← Book details Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 43

Sashe 2

Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

NA MAMAN AFRAH *First Class Writers Asso* Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGA Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 1 Zaune take a matsakaicin falonta kan kujera mai zaman mutum aya, inda take tsefe gashin kanta wanda ya rage saura guda aya rak ta gama tsifar. Sai da ta karasa, ta taje sannan ta fito daga falon ta nufi bedroom inta wanda yake jere da falon da yake irin akunan nan ne da ake yi wa lakabi da mu koma aji. Tsaye ta yi gaban mudubi tana karewa kanta kallo, fara ce tas sai dai tana da matsakaicin tsawo doguwar fuskarta mai yalwataccen gashin gira manyan idanunta da suke auke da zara-zaran gashin ido, hancin ta irin wanda ake yi wa lakabi da tamkar biro, gashin kanta baki wuluk wanda ya zuba har bayan kafa arta. Cikakkiyar halittar da take da ita daga sama har kasa wacce kowace mace za ta so a ce ta mallaki hakan, wannan kyawun halitta da Allah ya mata shi ya sa kawayenta suke mata kirari da MATAR MANYA amma sai dai kash! An samu akasin lissafi domin kuwa buri da mafarkinta bai cika ba a nata ganin kenan da kuma ganin wasu daga cikin kawayenta. Kasancewar ta auri mutumin da take ganin ba shi da sunan da ya dace a kira shi illa mai na sama ya ci bare ya ba na kasa ba. "Wannan ita ce kaddarata, sai dai na tabbata ba zan dawwama a hakan ba, dole na samarwa kaina mafita ko ba jima ko ba da e sai mafarkina na MATAR MANYA, ya cika domin ba zan lamunci zama da kaddararran auren kafinta ba" Ta furta a fili tana kara karewa cikakkiyar halittar da take da ita kallo wacce tana ganin har yanzu dai ruwa bai karewa an kada ba akwai sauran rina a kaba. Wani uban tsaki ta ja lokacin da ta hango hoton ABBAS ta cikin mudubin wanda yake jingine a gefen gado, tana jin wani haushi da takaici tabbas ba shi ne mafarki da burinta ba, shi in da mai gadin gidanta ya dace sai ga shi kaddara ta ha a aure a tsakaninsu, hakorinta ta saka ta dantse le anta na sama tana mai kankance idanu janyo ribon inta da yake kan madubin ta yi ta ha a gashin wuri aya ta yi parking insa, dakyar ta samu ta ha a wuri guda saboda tsawo da kuma cikarsa. Fitowa tsakar gidan ta yi ta rasa ma mai yake mata da i saboda kugin yunwar da cikinta yake, kicin ta karasa ta bu e ragowar sauran tuwon jiya wanda kasancewar ba shi da yawa ABBAS ya hakura ya ce ita ta umama ta ci gawayi ta kunna ta saka tuwon cikin miya ta ora. Karan wayarta da take ta ruri a falo ya sa ta taho kafin ta zo kiran ya katse har ta juya saboda idan ta auko wayar ma hakan ba shi da amfani saboda bata da kati bare ta bi kiran, shigowar wani kiran ne ya dakatar da ita ta koma ta auki wayar EESHART shi ne sunan da yake yawo a kan wayar. "Wai ina kika shiga ne kawata na miki sako saman whatsapp na ga bakya online yanzu ina kiranki ma shiru" "Data ce ta kare mini" Ta ce tamkar ta saki kuka. "Kai innalillahi gaskiya SALIMAH kin saka kan ki cikin wani hali ke yanzu data ma sai take gagararki, kamar dai ke kika rako mata duniya to shi kuma kiran da kika ki auka fa?". "Ina kicin ina umama tuwo... "Tuwo!?" Ta ce tamkar ta fa i wani mugun abu. Shiru ta yi saboda takaici ya gama cika mata zuciya. "Dama abubuwan da ar aiki ta dafa mini wanda nake son na ci, na auka a hoto na turo miki, yam balls, chicken pepper, wainar kwai sai shayin da na saka aka juye madarar gwangwani ta ruwa uku don ruwa ma ka an aka zuba" Ta ce jin ta yi shiru SALIMAH a take yawunta ya tsinke ta ji dama ita ce a cikin daular da kawar tata take. "Ai tun da kika za i zama cikin talauci kin dinga ganin takaici kenan, ni fa sai a wajenki ne nake jin sunan tuwo, don rabona da na saka shi a bakina tun ina gidanmu shi ma kin sanni sai na ga dama nake ci" ."To wai ya zan yi ne EESHART kin san dai bani da ikon sakin kaina shi kuma ABBAS yadda kika san da igiyar aurena aka halicce shi ya ce muddin yana numfashi ba zai ta a sakina ba kin san irin mutuwar da ya yi a kan sona... "Yo dama ya za a yi ya yarda ya saki mace kamarki, bayan ya samu tsuntsu daga sama gasasshe ai ya sani idan ya rabu da ke ba zai samu kamar ke ta aure shi ba, bayan ya san sa'a ya taka amma ki cigaba da gwadawa shi aure ai rai ne da shi daga wa'adinsa ya cika dole a rabu ko ba a so" "Haba EESHART kina ganin shekara biyar kenan ina fama amma bai sake ni ba". "Ki dai cigaba da gwadawa domin da gwado jirgin sama ya tashi" Da to ta amsa mata suka yi sallama bayan ta ce za ta saka mata datar da kati. Da tunanin mafita ta ajiye wayar tana jinjina ranar da za ta dace ABBAS ya furta mata kalmar saki ko da a cikin baccinsa ne ko da su utar baki ne don ta fita ta auri miji na kece raini ta rayu a gidan hutu wannan shi ne mafarkinta wanda marigayin Babanta ya yi fatali da shi a cewarsa ABBAS ne da ya dace da ita shi ne mai kaunarta da gaskiya duk runtsi duk wuya sai ga shi bayan auren Baban ya mutu kuma ABBAS ya ki sakinta har yau. Kicin ta koma tsabar tuno abin da kawarta za ta ci da kafa ta yi ball da karamar tukunyar tuwon da ta ora ya kuwa kife a kasa ta juya falon ta dawo ku in da ABBAS ya bata ta ba almajirinta ya auno shinkafa da kayan miya a yi abincin rana shi ta zari dubu aya ta fita ta bu e kofar gidan nasu wanda yake gidan haya ba mallakin ABBAS in bane. Tana bu e kofar idanunta ya sauka a kan gidan makocinsu Alhaji ALI wanda gidan yana kallon gidan nata, iya ganinka gida ne da aka kashewa dukiya don kuwa gida ne aljannar duniya gida ne da take mafarkin samu irin gidan nan ko da mutum bai rayu a ciki ba in har yana sa hangen na sama da shi tare da raina matsayin da Allah ya ajiye shi to kuwa zai so ko sau aya ne tak ya shiga gidan ya kashe kwarkwatar idanunsa. Ta yi nisa a zancen zuci ta shagala da kallon gidan bata ankara ba sai gani ta yi an wangale get in gidan motar da aka bu e get in don ita ce ta fito kallon yadda motar ta ha u tare da yin shekin sabunta ne ya auki hankalinta bayan sauran da take hangowa daga cikin get in wanda suke fake wasu a lullu e wasu a bu Alhaji ALI da yake bayan motar direbansa yana jansa ne ya yi gam da katar da ganin SALIMAH cike da mamaki yake ganin kyawunta da kuma kira da Allah ya mata kyakkyawa ce ajin karshe, tsantsar mamaki ne ya kama shi ganin cewar mace kamar wannan tana rayuwa a kaskantaccen gida kamar wannan domin yanayin shigarta ko ankwali babu ga rigar jikinta da ta kama ilahirin jikin nata hakan ya nuna matar gidan ce ba wai zuwa ta yi ba. Tsabar kallonta da yake har sai da ya sauke glass in motar, ido hu u SALIMAH ta yi da shi da yake bakin glass ne baka ganin na ciki amma na ciki yana ganinka ita kuma kyan motar take karewa kallo tana kiyasta ranar da za ta shiga mota kamar wannan. Ganin sun ha a ido sai kawai ta diririce ta shiga agawa almajirin da ta gani yana bara a wani gidan da yake gefen gidanta hannu alamar ya zo, hakan ya yi daidai da saita hancin motar da direban ya yi a inda suka saka gaba. Har waiwayenta Alhaji ALI yake har sai da suka ace daga layin sannan ya daina waiwaye. Karan rufe get in ne ya saka ta sauke ajiyar zuciya tare da maida hankalinta kan almajirin ta ce. "Je ka wurin mai biredin wancan ka siyo mini bidredi na ari uku kwai guda biyu madarar sachet guda aya" Robarsa ya bata ya tafi ta dawo ta ajiye robar jim ka an ya shigo da sallama. "Kwan ari biyu da hamsin-hamsin madara kuma ari da saba'in" Ya ce yana mika mata ledar da canjin naira talatin "Rike canjin" ,Kawai ta ce ta juya ya ce Allah kar a ya auki robar tasa ya juya ya fita, ko amsa masa bata yi ba ta wuce kicin in saboda yunwar da take kwakular an hanjinta ta dafa ruwan zafi ta soya kwan ta dawo ta ha a shayi ta zauna ta ci ta koshi. Sai lokacin ta ji dama-dama a kan kwa ayin da EESHART ta tada mata. Tana nan tana danne danne a waya ta shiga nan group in a whatsapp ta fita saboda datar da EESHART ta turo mata, wani group na bussines ta shiga inda admin in ta turo hotunan lesuna da dogayen rigunan abaya, wata mata da user name inta aka rubuta matar mai kumbar susa ita ce ta za i lesuna guda uku dogayen riguna guda biyu ta ce a mata total a tura mata acc no ta private ko ragi bata nema ba kusan dubu ari uku. i sun yi a
Chapter 2 · 0% Book details