← Book details Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 43

Sashe 19

Rubabbiyar Igiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ake tankwara shi idan ya bushe a tarki lankwasawa karyewa zai yi. Duk abin da ya zo ya yi da farko ka yi shiru to nan gaba ma zai kara yi da ka an da ka an sai abu yake yin gaba kafin ka ankara sai ka ga abu ya girmama ta yadda lokacin gyarawa zai gagare ka. Addu'a ita ce babban makami wajen tarbiyantar da yara, sannan kuma saka idanu a lamuransu tun suna kankana, ku lura su waye abokan su kuma su waye kawayensu nusar da su zama a class kusa da yara masu jin magana a aji ba masu wasa da rashin kulawa da karatu ba, wa anda ko a islamiya suke bayar da harda. Umar kuwa zaune ya tashi yana ta kelaya aman giya a falon Hajiya kuwa tana shar ar kuka ta tafi akin nasa tana bu ewa a ki ime ta karasa kasan gadon gabanta yana tsananta bugu tana tsoran abin da za ta gani. Tana lekawa kuwa ta yi ido biyu da kwalaben giya tamkar dai shagon siyar da giyar zai bu e saboda yawansu wasu sun kwalaben ne babu giya wasu kuwa giyar ce a ciki. Sosai ta yi mamakin yadda giya mai yawan wannan take zaune a gidanta amma bata sani ba ta fara tunanin sakacinta ne ya haifar da hakan da a ce tana saka ido a al'amuransa to ko bai daina duka ba zai rage amma ta bar shi sakakaka tamkar dabbobin da aka yi asakon su. Tana kuka tana fito da kwalaben sai da ta fitar duka sannan ta akko guda biyu ta nufo falon lokacin Alhaji Khamis ya ba Baba baki ya zauna sai dai ganin Umar ba karamin bakij ciki da takaici ba yake kara masa. Haka ta karaso tsakiyar falon idanun nan nata jawur tamkar ta kwana tana kukan. "Kika ishi mutane da cewa ana shan giya ashe kema kina sha" Umar ya ce yana aga idanu yana kallon Hajiya da take ji tamkar ta hau shi da duka. "Wai da gaske akwai a akin kenan?" Baba ya ce yana tashi tsaye yana kallon kwalaben da mamaki. "Sun fi kwalba talatin" Ta ce cike da takaici. "Bani in yi kur aya" Umar ya ce don har lokacin a buge yake, a kufule Hajiya ta karasa ya wanka masa mari wanda ya sa sai da ya tuntura daga zaunen da yake. "Kara masa shege tsinanne... "A'uzubillahi haba Alhaji Bukhari ya haka, da bakin ka kake tsinewa anka? Shin baka san baki shi yake kara kangarar da yaro ba? Akwai lokutan kar ar addu'a idan mutum ya yi tana kar uwa ko lokacin da mala'iku za su ce amin. Shi ya sa ake son iyaye su rika saka linzami a harshensu suke yin furucin mai da i ga yaransu ko da kuwa yaran sun ata musu rai su yi kokarin danne zuciyarsu su fa i kalma mai da i, ko da karamin yaro ne idan ya yi laifi kar ka ce masa shege an iska, ko munafuki da sauransu, ka yi kokarin cewa Allah maka albarka Allah sa wannan abin da kake yarinta ce, amma furuci mai muni shi yake kara kangarar da yaro maimakon al'amura suke baya sai suke yin gaba bayan kuma duk halin da suka shiga mu ne dai a ciki" Alhaji Khamis ya katsewa Alhaji Bukhari maganar. Dantse bakinsa ya yi yana jin yadda zuciyarsa take zafi so yake ya furzar da maganar ko ya ji sassauci amma kuma an taka masa birki da mummunan furuci. Wani ashar Hajiya ta yi wa Umar mai maiko... "Hajiya Rayyanatu ana ga yaki kina ga kura, ana hana wani maganar ke kina yi" "Wallahi Alhaji Khamis yaron ne sai da haka kullum daga an hana shi sata sai ya koma sane" "Kin ji fa, wai a nan fa kina nufin daga kin hana shi wannam sai ya koma wancan amma maimakon ki fa i hakan sai kika ce daga an hana shi sata sai ya koma sane, shin sata abu ne mai kyau? Ko sane yana da kyau? Amma kina danganta anki da shi ko zagi da iyaye suke yi wa yaransu tun suna kanana ba tarbiya ba ce saboda yara suna harda a kwakwalwarsu, sai kun ki yaro ya yi zagi sai ku kama shi ku duka kuna ikirarin ba kun hana shi yin zagi ba bayan kuma ku kuna yi kenan idan ba abu bane mai kyau mai ya sa kuke yi? In dai ana bada tarbiya sai an kiyaye da wasu abubuwan sosai saboda yara sun fi aukan abin da ake yi a aikace fiye da wanda ake koya musu" Ya ce yana kallonta daga ita har Alhaji sai suka yi if domin su basu san duk wannan abubuwam da yake fa a ba saboda su dama ba wani damuwa suka yi da tarbiyar ba. "Ai komai ya zo karshe a gobe zan aura maka aure domin ka sani ma, babu fashi ko ka san annabi ya faku ba, idan ka ga kana da iyali ka hankalta" Baba ya ce yana nuna shi da yatsa. "Kuma wannan shawara ce mai kyau aure yana sa nutsuwa da hankalta musamman in aka yi dace da yarinyar kwarai, sai dai ba a nan gizo yake sakar ba, shin a ina za ka samu matar? Ka san dai abokin kura guza kuma na san kalar zaren kalar yadin, ma'ana ba za a samu wata mace budurwarsa mai nagarta ba don babu nutsatstsiyar da za ta kula shi, kuma in ba ta kirki ba ce maimakon ya shiryu sai dani ya kara shiga dawa wato lamura su kara ta arewa" Cewar Alhaji Khamis. "Akwai matar da yake so kuma nutsatstsiya ce" Alhaji Bukhari ya fa "Ikon Allah!" Ya ce da mamaki don ya san dai wace ce za ta yarfa da haka, kafin ya dawo daga duniyar tunanin da ya lula na kankanin lokaci sai ji ya yi Alhaji ya aga waya yana ta kiran mutane yana cewa akwai aurin auren ansa da za a yi gobe karfe goma sha aya na safe, haka ya ringa kiran jama'a yana gamawa ya shiga kwalawa Hawwa kira. "Hauwa'u! Hauwa'u!! Hauwa'u!!!" HAWWA da take akin tana inke wa SABEER rigar islamiyarsa da ta yage da zare da allura ta da e tana ta yi kasancewar bata iya ba, ita hatta keken inki ma bata ta a ganin yadda ake inki da shi ba sai dai in an inko musu kaya ta saka kawai wata rana ma in inkin bai yi mata ba ta ce Ummie ta bayar da kayan saboda gata da suke da shi amma sai ga shi yanzu rayuwa ta juya musu maraici ya sa har tana iya inki da allura da zare, ga kayan duk sun tsufa sun ko e ko an aikin gidansu ba zai saka kayan da suka yi mugun tsufa haka ba, amma sai ga shi abin da suka fi karfinsa ya fi karfinsu dama yawanci gata na iyaye ne daga ranar da ka rasa su a duniya daga lokacin za ka fahimci girma da darajarsu babu wanda zai gane hakan sai maraya wanda ya rasa uwa ko uba ko ma ya rasa su gaba aya. Ko da za ka samu dukkanin gata a bayan ransu to ganinsu ka ai ma rahma ne, daga lokacin da mutuwa ta yi yankan kauna a tsakaninku za ka gane girma da acin maraici!. Yar aikin da ta shigo akin da sauri take fa a mata ta jiyo Baba yana kwala mata kira, da sauri ta yi jifa da riga da zare da allurar hannunta, don ta san yanzu za a ce ta yi laifi a hukunta ta ita kuma bata ji ba saboda hankalinta yana a kan SABEER suna hira suna ta kyalkyalar dariya saboda su biyu ne farin cikin junansu. Fitowa ta yi da sauri ta nufi sashen Baban ta shiga da sallama, tana shiga ta samu gefe a kasan tiles ta durkusa gwiyoyinta a kasa cikin ladabi ta ce. "Ga ni Baba" "Gobr da karfe sha aya za a aura auranku da Umar.... Idanu ta ago tana kallonsa gabanta yana bugawa da karfi, hatta jin ta sai da ya auke na wasu sakkani don kunnen nan nata dummm ya yi. "Alhaji ar aiki za ka aurawa Umar?" Alhaji Khamis ya tambaya yana kallon HAWWA wacce kayan jikinta suka tsufa hatta hijabin jikinta wuyan ya yi yawa ga shi daga gefe da yaga yadda daga gani dutsin guga ne ya kona. HAWWA jin an ce mata ar aiki sai da idanunta suka kawo ruwa duk da bata da bambanci da an aikin, hatta kayan jikinta har gwara na wasu an aikin, ita mutumin ma kallon sani take yi wa fuskarsa. ar gidan Yaya ce marigayi" "Wai HAWWA ce wannan?" Ya tambaya da mamaki. "Ita ce" Hajiya ta ce, shi kuwa Umar lokacin ma bacci ya auke shi yana yashe a tsakiyar falon don tun mangyarin da Hajiya ta masa sai ya kwanta duk kafafunsa a cikin aman da ya yi. "Amma Alhaji Bukhari baka kyauta ba, yanzu ar zumun naka ce ka bari haka a wulakance? Yanzu da shi ne zai bar tsatsonka su wulakanta idan baka raye?" Ya tambaya cike da mamaki "Dakata! Alhaji Khamis kar ka ora mini jakar tsaba kaji su bini, kar ku ka sa duniya ta zage ni ya zan akko yaran su biyu in rike su cin su shan su sutura da karatunsu duk in auki nauyi amma kake mini wata magana a karshe don in kara dankon zumunci ma auki ana sukutum zan aura mata" Murmushin takaici ya yi mai ciwo kafin ya ce "A ina rufin asirin yake? Wannan ne gata, kalli suturar da take jikin yarinyar nan kamar wata almajira yanayin jikinta da na nutsuwarta bai yi kama da na wanda yake cikin farin ciki ba sannan maganar aura mata Umar kuma ai ita za a zalunta tun da duk wanda yake da dogon tunani ba zai auki a mai kamala da hankali kamar HAWWA ya aurawa mashayin giya ba d... "Ya isa haka Alhaji Khamis! Wasa ya yi wasa ban da tsinkarin uwar miji, idan magana za ka fa awa mutane da tada tarzoma ha e da tada zaune tsaye to mun gode ka je umma ta
Chapter 19 · 0% Book details