sabo fil. Tamkar ba a ta a halittar SALIMAH ba haka ya ga gidan. Bedroom in ya dosa ya shiga yana ganin kofar dirowar kayanta a bu e ko rufewa bata yi ba jiyan duk ga kayanta nan a ciki saurin auke idanunsa ya yi daga kallon kayan nata, jin wani abu ya tsarga masa a kirjinsa kan mudubin ya kalla ganin kayanta duk suna nan sai ya ji kuka yana son taso masa. Bakin gadon ya karasa ya zauna ya sunkuyar da kansa yana jin yadda sonta yake kona masa zuciya. "Ya Allah kai ne kake jarabtar bayinka a kan komai, kai ka jarabce ni da son wannan baiwa taka wacce ita bata sona ya rabbi don tsarkin mulkinka, domin buwayarka don karfin ikon ka Allah, ka kawo mini mafita ta alkairi ka yaye mini damuwata na san babu abin da ya gagare ka, kai kake iko da kowa kai kake juya lamura ya rabb ka juya al"amurana zuwa abin da ya fi alkairi kar ka barni da son zuciyata ya Allah" Ya ce a zuciyarsa yana jin hawaye suna taruwa sai dai bai bari sun zubo masa ba ya ya ago tare da aga hannuwansa sama ya ce. ."Rabbi inni lima anzalta ilayya min kairin fakir, la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin, subhanallahi wa bi handihi subhanallahil azim, Allah hakika baka mayar da addu'ar bayinka, ko dai ka amsa a lokacin, ko ka sanya addu'ar ta kare musu wata musiba da ta tunkarosu, ko dai ka sauya musu da abin da ya fi wanda suka nema alkairi a gare su ko ka jinkirta musu Allah ka sa jinkirin tawa addu'ar ya zama alkairi, Allah ka kawo mini ranar da zan yi farin ciki sa anin damuwar nan da nake ciki" Ya kai karshen addu'ar bayan ya karanto sunayen Allah 99 ya shafa addu'ar tare da goge idanunsa. Dirowar kayansa ya bu e ya auki kayan ya saka a jaka ya fito daga akin da sauri tamkar wanda aka ce ya yi mantuwa a waje, cikin sauri ya fita daga gidan ya rufe kofar don ba ya so ko ka an wani abu ya tsikari zuciyarsa a cikin gidan game da SALIMAH. Washe gari ABBAS jin ya kasa jure rashin SALIMAH gaba aya ba ya samun ishashshan bacci, ko ka an ba ya cikin walwala ko kafintocin ba ya iya zuwa ji yake gaba aya duniyar ta masa kunci. FAROUQ ya kira a waya yake fa a masa cewa ya saki SALIMAH, maimakon da ya gama fa a masa yadda abubuwan suka wakana sai cewa ya yi. ."Alhamdulillahi, Allah na gode maka" "Haba FAROUQ ya ina fa a maka ina cikin matsala amma sai ka nuna farin ciki kana hamdala". "To ai dole na yi hamdala wannan abin a taya ka murna ne, haba ABBAS mace ka zama tamkar bawanta amma ba ta kaunarka ko ka an ta mayar da kai tamkar baka sam mai kake ba. Ai sakin SALIMAH shi ne kwanciyar hankalinka ka daure kawai don farko ne amma komai zai wuce tamkar ba a yi ba" Ya ce cikin halin ko in kula. ."To wallahi na san zaman da zan yi da kai" "Yo wane zama kuwa za ka yi da ni in ba wanda ya fi na baya tsawo ba" "Wai mai ya sa ka cika aukan abu da wasa, ina fa a maka bani da sukuni ko aiki bana iya zuwa zuciyata bata da nutsuwa ko na kawar da komai a raina sai tunaninta ya hana kwanyata sakat" "Saboda ka sake ta ka daina zuwa wurin neman halalinka? na fa a maka ka jure Allah zai baka wacce ta fi ta wacce za ta kaunace ka tun da ba ita ka ai ce mai kyau ba" "Sanin kan ka ne ba kyan SALIMAH ne ya ru e ni ba kawai kauna ce domin Allah da a ce SALIMAH fuskarta za ta yi dameji ta samu nakasa a jikinta wallahi daidai kwayar zarra son ta ba zai ragu a zuciyata ba". "Wannan abu ne da ka sha biya mini shi da karatu ne ma da tuni na haddace, yanzu mai kake so in maka" "Please FAROUQ ka zo gobe ka rakani bikonta ko Allah zai sa ta tausaya mini ta dawo" Ya ce cikin marairaicewa. amma kai dai ka cika marar zuciya mace ta sa hannu ta mareka har kake marmarin dawowa da ita to ba zan maka baki ba nan gaba za ta iya saka bulala ta zane ka, kuma ina so ka sani SALIMAH ba ta tausayinka kuma ba na jin za ta ta a tausaya maka, yadda ma take burin samun rabuwa da kai ba na jin za ta yarda ta dawo" "Fata na gari lamiri". "Haka ne ka jira ni gobe da bayan isha'i sai mu je ka gwada sa'arka" "Na gode abokina". "Tun yanzu kake gode mini ka bari sai mun dawo da ita" Ya ce cike da shekiyanci yana kyakkyalewa da dariya ya kashe wayar. Shi sosai ya ji da in sakin ko ba komai abokinsa zai samu nutsuwar ruhi in ta fita daga rayuwarsa. ABBAS kuwa wayar da suka yi sai ya ji nauyi ya ragu a zuciyarsa duk da ba shi da tabbacin dawowarta amma ya dace ta bibiyeta ko ba za ta dawo yanzu ba zai tsumayi zuwanta wata rana. Ko da ya fa awa Mama bata yi yinkurin hana shi ba, duk da ta san ba lallai ne ta dawo ba amma sai ta ga ba a kwacewa yaro garma hakan ya sa ta masa fatan nasara. Kwana ya yi yana sallah yana addu'ar Allah ya ora shi a kan SALIMAH da Ummarta. Ko wunin ranar ma bakinsa ba ya rabuwa da ambaton Allah har da sadaka ya yj duk na neman dacewa a wurin bikon. Da la'asar ya yi wanka ya saka wani yadinsa fari wanda yake ga ya fi kowanne sabunta a cikin kayansa, madarar turare ya shafa ya saka hula, sai murmushi yake yana jin da in zai yi kwalli da wacce ya fi kauna. Duk da a gefe aya yana ta jin fargaba tamkar amarya a daren farko. Hula ya saka sosai ya yi kyau kasancewarsa fari dogo mai doguwar fuska wacce ta kawatu da dogon hancinsa da yake har wajen baki, karamin pink in bakinsa wanda yake tamkar ya saka jambaki, hakoransa da suke a jere reras tamkar masara gashin kansa wanda yake baki wulik a kwance tamkar na larabawa, kwancaccan gashin girarsa da zara-zaran gashin idanu, idanunsa da suke farare tas kamar madara ha e da bakar kwayar idanun da ko kallonka yake sai ka ga tamkar kallon love yake maka,kakkarfa ne kuma fafffa a, ba shi da makusa ko ta ina a tare da shi ga uwa uba mahaddacin qur'ani za a iya kiransa da ya ha a komai kuma bai rasa ba komai. Tun da ya durkusa raka'ar karshe ta nafilar da ya yi bayan an idar da sallar ishsha'i addu'ar neman dacewa ya yi ta yi bayan kafin ya fito ya sanar da Mama a kan ta masa addu'a SALIMAH ta amince ta dawo da to ta amsa masa. Ko da ya fito daga masallacin a kofar gidan Mama ya samu machine in FAROUQ roba-roba tun da dama ya fa a masa ya kauro gidan Mama a can zai same shi. A kofar gidan suka ci karo da FAROUQ da ya fito bayan ya gaishe da Mama ta ce ya duba ABBAS in a waje bai dawo daga masallaci ba. "Kai mutumina irin wannan kyau haka kamar dai angon da zai je aurin aurensa" FAROUQ ya ce cike da tsokana. "Yo mene ne bambanci ni duba mini ma na yi kyau ko in koma in sauya kaya?". "Eh koma ka sake har fatarka ma sai ka sake , tun da wacce za mu je wajen nata ai za ta yaba ko" FAROUQ ya ce cike da gatse. ."Ka ji ka da wani abu za ta yaba mana". "Allah sa" Daga haka suka hau machine in suka kama hanyar gidan su SALIMAH da yake unguwar badarawa. A kofar gidan suka faka machine in nasu suka samu yaro domin ya kira musu ita, ABBAS ko magana ya daina sai sunayen Allah kawai yake jerowa gabansa yana fa uwa. "Assalamu alaikum, wai ana magana da SALIMAH" Cewar yaron da ya shigo. Maimakon Umma ta amsa masa, sai ta carara gu a. SALIMAH da take akin jin Umma tana guda sai ta bazamo da gundunta domin ta san ruwa ba ya tsami banza ma'ana Umma ba za ta yi gu a ba sai da dalili mai karfi. "Mene ne Umma?" "Sai ni uwar kyakkyawa shi ya sa aka ce a mace kyakkyawa jari ce, musamman kyakkyawa idan ana neman aurenta ka wanki gara idan ta yi aure ma kai ka kasa kayanka ka siyar" Umma ta ce tana darawa. "Wallahi Umma kin kara saka ni a duhu" "Ke goshi kika yi ar nan, tun baki yi idda ba har an fara zuwa zawarci kai na san dai bana kakarmu ta yanke saka" "Wayyo da i Umma na kusa fara kashe kala" "Ai kaloli ma za ki kashe iyar nan Allah ya mini gya ar dogo na kusa daina zaman gaban murhu ina toya kosai da koko" Ta ce tana mikawa SALIMAH hannu suka tafa kamar wasu kawaye. "Kula ki leka sai ki musu bayanin cewa su jira ka an kwanakin iddarki su cika, su zo su hau layi, don wallahi wannan karon sai kin za a kin darje Allah jikan Malam
Chapter 8 · 0% Book details