Sashe 15
Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zan yi" Ya fa a yana kallon Hawwa da take zuzzuba musu abincin tana ajiyewa kowa a gabansa. "Ai kai ne da jarabar naci ni ban ga abin so a wannan figaggiyar yarinyar ba ka nemi wayyayyi wacce take da cikakken gata amma sai ka kare a mai karatu iya sakandire marainiya da bata da wani gata" Hajiya ta ce tana ta e baki. "Ai na fa a masa ya ki ji ga an abokaina nan, amma ya ce sai ita tun da ita ya ce zai aura zan aura masa don in nuna masa indai ina raye ba zai ta a rasa abu ba, in ya so idan ya samu mata sai ya aura ko uku ne ya rufe kofa" Baba ya fa "Kai ma Yaya da wani abu wallahi ni fa yadda na tsani Hawwa bana jin akwai wani abu da zai ha a ni da ita sai dai in aiki za ta mini, yarinyar nan ta fini kyau ta fini ilimi ga kokari kamar masifa ko lokacin muna makaranta ita take aukan first position a class in ni in yi na karshe wannan mataccen uban nasu ya ringa mini fa an wai in dage in ke kokari yanyanyanyan ya ringa wata nasihar sa da ba shigata take ba illa mugun haushin sa da nake ji ita ma uwar tasu Ummie take ko Ummita bata da abu misali sai mu yi koyi da Hawwa... "Ya isa Lawisa! Wasa ya yi wasa ban da tsikarin uwar miji, duk abin da za ki fa a ji fa a iya kaina sa SABEER bana so ki ta o mini iyayena da suke kwance a cikin kasa" Hawwa ta ce cikin acin rai idanunta suna ciko da kwalla. "To mene ne saura idan an yi zancen matacce? Ai arahar kunu ta banza ce idan babu gaya a ciki, yanzu baku da gata da galihu don haka abin da kuka yi a gidan nan mai kyau shi zai sa ku samu abinci saboda abubuwan da iyayanku suka yi na kyautatawa ya wuce babu shi mun akko ku ne gidan nan ku yi mana hidima ku samu abinci, in kun yi da kyau za ku ga da kyau! Kuma ko Umar da yake cewa zai aure ki ba wai anci za ki samu ba illa iyaka bauta ce da musgunawa ki zama baiwarsa. Kanta ta sunkuyar ta ci gaba da zuba musu abincin hawaye suna sintiri a kumatun ta, a duniya ta tsani ta ji ana fa awa iyayanta maganganu, sannan ta ki jinin ta ji ana cewa za a aura mata Yaya Umar mutumin da bai san komai ba sai shaye-shaye kullum ya zo gida idanunsa jawur in ya dawo da dare a buge amma saboda ita ba su suka haife ta ba sai a aura mata shi, ita yanzu aure ma ba ya gabanta karatu take so amma tun da ta kammala karatun ga takardun sakandiren nan amma kuma an ki a sama mata adimishan ta cigaba da karatu in ta yi magana a ce wai ta gama karatu iya sakandiren ma ya isa saboda ba sa kaunar ta yi zurfi a karatu har ta zo ta samu aiki ta zama wani abu shi ya sa don su dakusar da rayuwarta za su aura mata Yaya Umar wanda shi ko secondryn bai gama ba ya watsar da karatun wai dama ana karatu ne don a samu aiki ana yin aiki ne don a samu ku i to su kuma dukiya gata nan har sun ci sun tada kai. Sallah wannan bai damu ya yi ba shin ta aure shi ta ce ta auri wa?" Fitowa ta yi bayan ta gama ha a musu ta nufi wajen Baba Sadiya ta kar o abincin SABEER wanda koko ne da kosai. "SABEER ba ya son kokon nan ya fi son shayi kullum in na masa dole ya sha sai ya yi amansa" Hawwa ta ce cikin sanyin murya. "Ki yi hakuri Hauwa'u da a ce da yadda za a yi in ke zuba masa shayin da ko na iya lipton ne da na zuba masa, to bani da wannan damar, da ina da ita hatta dankalin turawan nan da wainar kwai sai na zuba masa Hauwa'u to kin san dai tsari da dokar gidan nan matsawar aka yi hakan ko a oye ne sai ka fuskanci hukunci ko ka rasa aikin ma baki aya' "Na sani Baba Sadiya abubuwan ne suke damuna, ni na san babu na san hakuri amma SABEER yaro ne kullum sai ya yi mitar abinci sai ya yi mitar makaranta da zuwa makaranta a kafa sai ya yi mitar kwanciya a kasa a akin wancan kuma in dai zai yi sai ya sako maganar su Ummie a ciki sai ya tuno cewa da a gidanmu ne da an yi kaza da kaza ya kasa mantawa ni kuma hakan yana tada mini mikin damuwar da muke ciki yana tada mini rashin da muka yi wanda ba za mu mayar da gurbin ba har abada!" "Ita dama rayuwa tana canjawa mutum a lokacin da bai yi zato ba, to ya za a yi da lamarin ubangiji haka Allah ya tsara, wata rana sai labari duk abin da mutum ya yi hakuri wata ran zai zama tarihi" "Haka ne" Hawwa ta fa a tana danne kukanta. "Ki yi hakuri ke ma girma ne ya same ki wanda baki yi zato ba, haka za ji bi komai a sannu su kuma Allah ganar da su". "Amin Baba na gode da kulawarki gare mu".. "Babu komai Hauwa'u karamcin mahaifiyarki gare ni ba zan ta a mantawa ba mace mai kirki da girmama an adam kowa nata ne abin hannunta bai rufe mata ido ba, imbin dukiyar da suke da shi bai saka nata girman kai ko kyamatar talaka ba, ki je ki bashi abincin ku tafi ungo wannan ari biyun ko hau adaidaita sahu, idan kin kai shi sai ki dawo a kafa, wannan kuma man shafawar ne na lakuta muku kuke shafawa in aka biya mu ku in aiki zan saya muku naku tun da nakun ya kare" Hannu biyu ta saka ta kar a tana godiya yanzu duk duniya Baba Sadiya ce ka ai mai kaunarsu mai taimaka musu duk da taimakon ma a oye ake yi saboda kar masu gidan su ankara wani abu ya biyo baya. Dakyar ta samu ya kukkur i kokon jin ya ce zai yi amai ta kyale shi kosan ya ci ka an yana ta cewa da a gidansu ne da an yi kaza da Ummie ta ha a masa kaza ita dai tana ta cewa sun kusa dawowa. "Aunty Hawwa kullum fa sai Hajiya ta ce sun tafi kenan" "Wasa take yi" Ta ce tana jin zafin furucin da Hajiyar take musu tun da ga shi ya shiga kwakwalwar yaron ya zauna daram. Hannunsa ta kamo suka fito suna zuwa get in ga motoci nan guda shida a ajiye ga direbobi nan zaune suna jiran umarni. "Aunty Hawwa ki ce direba ya kai mu mun makarafa" "SABEER, SABEER, SABEER sau nawa na kira ka?" "Uku to ka daina cewa mu hau motacin nan daga su Ummie sun dawo za mu koma gidanmu sai mun za i wacce za mu hau" Ta ce tana sakar masa murmushi tare da lakato hancinsa dariya ya kyalkyale yana kankame ta suka cigaba da da hira suna darawa su ka ai ne farin cikin junansu. Har suka samu napep an arziki a ari da hamsin ya kai su sai ta siya masa biskit na hamsin in yana ta murna. A da SABEER bai damu da biskit ba saboda gasu nan kala-kala- da wafera da cakulet lemuka iri -iri a store in aka saka masa cikin lunch box insa wata rana ma haka zai dawo bai ci ba, amma rayuwa kenan yanzu sai ya yi wata ma bai ci ba. Tana dawowa Hajiya ta tisa ta da masifa wai ta je ta da e ko yawon banza take tafiya, haka ta yi ta gasa mata maganganu ta shiga aiyukan gidan duk da akwai isassun masu aiki amma don a musguna mata ita ake sakawa rabi da kwatar aikin gidan. "Ki je ki gyara akin Umar saboda raini kullum sai ki gyara ko ina ban da akinsa ki gyarawa kowa nasa akin amma ban da shi" Hajiya da take zaune a kan kujera ta ora kafa aya kan aya ta ce tana aika mata harara. Da to ta amsa tana daukan kayan gyaran ta nufi akin nasa ta tsani zuwa akin Yaya Umar kasancewar shi namiji kuma mashayi. Tana tura kofar wari ya mata sallama wannan warin da take ji gwara warin kashi a kansa. Kolon amai ne ya sa ta fitowa daga akin tana danne bakinta da tafin hannunta Hajiya da take zaune ganin wulgawarta da ta fito daga part in Umar sai kuwa ta taso cike da masifa son a zaton ta gyaran ne ta yi ha,inci bai gyaru ba ta fito. Duk kiran da take mata bata amsa ba kasancewar aman ya taho can ciki ta wuce angarensu na ma'aikata ta je makwarara ta ringa kela amai cikinta yana kullewa kasancewar babu wani abinci a cikin sai da gama ta wanke fuskarta ta gyara wajen ta dawo nan ta samu Hajiya ko ta bakinta ba ta saurara ba illa iyaka ta ce ta raina mata wayo tana ji tana kiranta ta kyale ta sai yanzu ta zo a shelake. Hakuri ta shiga bata duk da bata san takamaiman laifinta ba amma haka ta kama kunnenta ta mur e sai da ta kusa sakin fitsari sannan ta kyale ta ganin ta jigata. Umarni ta mata a kan ta koma ta kara gyara akin Umar in ira Hawwa bata samu damar cewa komai ba tun da ba saurarenta za a yi ba. ankwalinta ta since ta aure hancinta ta shiga akin duk kayansa a kasa haka ta tattare ta kintsa su a waje guda hango wasu kwalabe reras a kasan gadon karambani ya sa ta yin kallon kwakwaf ai kuwa ta yi tozali da kwalaben giya. Sosai jikinta ya shiga karkarwa tana mamakin shi dai Yaya Umar duk wani abu na sa o yana yi bayan shan kwaya, yana shan giya ga neman