← Book details Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 43

Sashe 37

Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sa take ganin in ta shiga gidansa matansa ba za su zame mata kishiyoyi ba sai dai su zama tamkar bayi a wajen sarauniyai!!!. Niyyarta ta gallaza musu ta ci karenta babu babbaka a arshe duk wacce ta gaji da gashin umar cikin gidan ta cikawa bujenta iska. Sai dai kash! Yau ta gane akwai bambanci tsakanin aya da tsakuwa ashe dai kallon haddirin nesa ne ya sa ta yi wanka da kashi, tabbas kallon kitse take wa rogo. A yau aya ta gane karin maganar da bahaushe yake cewa gaba da gabanta aljani ya taka wuta. Bata ta a zaton duk kyan da take ta ama da shi ba za ta samu wacce ta fi ta ari bisa ari a cikin gidan Alhaji Tahir ba, kyan da shi ne makamin da ya sa ta kashe aurenta don tana ganin kyan nata zai sa ta samu mai ku i inda za ta yi amfani da zallar son ta ci duniyarta da tsinken tsire. Sai ga shi matarsa da ta fara shigowa ta kere ta a komai ko ayar ma ta fi ta komai haske kawai za SALIMAR za ta fa a mata, domin irin matan nan ne da ake wa la abi da black beauty. Idanunta tamkar za su fa o take kallonsa wanda shi in ma ita yake kallo da mamakin ganin ru ewarta a anuwar maganar da ya yi, wacce bata fi kalmomi alilan ba, taku aya biyu ta yi za ta arasa gabansa saboda yadda take jin zuciyarta tana azalzalarta dole ta tauna tsakuwa ko aya ta ji tsoro dole ta ankarar da shi mummunan kuskure zai yi don idanunta a rufe suke basa tsoron ta mutu ko ta yi rai. "Alhaji Tahir! Haka muka yi da kai? Ni SALIMAH za ka ci wa mutunci ka wula anta a idanun duniya sa... "Da na miki me?" Ya tari numfashin ta har yana ance ido aya saboda shayar da shi giyar mamakin kalamanta. "Tambaya kake ko neman sani? Idan ka manta in tuna maka yau kwanana uku kacal a cikin gidanka ko wulginka ban gani ba, a matsayina na amaryar da ka yi wa furucin kalmar so da auna ba wacce aka la aba maka auren dole da ita ba, amma kake ikirarin gobe za a aura maka wani auren? Ni kuma a wane matsayi ka ajiye kenan? To bari ka ji ni SALIMAH ba zan lamunci raini ba kuma ina so ka sani shi rashin mutunci biki ne idan ka mini ramawa zan yi don wallahi! Wallahi!! Ba zan aga maka afa ba" A fusace ya mi e tsaye cikin zafin nama yana nuna ta yatsa ya ce "SALIMAH ki sani nan ba wajen warginki bane, idan kin saba duk wani abu da kike ta ama da yinsa to ki sani shi fa bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane idan kina cin asa ki kiyayi ta shuri!. Da kike ikirarin duk abin da kike fa a yanzu shin sakin ki na yi? To ko sakin ki na yi baki da hurumin tuhumata tun da ni nake aurenki ba ke kike aurena ba. Aure kuma babu fashi ki kalle su mai suka rasa? Kyau ko diri? Duk wani abu da a mace za ta yi ta ama da shi kowaccensu tana da shi amma na auro ki" Ya ce yana nuna mata matansa da suke zaune, samun kanta ta yi da waiwayawa ta kalle su kamar mai son tabbatarwa da maganar tasa. Farar ganin SALIMAH ta juyo har da gyara kafa ar rigarta irin ta kalle ta da kyau, ba ar kuma sai ta gyara aurin ankwalinta wanda ya kasance ture ka ga tsiya ya sake iyowa gaban goshinta, wani mugun haushin matan nasa da tsanarsu ne suka dirar mata a zuciya. "Ka san suna da komai amma ka auro ni" "In kin manta in tuna miki ko lokacin da kika yi kuri da kyau wata rana da muna magana, in za ki lura ai ban yi magana ba kawai dariya na yi saboda na san mai na ajiye a cikin gidan" "Ba wannan ba Alhaji dole ka fasa maganar aurenka, tun da su wannan na san da zaman su da wacce kake arin ba ofar shigowa nake, idan ma har ya zama dole za ka yi sai dai idan na gama cin amarcina!" "Baki isa ba SALIMAH ni bai mace bata juyani, kuma ina so ki sani a gobe idan an aura aure a goben amarya za ta tare, sannan bakin kwananta ne don naki ya wuce a a'ida ita dama bazawara kwanaki uku ne nata kacal!!!. Kuma kin cinye naki domin kuwa sun wuce gobe kwanankin amarya ne in suka are sai na uwar gida, sannan na mai akin tsakiya daga ita kuma a sannan ne aka zagayo kan ki ina fatan kin fahimta!" Ya fa a babu ko alamar wasa don yadda ma yake magana ko walwala babu a fuskarsa yana yi ne cikin hargowa tamkar zai kai mata duka. if ta yi tamkar ruwa ya ci ta, ashe wula aci ba shi da da i? Ashe akwai damuwa a nuna maka baka isa ba a inda kake ganin ka isa har ka yi yawa? Ashe abu ne mai cin rai a nuna maka kai ba kowa bane a inda kake ganin ka isa, yau ita SALIMAH za a yi wa tonon silili ina dirin jikinta da yake aukan hankalin maza? Ko shi Alhaji Tahir makaho ne? Amma in makaho ne ya aka yi ya ga diri da kyan nata har suka ru e shi ya aure ta, yanzu duk kyan da ya zame mata jari take ganin za ta juya namiji kamar sitiyarin mota amma wai ake nuna mata kwananta ya wuce, wai ake tabbatar mata kwananta uku ne na bazawara bayan shi da kanshi ya sanar da ita ta fiye masa budurwa, kuma kwana ukun ma ba a mata shi ba, tunaninta sai sun kwashe wata uku currr suna cin amarci ba tare da ya waiwayi kwanan sauran matan nasa ba sai ga shi ko saninta bai yi ba a matsayin mace yana ambaton kwanakin sun wuce sai kuma sun zagayo, wannan shi ne alubale babba a wajen a mace mijinta ya nuna mata raya sunnar aure da ita ba bakin komai bane don hakan ya nuna Alhaji Tahir ba ya mararin sanin wace ce ita a cikin mata shu ya sa ya ce kwananta ya wuce. "Ka ha'ince ni wallahi" Ta ce wani kuka yana neman wace mata. "Na ha'ince ki ko kika ha'inci kan ki? Auren nera kika yi kuma ga ki ga nairar, ki kalli Khadija da kyau " Ya fa a yana nuna ba ar matarsa. "Ita ce uwar gidana, kuma mahaifinta mai ku in gaske ne, haka ma Aina'u" Ya ce yana nuna farar da yatsa. "Ita ma mahaifinta mai mugun ku i ne, zan iya cewa babu wacce ta aure ni saboda dukiyata, kuma a ranar da Khadija ta tare washe gari aka aura aurena da Aina'u kuma a ranar aka kawo ta babu wacce ta yi musu da magana ta kuma har yau tsawon shekara goma da auren mu babu wacce ta etara umarni na sai ke? Ke da ba ar kowan kowa ba ke da na auro a duhun talauci na fito da ke hasken arzi i bari ki ji daga bakin abokanan zamanki ku fa a mata doka ta" Ya ce yana kallonsu. "Ba a musayar zance da kai" Khadija uwar gida ta fa "Ba sa a magana ko karya dokar ka" Aina'u mai akin tsakiya ta ce. "To dawo nutsuwarki idan za ki ci arzi i ki ci ki idan kuma za ki koma angin talauci to dama daga shi kika zo, sai dai ki sani fita daga gidan nan akwai ha ari, ha arin da ba za ki so jin wane iri bane" Hawaye ne suka fara sintiri a kumatun ta jin ya mata gorin arzi i wai har yana cewa ta zo daga angin talauci, wato su sauran matansa an masu da shi, ita kuma talaka, idanunta ta aga ta sauke a kan fuskarsa da take ha e kamar ta mayunwacin zaki, fuskar da take ganin ta fi kowacce fuskar muni a duniya yau, tana jin yadda zazzafar kalmar da ya jefe ta da ita ta talauci tana kai kawo a birnin zuciyarta. "Haka ABBAS yake ji idan na ambace shi talaka ahalil fu ara'u? Ashe dai kalmar talauci a dangantaka da ita ta sigar cin mutunci baka jin da i ko da kuwa kai talakan ne tun da ba kai ka addarawa kan ka ba, a karon farko da ta gane cewa ABBAS yana jin una a ransa, dama baka sanin munin abu ko kyansa idan kana yi sai ranar da aka maka. "Talauci?" Ta tambaya tamkar an fisgo maganar daga bakinta. "Eh, kuma na fa a saboda ku i kika aure ni, ki kalli tazarar da take tsakanin farin fatarki da ba ar fatata, ki kalli ratar da kyan da kike da shi da munin halittata, ki dubi tsawon shekaruna da suka ara naki, a iyasi a haihuwar kaji na kusa haifar ki SALIMAH ki hasko ni a idanun zuciyarki ina sanye da rigar talauci shin za ki yarda ki aure ni? " "Kenan ku ina su suka lullu e muni, shekaruna, da duk wani abu da za ki ga gazawata" Ya ora ba tare da ya jira cewarta ba "Ki koma wajen zamanki aure babu fashi ki saurara ki ji dokokin gidan nan wanda su ne abu mafi a'ala a gare ki don sa a su ba aramin barazana bane a gare ki" Ya ce yana komawa ya zauna yana aika mata wani kallon mai cike da ma'anoni da dama amma ba masu kyau ba don tuni ya gane ba don Allah ta aure shi ba, duk da shi in ma hakan take a wajensa sai dai shi ya aure ta don cim ma wata oyayyar manufa( Littafin MAIMUNA IYAM) manufar da shi ka ai ya santa kuma saboda cikar burinsa. Dur ushewa ta yi a wajen, ba don bin umarninsa na cewa ta koma mazauninta ta zauna ba, sai don afafunta sun kasa jumurin aukan gangar jikinta, gaba aya ta rasa a wace kalar duniya take,
Chapter 37 · 0% Book details