Sashe 22
Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
anta sai shekin lip stick in da ta shafa suke. Yana danne ok ya kara wayar a kunne kamar an ce ya ago kansa sai ya hangi fitowar SALIMAH daga mota wani mutumi yana rike da murfin kofar da ta fito in, sai wani kare mata kallo yake yana washe baki kamar tsoho ya ga budurwa ita kuma tana masa wani murmushi da shi kansa ABBAS a iya sanin da ya mata na matsayin matarsa tsawon shekara biyar bai ta a ganin ta yi irinsa ba murmushi ne mai cike da ma'anoni da dama murmushi ne da yake nuna tsantsar so da kauna da nuna kulawa ga wanda ake yi wa shi. "Ko don ba ta so na shi ya sa bata ta a yi a gabana ba" Ya ce a zuciyarsa kirjinsa yana bugawa amma ka an ba wani sosai ba ambaton Allah da ya fara yi a zuciyarsa shi ya sa ya ji nutsuwarsa ta daidaita, a hankali ya auke idanunsa daga kallonta ya yi tamkar bai san fa zamanta a wajen ba tamkar babu wata halitta SALIMAH haka ya nuna yana magana a wayarsa wanda ba da kowa yake wayar ba sai Mama har da dariya yake wacce ta bayyana hakoransa. SALIMAH gefe ta matsa Alhajin ya rufe kofar. Duk da a jike take da ku i ko azu ya mata transper na dubu ari biyar sannan da suka je shagon siyayyar ya bata dubu ari kuma duk kayan da ya auka shi ya biya ku in amma yanzu ya fito da 50k ya mi a mata ta kar a. Tana taku ai suna masu jerawa duk gurin kafintocin cike yake da ma'aikatan kowa yana angarensa yana aiki amma sai ta tsallake wajen kowa ta nufi wajen ABBAS saboda cim ma manufarta domin ta fara zargin kamar bai gane ta ba tun da ta hangi lokacin da ya kalleta har kamar ma sun ha a ido sai dai ta ga bata zame masa TV ba don ta san da ya gane ta zai saka gaba yana kallo tamkar ta samu TV musamman da aka auki tsawon lokaci bai saka ta a idanunsa ba tun ranar da suka je da FAROUQ. Gabansa suka karasa tana wani yauki da jijki da kai ita ala dole tana son bayyana masa ta fi karfin talaka tana son kara tabbatar masa matar manya don da manyan ta dace. "Sannu da aiki fa " Alhaji Tahir ya ce yana murmusawa. "Yawwa Alhajin Allah barkan ku da zuwa" ABBAS ya ce cikin sakin fuskan. "Barkan ku dai?" SALIMAH ta maimaita a zuciyarta tana mamaki don ABBAS ya shayar da ita mamaki sai dai tana zargin bai gane ta ba watakila ko saboda hutu ya ratsa ta sosai, amma dai a nata zaton ko wae irin canji ta samu bata zaci zai kasa gane ta ba. Satar kallonsa ta yi a nan ta ga abin mamaki ya kara fari ya yi kiba duk tunaninta za ta gan shi ya kare kamar hatsin guzuri amma sai ta ga sa anin haka. "Yawwa kujera muke so" Alhaji ya fa "Wace iri kuke so Hajiya" ABBAS ya tambaya yana kallon SALIMAH da duk ta sha jinin jikinta tun da ta zo don ta tada masa hankali sai ta ga ko a jikinsa wai an tsikari kakkausa. "Eh kujerar za...za... zama " "Haba Hajiya ke da za ki fa i wace iri ai kowace kujera ta zama ce" Ya ce yana dariya. Duk ta diririce ji take tamkar ta ce ABBAS baka gane ni ba sai dai babu amfanin hakan. "Ta zaman tsakar gida" Alhaji ya fa a yana dariya, akko musu ya yi ta ce guda biyu suke so, ya ce kowacce dubu biyu. Dubu ashirin ta lissafa daga cikin 50k in da Alhajin ya bata yanzu, ta mika masa. Kar a ya yi tare da aukan kujerun ya bi bayansu da su da yake idan aka zo siyan kayan in za a saka a mota su suke kaiwa costomer mota. Alhajin ya bu e masa ya saka a baya, Alhajin ya bu e mata ta shiga ta zauna, ABBAS kuwa tsayawa ya yi daga gefe ya irgi ku insa dubu hu u ya zo gaban kofar da ta shiga ta zauna Alhajin yana kokarin rufewa ABBAS ya mika ku in ya ora mata a cinya yana mai cewa "Hajiya kin yi mantuwa ku in sun zarta kimar wanda za ki biya" Ya ce yana mata murmushin gefen baki. Baki sake take kallonsa wato ma ba zai kar i bajintar da ta masa ba, dama ba don tausayinsa ta bashi ku in ba sai don ta nuna masa a halin da ake ciki yanzu wutsiyar rakumi ta yi nesa da kasa, duk da ta san ta biya masa wannan karatun da baki amma sai ta ga dacewar yanzu ta biya masa shi a aikace. "No ka bar shi ka kara cefane" "Lah ki bar shi godiya nake" Ya ce ba tare da ya jira cewarta ba ya juya ya bar ta baki sake ga takaici shi kuwa Alhaji bai kawo komai ba saboda ya san akwai mutanen da suke basa son a musu kyauta ko an musu sai su ki kar a bai san cewa ABBAS in tsohon mijin SALIMAH ne da ta guda saboda talaucinsa.... IYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH *GARGAGA Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 10 *HAJIYA RAYYANATU* Tun da magriba ta tara Baba Sadiya da sauran ma'aikatan ta fa a musu gobe HAWWA amarya ce don haka kar su jira ta shiga kicin su gabatar da break fast in. Sun amsa mata inda kowa a zuciyarsa ya yi mamakin kalaminta ganin babu wani shiri a tare da HAWWA da zai nuna cewa ita in amarya ce. Saboda haka ko da safe babu wanda ya lura da cewa HAWWA da SABEER basa gidan in banda Baba Sadiya da ta san sun bi dare sun gudu. Hajiya Rayyanatu ce zaune a kujera a falonta ta har aya kan aya sai Lawisa da take latsa waya, aya daga cikin ma'aikatan ce ta shigo cikin ladabi take sanar da Hajiyar cewa HAWWA bata gidan daga ita har SABEER in. Da farko ta an ji wani irin don bata zaci cewa guduwa suka yi ba sai da aka duba gidan kaf aka ce basa nan sannan kuma daga sassafe har zuwa yanzu da ake karfe tara mai gadi ya ce bai ga fitarsu daga gidan ba. Ko da aka bincika cewa komai nasu yana akin sai ta kuduri cewar ko ma ina ta tafi za su dawo ne su same ta. Wajen goma da rabi Baba ya fito daga angarensa sanye cikin babbar riga shi dama gogan Umar yana get ya sha shaddar nan sai she i take ya kafa hula sai kamshi yake shi a dole za a tafi masallacin unguwar a aura masa aure, saboda haka Hajiya bata ma san sun fita ba saboda ma kayan amarya da ta bayar aka inka yana ajiye a kan kujera a falo dama atamfa ce leda (Atamfa roba) Wacce ba cotton ba aka yi doguwar riga wata binjimemiya tamkar buhu wai a cewar Hajiya atamfa leda ta fi kwari kuma inkin a mata maje gaba wanda za ta da e tana mora. Wata makociyarsu ce da Hajiya Rayyanatu da mata waya ta sanar da ita aurin auren ta zagayo don ta ce musu auren za a aura a gaba za a yi shagalin biki. Sosai ta shiga yaba inkin amaryar a maimakon ta fa a mata gaskiya cewar atamfar da inkin basu dace da amarya ba amma sai ta shiga yabawa tana sam barka. "Ni fa a yau ban saka yarinyar nan a idona ba" Hajiya Raytanatu ta ce tana kallon makociyarta. "To ina suka je da duku duku an mai gidana yake ce mini ya ganta ita da aninta a tasha" Da mamaki Hajiya ta kalleta ta ce "Tasha kuma wace irin tasha" "Tashar hawa mota ai ya je kai abokin mai gidana da za hau mota da ya dawo yake fa a mini ya gansu kasancewar jiya da kika kirani muna tare sai nake fa a musu aurenta za a aura yau shi ne da ya dawo yake ce mini ya ga amaryar da nake ce musu za a aura mata aure" Ta kai karshen maganar tana fito da wayarta ta yi danne -danne ta kara a kunne. "Ni wa ka ce mini ka gani a tasha da safe" Nan ya mata bayani Hajiya Rayyanatu da kunnenta ta ji da yake a handsfee ta saka wayar. Wayarta ta auka ta dokawa Baba kira, Baba da yake tsakiyar taro sai baza malun-malun yake wani maro i yana binsa yana ta masa kirarin uban amarya uban ango. Vibration in da wayarsa da take cikin aljihu ta auka hakan ya ankarar da shi ana kiransa fito da ita ya yi ya kara a kunnen nasa yana agawa wasu abokansa hannu yana ta doka murmushi, Umar ango sai washe baki yake jin ka an ta gyara hula abinka da ba a saba sakawa ba. "Alhaji wallahi kar a aura auren nan, shegiyar yarinyar nan ashe bata kwana a gida ba ta auke wannan zololon anin nata sum je tasha sun hau mota sun gudu" Har ta gama bayanin bai ce uffan ba ya yi mutuwar tsaye yana hango Umar da yake ta gaisawa da mutane kamar abin arzi "To" Kawai ya ce wani gumi yana karyo masa ya shiga arewa yawan bataliyar mutanen da ya tara domin halartar auren babban ansa, da kuma an uwansa da ya gama yayatawa cewa suna kaunar junansu kamar su cinye juna. Hakan ya sa aka yi ta masa sam barka mutane suna ara ganin girmansa na ganin ya ri ar zumunsa har zai aurar da ita don wasu basu san halayyar Umar in ba sun auka